Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Injiniya Saidu Aliyu da zai maye gurbin Farouk Ahmed?
Jim kaɗan bayan sanar da murabus da Ahmed Farouk ya yi daga shugabancin hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutumin da zai gaje shi.
A wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya ce shugaba Tinubu ya nemi majalisar dattawa da ta amince da naɗin da ya yi wa Injiniya Sa'idu Aliyu Mohammed a matsayin sabon shugaban NMDPRA.
Wane ne Injiniya Sa'idu Aliyu Mohammed?
An haifi Injiniya Sa'idu a 1957 a garin Gombe da ke jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Injiniya Sa'idu Aliyu Mohammed ya kammala digirinsa na farko a 1981 daga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya karanci fannin injiniyan sinadarai.
Injiniya Aliyu ya yi aiki a matsayin manajan darekta na kamfanin sarrafa dangogin man fetir da ke Kaduna, KRPC da kuma kamfanin Iskar Gas na Najeriya.
Ya kuma riƙe shugaban kwamitin kamfanin kula da bututun iskar gas na Afirka ta yamma da rassan kamfanin iskar gas na Najeriya, LNG da kuma NNPC.
Bugu da ƙari, Injiniya Aliyu ya riƙe muƙamin shugaban hukumar iskar gas da wutar lantarki inda a nan ne ya samar da manyan ayyuka da suka jiɓanci iskar gas da kuma tsare-tsaren da suka hada da taswirar alkilta iskar gas da tsarin amfani da iskar gas na Najeriya.
Sannan kuma ya taimaka wajen tabbatar da dokar PIA da ta fayyace ayyukan man fetur a Najeriya.
Sauran ayyukan da Injiniya Aliyu ya yi sun haɗa da manyan ayyukan kamar na shimfiɗa bututun iskar gas daga Escravos zuwa Legas da na Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano.
Me ya sa Farouk Ahmed ya yi murabus?
Injiniya Farouk Ahmed ya yi murabus ɗin ne kwanaki uku bayan da shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Dangote ya yi zargin cewa shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA na biya wa ƴaƴansa guda huɗu kuɗin makaranta a Switzerland da suka kai dala miliya biyar.
"A shekara shida da suka yi su huɗu abin da ya biya shi ne dala miliyan biyar...Ka ga kuwa mutumin da yake ɗaukar albashi ai ba zai iya biya wannan kuɗi ba. Ko ni kaina da nake ɗan kasuwa ai ba zan yi wannan haukan ba, saboda na san akwai mutane a Kano da ba sa iya biyan kudin makarantar ƴayansu naira 100,000. Kuma mun san babansa ba ɗan kasuwa ba ne," in ji Dangote, a wata tattauna da ya yi da ƴan jarida a Legas.
Ɗangote ya ce yana kira ga hukumar da ke yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC ta ta yi bincike kan zargin.
" Ya kamata a bincike shi ko kuma ya fito ya gaya wa mutanen idan babansa ne ya biya masa. To amma mun san cewa babansa ba ɗan kasuwa ba ne. Kowaye ya biya a zo a faɗa cewa ga shi," in ji Aliko Ɗangote.
Tuni dai hukumar yaƙi da almundahana ta Najeriya ICPC ta ce za ta yi bincike kan zargin da shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi wa shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya NMDPRA, Ahmed Farouk.