Yadda ƙishirwa ke kashe 'yan Sudan ta Kudu saboda gaurayar ruwa da man fetur

Wata mata sanye da baƙaƙen kaya ke tafiya ɗauke da abarba a kanta. A ɗaya gefen, itatuwa ne suka kewaye bayan ambaliya - a Bentiu, da ke Sudan Ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Maura Ajak and Stephanie Stafford
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
  • Lokacin karatu: Minti 9

Makiyaya da ke amfani da ruwan wani kogi da ya gurɓata a Sudan Ta Kudu, na sane da irin haɗarin da ke tattare da shansa.

"Ruwan ya gurɓata saboda akwai man fetur cikinsa - kuma yana da sinadaran Chemical a ciki," in ji wani jagoransu Chilhok Puot.

Wata mata da ke kiwon dabbobi a yanki a kuma tsakiyar wuraren da mai ya gurɓata a jihar Unity, Nyatabah, ta ƙara da cewa: "Idan ka sha ruwan, zai sanya ka riƙa yin tari.

"Mun san ruwan ba shi da kyau, amma ba mu da wani wuri da ya fi shi, kishirwa tana kashe mu."

Wani tsohon injiniyan mai ya faɗa wa BBC cewa ambaliyar ta janyo gurɓacewar wuraren samun ruwa a yankin.

Wani ɓangare na jihar ya cika da ɗimbin ruwa na tsawon shekaru bayan mummunar ambaliya da aka fuskanta, wanda masana kimiyya suka ce sauyin yanayi ya ƙara ta'azzara lamarin.

David Bojo Leju ya ce ambaliyar ta kasance "babbar balahita" kuma gurɓacewar muhalli daga wuraren man fetur da ba a kula da su ba na yaɗuwa a faɗin jihar.

Wuraren da mai ya gurɓata

Asalin hoton, David Bojo Leju

Bayanan hoto, Tsohon injiniyan man fetur David Bojo Leju ya ɗauki bidiyon wurare da dama bayan da man fetur ya gurɓata su sannan ya gauraya da ruwa a yankin Roriak

Sudan Ta Kudu ita ce ƙasa da aka ƙirƙira ta baya-bayan nan a duniya kuma ɗaya daga ciki mafiya talauci a duniya, wadda gwamnatin ta dogara da man fetur.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jihar Unity, wadda ke sahun gaba wajen samar da man fetur, ta sha fuskantar ambaliya a kowace shekara.

Sai dai a 2019, mamakon ruwa ya afkawa ƙauyuka da kuma dazuka. An ci gaba da samun ruwan saman a shekara-shekara. Ruwan ya malala, ya kuma shiga cikin gonaki.

Lamarin ya munana a 2022, inda ruwa ya shanye kashi biyu bisa uku na jihar ta Unity, a cewar shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) - ta ce kashi 40 na cikin ruwa har yanzu.

Mista Bojo Leju ya yi aiki na tsawon shekaru takwas a kamfanin mai na Greater Pioneer Operating Company (GPOC), wadda haɗin gwiwa ne tsakanin kamfanonin mai na Malaysia da Indiya da kuma China - gwamnatin Sudan ta Kudu ta mallaki kashi 5 na hannun jari a kamfanin.

Bayan da wani babban bututun mai ya fashe shekaru biyar da suka wuce, ya fara ɗaukar hotuna da kuma bidiyon tafkunan ruwa a wurare a jihar Unity, ciki har da wuraren da ke kusa da Roriak, inda makiyayan ke zaune.

Ya ce malalar da ake samu daga rijiyoyin mai da bututun mai abu ne mai ta da hankali, kuma yana da hannu wajen jigilar gurɓatacciyar ƙasa daga hanyoyi, don haka ba za a ganta ba.

Ya yi ƙoƙari ya bayyana damuwarsa ga shugabannin kamfanoni, amma ya ce ba a yi wani abin kirki ba kuma "babu wani tsarin kula da ƙasa."

