PSG ta kai zagayen karshe a UCL bayan doke Arsenal

Asalin hoton, Reuters
Lokacin karatu: Minti 1
Paris St Germain ta tsallake zuwa zagayen karshe a gasar Zakarun Turai bayan doke Arsenal gida da waje.
PSG ta tsallake ne da jimillar kwallaye 3-1, bayan doke Arsenal 2-1 a Paris da kuma ci 1-0 a Emirates.
Karo na biyu kenan da PSG ta kai zagayen ƙarshe a gasar Zakarun Turai tun 2020 da Bayern Munich ta doke ta kuma ta lashe kofin gasar.
PSG ba ta taɓa lashe kofin Zakarun Turai ba a tarihinta
Yanzu PSG za ta hadu ne da Inter Milan wadda ta fitar da Barcelona.
PSG na harin lashe kofi uku ne a bana inda tuni ta lashe kofin Lig 1, sannan za ta buga wasan karshe a kofin kalubale na Faransa, yanzu kuma ta kai zagayen karshe a gasar Zakarun Turai.






