Wane zaɓi ya rage wa ƴaƴan jam'iyyar PDP gabanin zaɓe?

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Litinin 9 ga watan Maris ne kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar soke hukuncin kotun farko, wadda ta hana hukumar INEC amincewa da sakamakon babban taron jam'iyyar PDP da aka yi a ranar 31 ga Oktoba.

A bara ne dai mai shari'a James Omotosho na babban koton tarayya da ke Abuja ya soke babban taron PDP da aka yi a birnin Ibadan na jihar Oyo a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban bara.

A hukuncin, wanda dukkan alƙalan kotun guda uku suka yanke, kotun ɗaukaka ƙarar ta amince da hukuncin na ƙaramar kotun, inda ta ce hukuncin watan Oktoban ya yi daidai.

Tun da farko dai wata kotu ta dakatar da jam'iyyar daga gudanar da taron, wanda a wajen ne aka zaɓi sababbin shugabanninta a ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki, duk da cewa wata kotun daban ta amince mata.

Sai dai kuma a ranar Alhamis na kafin babban taron ne wata babbar kotun jihar Oyo ta goyi bayan ci gaba da shirin gudanar da taron, inda ta jaddada umarnin da ta bayar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙorafin da mai ƙara ya shigar.

Hukunce-hukuncen kotu

Tun da farko kafin babban taron, ɓangaren da ke biyayya ga Ministan Abuja Nyesom Wike ya dakatar tare da kafa sabon kwamatin amintattu na PDP, wanda shi ne mafi girma a tsarin shugabancin jam'iyyar. Sun kuma dakatar da Ilya Damagun da sauran manyan shugabanni na lokacin.

Sun ɗauki matakin ne bayan tsagin Damagun ya dakatar da wasu shugabannin jam'iyyar da ke yi wa Wike biyayya, ciki har da sakataren jam'iyyar na ƙasa na wancan lokacin, Samuel Anyanwu.

Sannan kuma masu ƙorafin sun nemi kotu ta dakatar da shugaban PDP na ƙasa na lokacin a ƙarƙashin Iliya Damagun, da kwamatin gudanarwa, daga gudanar da taron kamar yadda aka tsara, bayan umarnin wata kotu da ya ce a dakata.

A gefe guda kuma, tsohon Gwmanan Jigawa Sule Lamido ma ya shigar da jam'iyar ƙara yana ƙalubalantar hana shi sayen tikitin takarar shugabancin jam'iyyar na ƙasa kafin zaɓen na ranar 15 ga wata.

1 - PDP ta fara fuskantar umarnin kotu ne a ranar 31 ga watan Oktoba, lokacin da babbar kotun tarayya a Abuja ta umarci a dakatar da shirin gudanar da babban taron na ƙasa.

Mai Shari'a James Omotosho ya bayar da umarnin bayan shigar da ƙorafi gabansa domin ya duba ko PDP ɗin za ta iya ci gaba da shirin gudanar da taro na 15 da 16 ga watan Nuwamba.

Mutum uku da suka shigar da ƙarar abokan siyasar Ministan Abuja Nyesom Wike ne, wanda ya ci alwashin hana gudanar da taron sakamaon rigimar da yake yi da shugabancin jam'iyyar.

Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa PDP ta gaza wajen bin dokokin mulkin jam'iyyar da kuma Dokar Zaɓe ta 2022 game da shirin gudanar da taron.

Lauyan masu ƙorafi ya faɗa wa kotun cewa PDP ba ta gudanar da zaɓukan shugabancin jam'iyyar ba a jihohi 14, inda ya nemi kotun ta duba ko hakan ya saɓa wa doka.

2 - Sai kuma a ranar Talata 11 ga watan Nuwamba wata babbar kotun a Abuja ta sake bayar da umarnin dakatawa da shirin gudanar da taron sakamakon ƙarar da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya shigar.

Kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Peter Lifu ta bayar da umarnin ne tana cewa har sai ta kammala sauraron ƙorafin na Sule, sannan ta hana hukumar zaɓe zuwa domin saka ido a zaɓen.

Alƙalin ya ƙara da cewa ya aminta da ƙorafin da Sule ya shigar na cewa PDP ba ta wallafa jadawalin yin taron ba saboda mambobinta su sani kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.

3 - A wani umarni mai cin karo da wancan, a ranar 4 ga watan Nuwamba babbar kotun jihar Oyo ta umarci PDP ta ci gaba da shirin taron bayan wani ƙorafi

Mai Shari'a Ladiran Akintola ya umarci jami'an PDP da wakilanta da su guji duk wani yunƙuri na dakile ko karya jadawalin da aka aka fitar, sannan ya umurci hukumar zaɓe ta tura jami'anta domin sa ido.

Zaɓi ga ƴan PDP

Dokta Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano ya ce idan aka yi la'akari da yanayin masu riƙe da madafun iko a Najeriya, har yanzu PDP ce babbar jam'iyya ta biyu.

Sai dai ya ce wannan hukuncin zai ƙara taɓa jam'iyyar, saboda zai ƙara jefa rashin tabbas a tsakanin ƴaƴanta.

"Abin da nake gani shi ne su duba maslahar jam'iyyar. Idan sun fi aminta da shugabancin Turaki, sai dai su bar jam'iyyar. Amma idan amma idan suna gani za a samu maslaha ko kuma shugabancin Turaki za su yi haƙuri domin tafiyar da jami'ar, to ina ganin sai a karɓa da haƙurin, sannan su haɗu baki ɗaya su ga yadda za su ciyar da jam'iyyar da dimokuraɗiyya gaba."

Masanin siyasan ya ce idan aka yi la'akari da ƙaratowar lokacin zaɓe, ko an ci gaba da shari'a babu tabbacin za a iya kammala cikin lokaci, "don haka sai dai ko dai su bar jam'iyyar ko su yi haƙuri su gyara," in ji shi.

Sufi ya ƙara da cewa hukuncin lallai ba ƙaramin kawo ruɗani zai haifar ba a PDP, sannan ya bayar da shawarar a ci gaba da rajistar ƴaƴan jam'iyyar kamar yadda doka ta tsara.

A game da fargabar da ake yi kan komawar jam'iyyar a hannun tsagin Wike, Sufi ya ce dama tun baya akwai fargabar.

"Tun a can baya wasu manyan jam'iyyar suke ganin idan ba a kore shi ba, zai haifar musu da matsala, har suke ganin idan yana jam'iyyar su za su fice, amma jam'iyyar ta kasa."

Sai dai duk da haka masanin harkokin siyasar na ganin bai kamata a yi watsi da jam'iyyar PDP ba, domin a cewarsa zai fi kyau a lalubo hanyoyin da za a iya gyara ta ta sake farfaɗowa.

"Yanzu dai ya rage wa ƴaƴan jam'iyyar wajen nemo hanyar da ta fi zama musu mafita, amma a yanzu PDP ita ce ta biyu wajen a Najeriya idan aka yi la'akari da riƙe madafun iko."

"Don haka a ce an haƙura da ita baki ɗaya ba tare da tabbatar samar da wata babbar hamayya ba, bai dace ba."