Wace maƙabarta ce Baqi'a kuma mece ce falalar binne mamaci a cikinta?

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Tun bayan binne gawar fitaccen ɗan kasuwar nan na Najeriya Alhaji Aminu Dantata a maƙabartar Baqi'a da ke birnin Madina, mutane suka fara magana game da maƙabartar.

An dai binne Aminu Dantata a maƙabartar ta Baqi'a ranar Talata bayan rasuwarsa a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Marigayin ne ya bar wasiyyar binne shi a maƙabartar, matakin da hukumomin Saudiyya suka amince da shi bayan rasuwar tasa.

Kan haka ne BBC ta tattaro bayanai game da wannan muhimmiyar maƙabarta da irin mutanen da aka binne a cikinta da lokacin da aka fara amfani da ita.

Ma'anar kalmar Baqi'a

Kalma ce ta harshen Larabci, wadda asalinta shi ne ''Baqi'', ma'ana fili ko wani tsagin gona mai ɗauke da shukukoki ko saiwoyin bishiyoyin da suka mutu''.

Bishiyoyin da suka shahara a filin a baya su ne sabara ko wani abu mai kama da haka, da suka fi yaɗuwa a ƙasashen Larabawa.

''Don haka ne ma ake yi masa laƙabi da sararin sabara'', a cewar Sheikh Abubakar Baban Gwale, wani Malamin Addinin Musulunci a Najeriya.

Maƙabartar Baqi'a

Babbar maƙabarta ce a mai ɗimbin tarihi a birnin Madina, inda aka binne fitattun sahabbai da iyalan Annabi Muhammad (S.A.W).

Maƙabartar na kusa da masallacin Annabi da ke birnin na Madina.

A Baqi'a, an kuma binne Tabi'ai da manyan malaman musulunci.

Maƙabartar na yankin kudu maso gabashin masallacin Annabi da ke Madina.

Girma da faɗin maƙabartar

Baqi'a ce maƙabarta mafi girma a birnin Madina, wadda aka binne sahabban Annabi (S.A.W) aƙalla 10,000.

Baqi'a na da ƙofofi uku ɗaya a arewaci ɗaya a gabas sai kuma babbar ƙofar da ke yammaci, waɗanda ake amfani da su a lokacin ziyara da binne gawarwaki.

A lokacin da aka fara samar da makabartar tana da fadin murabba'in mita 80, to amma daga baya an rika faɗaɗa ta, inda a yanzu ta kai faɗin murabba'in mita 175,000.

Wa aka fara binnewa a Baqi'a?

Bayanai daga litattafan tarihi sun nuna cewa bayan Hijirar Annabi daga Makka zuwa Madina, ya samu maƙabartu masu yawa da mutanen Madina ke amfani sa su.

To amma daga baya ubangiji ya umarce shi ya riƙa binne Musulmi a filin Baqi'a.

Sahabin Annabi na farko da aka fara binnewa a maƙabartar shi ne As'ad ibn Zurarah, daga ƙabilar Khazraj a Madinah, kamar yadda masanin tarihi Ali al-Samhudi (d. 911/1533) ya bayyana.

Sahabin ya kasance cikin sahabban Madina na farko da ake kira al- Ansar, wanda ya rasu wata tara bayan hijirar Annabi (S.A.W)

A ɓangaren sahabban da suka yi hijira tare da annabi daga Makkah (Muhajirun), Uthman ibn Maz'un ne aka fara binnewa a Baqi'a shekara biyu bayan hijira.

Annabi S.A.W ne ya jagoranci jana'izar sahabban a wannan maƙabarta, ya kuma riƙa kai musu ziyara tare da yi mus addu'o'i.

Waɗanne sahabbai aka binne a Baqi'a?

Yayin da ka shiga maƙabartar za ka riƙa ganin alamomin da aka ajiye na irin mutanen da aka binne a ciki kama da ga manyan sahabbai da iyalan gidan annabi Muhammad (S.W.A), kamar matayensa da ƴaƴansa.

