Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ina son a bar mahaifina ya mutu a gidan yari'
- Marubuci, Laura Gozzi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Gargadi: Wannan labarin ya ƙunshi bayanai da suka jiɓanci cin zarafi ta hanyar lalata
Da ƙarfe 20:25 na yammacin Litinin a watan Nuwamba 2020 ne Caroline Darian ta amsa kiran wayar da ta sauya mata rayuwa.
Mahaifiyarta, Gisèle Pelicot, ce ta kira ta wayar.
"Ta sanar da ni cewa ta gano a safiyar ranar cewa [Mahaifina] Dominique ya kwashe kusan shekaru 10 yana ɗirka mata ƙwaya domin maza daban-daban su yi mata fyade," in ji Ms Darian a wata hira da Emma Barnett na shirin BBC Radio 4.
"A wannan lokacin, rayuwata ta sauya daga yadda na san ta," in ji Ms Darian, mai shekaru 46 yanzu.
"Na tuna cewa na yi ihu, na yi kuka, har zaginsa sai da na yi," in ji ta. "Abin ya zame mun kamar girgizar ƙasa."
An yankewa Dominique Pelicot hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari a watan Disamba bayan an kwashe wata uku da rabi ana yi masa shari'a.
Fiye da shekaru huɗu bayan haka, Ms Darian ta ce ya kamata mahaifinta "ya mutu a kurkuku".
Maza 50 da Dominique Pelicot ya tattaro daga shafukan intanet don su yi lalata tare da cin zarafin matarsa Gisèle a lokacin da ba ta cikin hayyacinta su ma an tura su gidan yari.
Ƴan sanda sun kama shi ne bayan ya ɗauki hoton al'uarra wata mata ba tare da izizni ba a wani babban kanti, lamarin da ya sa masu bincike suka sanya masa ido. A kan kwamfuta da wayoyinsa masu bincike sun gano dubban bidiyo da hotuna na matarsa Gisèle, a sume, inda wasu mutane na daban ke yi ma ta fyaɗe.
Baya fito da batutuwan da suka shafi fyaɗe da cin zarafi a tsakanin maza da mata, shari'ar ta kuma fito da batun amfani sinadarai domin a samu galabar mutum - wato kai hari ta hanyar amfani da muggan ƙwayoyi.
Caroline Darian sha alwashin yin gwagwarmaya don yaƙar amfani da sinadarai domin samun galabar mutane, wanda ake tunanin ba kasafai ne ake samun rahoto akansa ba saboda yawancin waɗanda abin ya shafa ba su cikin hayyacinsu a lokacin da aka kai masu harin kuma mai yiwuwa ma ba za su gane cewa an yi musu amfani da muggan kwayoyi ba.
A kwanakin da suka biyo bayan mummunar kiran wayar da Gisèle ta yi, Caroline Darian da ƴan'uwanta, Florian da David, sun yi tafiya zuwa kudancin Faransa inda iyayensu ke zaune don tallafa wa mahaifiyarsu yayin da ta fahimci cewa - kamar yadda Ms Darian ta ce yanzu - mijinta ya kasance "ɗaya daga cikin mafi munin masu cin zarafi ta hanyar lalata a cikin shekaru 20 ko 30 da suka gabata".
Ba da daɗewa ba, Ms Darian ita kanta ƴan sanda suka kira ta - kuma ruyuwarta ta sake rugujewa.
An nuna mata hotuna guda biyu da suka samu a kwamfutar mahaifinta. Sun nuna wata mata a sume akan gado, sanye da ƙaramar riga da kamfai.
Da farko, ta kasa gane cewa ko ita ce matar. "Daga farko na kasa gane kai na," in ji ta.
"Sai ɗansandan ya ce: 'Duba, ku na da alama mai launi iri ɗaya a kumatunku... ke ce." Na kalli waɗannan hotuna guda biyu... Ina kwance a gefen hagu na kamar mahaifiyata, a duk hotunanta."
Ms Darian ta ce ta na da tabbacin cewa mahaifinta ita ma ya yi ma ta fyade - lamarin da ya sha musantawa a kodayaushe, duk da cewa ya bayar da bayanai masu cin karo da juna kan hotunan.
"Na san cewa ya bani ƙwaya, watakila don ya yi lalata da ni. Amma ba ni da wata shaida," in ji ta.