Mista Bojo Leju ya kuma ce "ruwan da aka samar" - ruwan da ake fitarwa daga ƙasa lokacin da ake hako mai kuma galibi ke ɗauke da sinadarin hydrocarbons da sauran gurɓataccen yanayi - ba a kula da su yadda ya kamata.

Makiyaya a Sudan Ta Kudu
Bayanan hoto, Makiyayan na fargabar cewa gurɓacewar ruwa a yankin Roriak na janyo dabbobinsu kamuwa da ciwo

Akwai rahotannin kasancewar mai da yawa a cikin ruwan da ake samarwa kuma wannan ruwan shi a ke kai wa al'umma su sha".

"Tambayar ita ce ta ina ruwan ke fita?" in ji shi.

"Daga koguna, daga wuraren da mutane ke samun ruwan sha, har ma zuwa ƙoramun da mutane ke kama kifi."

Mr Bojo Leju ya faɗa cewa "wasu sinadaran mai ɗin sun shiga cikin ƙasa sosai, inda suke zarcewa zuwa rijiyoyin burtsatse.

"Ruwan ya gurɓata."

Lokacin da aka fara samun mamakon ruwan sama a 2019, an samu zaizayar ƙasa kusa da wuraren da man fetur ya malala "amma bai kai yawan da zai gauraya gaba-ɗaya da ruwa ba", in ji shi.

A yankin Roriak, akwai babu wasu bayanai kan ingancin ruwan da makiyayan ke sha, sai dai akwai fargabar cewa gurɓacewar muhalli na saka dabbobi su faɗa rashin lafiya.

Sun ce ana haihuwar ƴaƴan shanu ba tare da kai ko yatsu ba.

Ministan aikin gona na jihar Unity ya ɗora laifin mutuwar dabbobi sama da 100,000 a shekara biyu da suka wuce kan ambaliyar da aka samu da kuma gurɓata muhalli da mai ya yi.

Hoton wani sansani da aka tsugunar da waɗanda ambalkiya ta ɗaiɗaita a Sudan Ta Kudu
Bayanan hoto, Zaizayar ƙasa da kuma ambaliya ta ɗaiɗaita kusan mutum 140,000

A wani daji kusa da kauyen Roriak, wasu mutane ne maza da mata ke aikin sare itatuwa domin yin gawayi.

Sun yi tafiyar kusan sa'a takwas a kan hanyar da ta gurɓace sakamakon ambaliya kafin kai wa dajin.

Sun ce ruwan da suke samu a can ya gurɓace.

Sun kuma ce yana janyo amai da gudawa da kuma ciwon gaɓoɓi", in ji wata mata, mai suna Nyakal.

Ita ma, wata mata mai suna Nyeda wadda ke share hawaye a fuskarta, ta ce tana son gawayin domin sayar da shi, amma tana cikin damuwa kan ƴaƴanta bakwai, da ta bari tare da mahaifiyarta na tsawon mako ɗaya.

"Ba ni da komai," in ji ta.

Nyeda na zaune ne a Bentiu, babban birnin jihar Unity, a wani ɗan karamin sansani mai ɗauke da mutum 140,000 waɗanda suka tserewa rikici ko kuma ambaliya. Ruwa ya mamaye ɗaukacin sansanin, inda yake samun kariya kaɗai daga shingayen tare ruwa da aka yi.

Ana ba wa mutanen wurin tallafin abinci, sai dai da dama daga cikinsu na rayuwa ne da kifi da kuma ruwa a wasu yankuna.

Tsaftataccen ruwa ya yi ƙaranci. Nyeda na amfani da ruwa daga wani rijiyar burtsatse wajen yin wanki da kuma girki, amma tana buƙatar kuɗi domin sayen ruwan sha.