Wasu daga cikin fitattun sahabban Annabi da aka binne a maƙabartar sun haɗa da:

  • Uthman ibn Maz'un
  • Abdul Rahman ibn Awf
  • Sa'd ibn Abi Waqqas
  • Asad ibn Zurara
  • Khunais ibn Hudhafa
  • Fatima bint Asad, mahaifiyar Ali ibn Abi Talib

Ƴaƴan Annabi huɗu da aka binne a ciki

Ƴaƴan Annabi huɗu aka binne a Baqi'a sun haɗa da:

  • Umm Kulthum
  • Ruqayya
  • Zaynab
  • Ibrahim

Matan Annabi (S.A.W)

Arewa da ƙaburburan ƴaƴan Annabi (S.A.W) kaɗan ƙaburbura ne na matansa da ake yi wa laƙabi da Ummul Mu'uminina.

Kusan duka matansa a Baqi'a a aka binne su, in ban da Khadija bint Khuwaylid da aka binne a maƙabartar Mualla da ke Makka, Sai Maymuna bint al-Harith, da aka binne a wata maƙarta da ke arewacin Makka.

Matan annabi da ke kwance a Baqi'a sun ne:

  • Aisha bint Abu Bakr as-Siddiq
  • Sawda bint Zam'a
  • Hafsa bint Umar ibn al-Khattab
  • Zaynab bint Khuzayma
  • Umm Salama bint Abi Umayya
  • Juwayriyya bint al-Harith
  • Umm Habiba, Ramla bint Abi Sufyan
  • Safiyya bint Huyayy
  • Zaynab bint Jahsh M

Mece ce falalar binne mamaci a maƙabartar Baqi'a?

Sheikh Abubakar Baban Gwale ya ce maƙabartar na da falala mai girman gaske a Addinin Musulunci.

''Babba daga ciki shi ne kusanci da inda kabarin Annabi (S.A.W) yake tare da manyan sahabbansa guda biyu, Abubakar da Umar (R.A) da matansa da wasu ƴayansa.

Haka kuma Sheikh Baban Gwale ya ce wata falalar Baqi'a ita ce maƙabartar da ba a taɓa binne wanda ba musulmi ba a cikinta.

Maƙabarta ce da ke ɗauke da manyan sahababbai masu yawan gaske, domin kuwa bayanai na cewa an binne sahabbai fiye 10,000 a cikinta.

Sheikh Baban Gwale ya kuma ce an shar'anta wa duk wanda ya je aikin hajji, ya kuma je ''ziyara masallacin Annabi da kabarinsa to ana so ya je Baqi'a''.

Sannan Malamin Addinin ya ce Annabi e ya fara jagorantar janaza a maƙabartar, da kuma ziyara, ''don haka duk wani hukunci da ya zo daga Annabi da ya shafi maƙabarta, to daga Baqi'a ya samo asali''.

''Duk abin da ka ji an faɗa dangane da annabi na abin da ya shafi maƙabarta to daga wannan maƙabarta aka samo hukuncin'', in ji shi.

Malamin ya ce akwai hadisin Ummu ƙais bintu Misan, da ya zo cikin littafin Fatwul Bari - wanda a ciki Ummu Ƙais ta ce Annabi, ya riƙe hannuna har muke je maƙabartar Baqi'a sai ya ce ''Ya Ummu Ƙais wannan maƙabarta daga cikinta Allah zai tashi mutum 70,000 ya shigar da su aljanna ba tare da hisabi ba, sai wani sahabi (Ukasha) ya ce ya manzon Allah roƙa min Allah in kasance cikinsu, sai Annabi ya ce kana ciki, sai wani ma ya sake cewa ni ma roƙa min, sai Annabi ya ce Ukasha ya riga ka''.

Haka kuma ya ce akwai wani hadisin Imamul Ajluni da ya kawo a cikin littafin Kashful Kafa, ''kodayake bai inganta ba'', da a cikinsa Annabi (S.A.W) yake cewa ''maƙabartar Baqi'a ta Madina da maƙabartar Hajum ta Makka ranar alƙiyama za a kama gefensu a tuttule waɗanda ke ciki a aljanna''.

''To ka ga ai duk wannan falala ce da wannan maƙabarta ke da shi'', in ji Sheikh Baban Gwale.