Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An gurfanar da mutumin da ake zargi da gayyato maza 72 don yi wa matarsa fyaɗe
- Marubuci, Lucy Clarke-Billings
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Wannan labarin na ƙunshe da bayanai masu tayar da hankali.
An gurfanar da wani mutumi a Faransa bisa zargin sa da banka wa matarsa ƙwayayo da yi mata fyaɗe a lokuta da dama, har ma da gayyato wasu mazan da dama domin su yi wa matar tasa fyaɗe.
Mutumin, mai suna Dominique P, mai shekara 71 a duniya, ana zargin sa ne da nemo mutane a intanet yana gayyato su gidansa domin su yi wa matar tasa fyade, a tsawon shekara 10.
Lauyan matar ya ce ana ɗirka wa matar ƙwayoyi ne sosai har ta fita hayyacinta, ta yadda ba ta san lokacin da mutanen ke yi mata fyaɗen ba.
Wannan al’amari ya girgiza mutane da dama, ganin irin girman lamarin.
Ƴansanda sun iya tantance cewa maza 72 ne suka yi wa matar fyade sau 92. An gano mutum 50 daga cikin mutanen da suka yi mata fyaɗen waɗanda yanzu haka aka gurfanar da su tare da mijin nata.
Matar, wadda a yanzu take da shekara 72 a duniya, ta samu masaniya kan fyaɗen da ake yi mata ne a shekarar 2020, lokacin da ƴansanda suka faɗa mata.
Lauyanta, Antoine Camus ya ce shari’ar za ta kasance “mai tayar da hankali” kasancewar zai zamo karon farko da matar da za ta ga bidiyoyin da ke tabbatar da cewa an yi mata fyaɗe.
Ya faɗa wa kamfanin dillancin labari na AFP cewa “a karon farko, za ta yi rayuwa tare da jimamin fyaɗen da aka kwashe shekara 10 ana yi mata.”
Ƴansanda ne suka fara gayyatar Dominique P a watan Satumban 2020 sanadiyyar wani abu da ya faru, lokacin da jami’an tsaro suka kama shi yana ɗaukar bidiyon wasu mata uku a asirce ta ƙarƙashin fatarinsu a wani kanti.
Daga nan ne ƴansanda suka gano ɗaruruwan hotuna da bidiyoyin matarsa a cikin cikin kwamfutarsa, inda alamu suka nuna cewa ba ta cikin cikin hayyacinta.
Bidiyoyin sun nuna alamun zargin cin zarafi da dama a gidan mutumin. Ana zargin cewa cin zarafin ya fara ne tun shekarar 2011.
Haka nan masu bincike sun ga tattaunawarsa ta intanet, inda mutumin ya riƙa gayyato wasu mutanen na daban domin zuwa gidansa su yi lalata da matar tasa.
A lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa ya riƙa ɗirka wa matar ƙwayoyin kashe jiki, ciki har da wata ƙwaya da masu lalurar zaƙuwa ke sha.
Ana zargin sa da yi mata fyaɗen shi kansa, da kuma ɗaukar bidiyon sauran mutanen da ya gayyato suna wa matar tasa fyade yayin da yake ƙara ƙarfafa musu gwiwa, kamar yadda masu bincike suka gano.
Sai dai babu alamun cewa ya karɓi kuɗi domin bai wa mazan damar yi wa matar tasa fyaɗe.
Sauran mutanen da ake zargi, sun kama ne daga shekara 26 zuwa 74, waɗanda suka fito daga wurare daban-daban. Yayin da wasu sau ɗaya kawai suka yi wasu kuma sun je sun yi mata fyaɗen har sau shida, in ji masu bincike.
Mutanen sun ce sun aikata abin da suka aikata ne domin taimaka wa ma’auratan cika burinsu, to amma Dominique P ya shaida wa masu bincike cewa dukkanin mutanen na da masaniyar cewa matar tasa a buge take.
Wani masani ya ce ƙwayoyin da ake ɗirka wa matar na sanyawa ta zama “tamkar wadda ta suma.”
Dominique P, wanda ya ce an taɓa yi masa fyaɗe a lokacin da yake ɗan shekara tara a duniya, a yanzu “ya shirya fuskantar iyalansa da ƴan’uwa”, in ji lauyansa, Beatrice Zavarro.
An kuma zargi mutumin da yin fyaɗe da kisa a 1991, sai dai ya musa, da kuma yunƙurin yin fyaɗe a 1999, wanda ya amsa laifinsa bayan an yi gwajin ƙwayoyin halitta na DNA.
Shari’ar wadda ake yin ta a birnin Avington da ke kudancin Faransa, ana sa ran za a ci gaba da ita har zuwa watan Disamba.
A ranar Litinin, lokacin da aka fara shari’ar, matar ta bayyana a kotu tare da ƴaƴanta uku, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.
Lauyanta ya ce za ta so a ce an saurari shari’ar a sirrance, to amma sun gane cewa abin da waɗanda ake zargi za su fi so ke nan.