Nyeda riƙe da adda a kan kafaɗarta a cikin dajin da ke kusa da ƙauyen Roriak
Bayanan hoto, Nyeda ta bar ƴaƴanta bakwai tare da mahaifiyarta na tsawon kwanaki shida domin zuwa cikin daji ta samu gawayi don ta zo ta sayar

Masana kiwon lafiya da ‘yan siyasa a yankin sun shaida wa BBC cewa suna fargabar gurɓacewar muhalli da rashin tsaftataccen ruwan sha na yin illa ga lafiyar bil’adama.

A wani asibiti a Bentiu, wata uwa ta haihu. Ta haifi jaririn hanci da kuma bakinsa a haɗe.

"Ba su da damar samun ruwa mai tsafta," in ji Dr Samuel Puot, ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da jaririn.

"Suna sha ne kawai daga kogin da ke haɗe da ruwa da mai, watakila wannan shi ne matsalar."

Ya ce akwai ‘ya’ya da dama da aka haifa da rashin lafiya, kamar waɗanda ba su da gaɓoɓi ko kuma masu karamin kai, a Bentiu da kuma Ruweng, yankin da ake hako mai a arewacin jihar Unity.

Suna mutuwa cikin kwanaki kaɗan ko watanni, in ji shi.

Gwajin kwayoyin halitta na iya ba da alamu game da abubuwan da ke haifar da rashin haihuwa, amma asibitin ba shi da kayan aiki, kuma ba a kammala sakamakon a yawan lokuta.

Dr Puot yana son gwamnati ta ajiye rajistar kararraki.

Jaririn da aka haifa wanda bakinsa da kuma hanci a haɗe, kwance a wani asibiti a Bentiu
Bayanan hoto, Iyayen wannan jariri da aka haifa a asibitin Bentiu na zaune a wani yankin da ruwansa ya gauraya da man fetur, kamar yadda wani likita ya faɗa wa BBC

"Abin damuwa ganin cewa gurɓacewar muhalli sakamakon malalar mai zai janyo ƙaruwar barazanar haihuwar jarirai ba tare da wasu gaɓoɓi ba," a cewar Dr Nicole Deziel, wata kwararriya kan lafiyar muhalli a Jami'ar Yale.

Gurɓacewar muhalli babban barazana ne ga al'umma, saboda zai shafi kwayoyin halitta da janyo cutuka da kuma rashin samun abinci mai gina jiki, in ji ta.

Wasu sinadarai da ake fitarwa yayin samar da man fetur su ma za su shafi haihuwa, in ji Dr Deziel.

A 2014 da 2017, wata ƙungiya mai zaman kanta a Jamus mai suna Sign of Hope, ta gudanar da bincike kan wuraren samar da mai a jihar Unity.

Sun gano cewa akwai sinadarai da yawa a cikin ruwa kusa da rijiyoyin mai, inda sinadaran lead da barium suka fi yawa.

Masu binciken sun karkare da cewa hakan na nuna gurɓacewar muhalli da aka samu sakamakon malalar fetur.

Wani mutum tsugune yana cire bado daga ruwan ambaliya kusa da birnin Bentiu
Bayanan hoto, Mutane na ɗibar bado su ci daga ruwan na ambaliya, wanda Mista Bajo Leju ke ganin na ɗauke da cutuka

Gwamnatin ƙasar ta kaddamar da alkaluma na tasirin da masana'antar mai ta yi a muhalli, sai dai har yanzu ba a fitar da alkaluman ga jama'a ba sama da shekara ɗaya.

Wata babbar ƴar siyasa daga jam'iyya mai mulki, Mary Ayen Majok na nuna damuwa kan gurɓacewar muhalli da mai ya janyo sama da shekara goma.

Ta kasance jami'a a gwamnatin ƙasar kuma mataimakiyar kakakin majalisa a majalisar dattijan Sudan Ta Kudu, ta kuma fito daga Ruweng.