Ba kamar na mahaifiyarta ba, babu tabbacin abin da Pelicot ya yi wa Ms Darian.
"Kuma haka lamarin yake ga mafi yawan waɗanada lamarain ya shafa? Ba kasafai ake yarda da su ba saboda babu wata shaida. Ba a sauraransu, ba a tallafa musu," in ji ta.
Jim kaɗan bayan laifin mahaifinta ya fito fili, Ms Darian ta rubuta littafi.
'Ba zan sake kiransa ba Baba' inda ta bayyana mawuyacin halin da iyalinta ke ciki.
Har ila yau, ya zaƙulo bayanai kan batun amfani da sinadarai, wanda wayancin magungunan da ake amfani da su "ana samunsu ne daga waɗanda ake amfani da su a cikin gida".
"Magungunan kashe zafi, masu kwantar da hankali. Duk magunguna ne, "in ji Ms Darian. Kamar yadda lamarin ya kasance ga kusan rabin waɗanda aka yi amfani da sinadarai aka samu galabarsu, ta san wanda ya ci zarafinta: haɗarin, in ji ta, "daga na jikinka ya ke fitowa."
Ta ce a cikin halin da ake ciki na gano cewa mutane daban-daban fiye da 200 sun yi mata fyaɗe, mahaifiyarta Gisèle ta gagara yarda cewa akwai yiwuwar maigidanta ya ci zarafin ƴarsu.
"Ga uwa yana da wahala ta iya tuanin duk waɗannan abubuwan a lokaci guda," in ji ta.
Amma duk da haka lokacin da Gisèle ta yanke shawarar buɗe shari'ar ga jama'a da kuma ƴan jarida don fallasa abin da mijinta da wasu maza suka yi mata, uwa da ɗiya sun yi yarjejeniya kan abu guda: "Na san mun fuskanci wani abu ... mummuna, amma dole ne mu fuskanci lamarin cikin mutunci da jajircewa."
Yanzu, dole Ms Darian ta fahimci yadda za ta rayu da sanin cewa ita ƴar mai azabtarwa ne da kuma wanda aka azabtar - wani abu da ta kira "mummunan nauyi".
Yanzu ba ta iya lokacin yarantan ta da mutumin da yanzu ta ke kira Dominique, sai dai a wasu lokuta tana komawa cikin al'adar kiransa a matsayin mahaifinta.
Ta ce: "Idan na waiwaya baya ba na tuna da mahaifin da nake tsammani shi ne. Ina zuwa ne kai tsaye in kalle shi a matsayin mai laifi, wanda ya aikata laifukan lalata," in ji ta.
"Amma kwayoyin halittansa na cikin jini na kuma babban dalilin da ya sa na dukufa wurin tallafawa waɗanda ba a san da su ba kuma wata hanya ce da zan yi amfani da ita wurin nisanta kai na wannan mutumin," ta shaidawa Emma Barnett. "Ni gaba ɗaya na bambanta da Dominique."
Ms Darian ta ƙara da cewa ba ta san ko mahaifinta ya kasance "dodo" ba, kamar yadda wasu ke kiransa. "Ya san sarai abin da ya yi, kuma ba rashin lafiya ke damunsa ba," in ji ta.
"Shi mutum ne mai hatsari. Bai kamata a ce zai fita ba, Babu yadda za a yi."
Za a yi shekaru kafin Dominique Pelicot, mai shekaru 72, ya cancanci samun afuwa, don haka yana yiwuwa ba zai sake ganin iyalinsa ba.
A halin yanzu, ƴan gidan Pelicot suna sake farfaɗowa ne. Gisèle, Caroline Darian ta ce, ta gaji daga shari'ar, amma kuma tana "murmurewa... Tana farfaɗowa".
A ɓangaren Ms Darian, lamari ɗaya tilo da ta sanya gaba yanzu ita ce wayar da kan jama'a game da amfani da ƙwayoyi - da kuma ilimantar da yara kan cin zarafi mai alaƙa da lalata.
Tana samun ƙwarin gwiwa daga mijinta, da ƴanuwanta da ɗanta ɗan shekara 10 - "ɗanta kyakkyawa", ta faɗa yayin da ta ke murmushi, muryarta mai cike da ƙauna.
Abubuwan da suka faru a ranar na cikin watan Nuwamba sun suay yadda rayuwarta ta ke a yau, in ji Ms Darian. Yanzu gaba ta ke hangowa.