Ta ce wani ɗan uwanta yana da ɗa wanda aka haifa da wasu gaɓoɓi a haɗe kuma tana da yaƙinin cewa akwai irin waɗannan abubuwa da yawa da ba a bayyana ba saboda fargabar tsangwama ko rashin samun ingantattun asibitoci.

Ms Majok ta ce Sudan Ta Kudu "ta gaji masana'antar da aka lalata da ayyukan ba daidai ba" lokacin da aka kafa ƙasar a 2011 bayan samun ƴancin kai daga Sudan.

Wani yaƙin basasa na tsawon shekara biyar ya ɓarke a 2013. Ga ƙasar da ke fuskantar rikici da kuma ta dogara kan man fetur, inganta yanayin muhalli "shi ne abin da muka fi bai wa fifiko", in ji ta.

An kirkiro da dokoki da kuma hukumomi, sai dai "gaskiya da amana ta yi ƙaranci", in ji Majok.

 Mata ke nuna ruwa a cikin buta da kuma kofi a ƙauyen Roriak, da ke Sudan Ta Kudu
Bayanan hoto, Mata da ke aikin sare itatuwa don yin gawayi a yankin Roriak sun ce suna ɗuma ruwa kafin su sha, amma duk da haka yana janyo musu ciwo

"Magana a kan man fetur tamkar taɓa zuciyar gwamnati ne," in ji Mista Bojo Leju.

Ya tattauna da BBC a Sweden, inda aka ba shi mafaka.

A shekarar 2020 ne lauyoyin Sudan ta Kudu suka tunkare shi lokacin da suka so kai karar gwamnati kan gurɓatar man fetur.

Na yarda in yi magana a matsayin mai shaida. Sai dai ya ce jami’an tsaro sun tsare shi, suka buge shi da bindiga a kai tare da tilasta masa sanya hannu a kan takarda da ke musanta shaidarsa.

Ya gudu daga ƙasar bayan nan. Lauyoyin ba su ci gaba da shari'ar tasu ba.

BBC ta buƙaci ƙungiyar mai ta GPOC da ofishin shugaban Sudan ta Kudu da su yi tsokaci kan wannan zargi a cikin wannan rahoto, amma ba su mayar da martani ba.

David Bojo Leju speaking in Sweden
Bayanan hoto, An ba wa Mr Bojo Leju zaman mafaka a Sweden bayan matsin lamba a Sudan Ta Kudu

Masana kimiyya ba su da tabbacin cewa ambaliyar da ta ɗaiɗaita jihar Unity ko ta ragu ba.

Dr Chris Funk, darektan kula da barazanar sauyin yanayi a Jami'ar Carolina, a Santa Barbara, ya ce an samu ƙaruwar tumbatsar ruwa a 2019 a tekun yammacin Indiya.

Iska mai ɗumi zai iya riƙe danshi sosai, kuma ya ce akwai alaƙa mai karfi tsakanin yanayin koguna da kuma mamakon ruwan sama da aka fuskanta a Gabashin Afrika a 2019.

Dr Funk ya ce an ci gaba da fuskantar mamakon ruwan sama tun lokacin a tafkin Victoria wanda ya zarce zuwa Sudan Ta Kudu.

Yanayi ya ƙaru a Sudan Ta Kudu kuma ana sa ran zai ci gaba da ƙaruwa, in ji shi.

Duk da fargabar ambaliya da kuma gurɓacewar muhalli, mutane da yawa na fatan koma rayuwar kiwon dabbobi da kuma zama a ƙasarsu.

A Roriak, yara ne ke miririn ƙauyen da aka gina da laƙa, mai ɗauke da ɗakunan taɓo da kuma shanu.

A can kusa da birnin Bentiu, wata tsohuwar mata ce ke cire bado kusa da hanyar ruwa. Ta ce tana son sake samun shanu watarana.

"Idan ruwan ya ragu, zan noma hatsi, ko da cikin tsawon shekaru ne," in ji ta.