Me ya sa Ukraine ta ƙi sayar wa ƙasashen yankin Gulf makaman kariya?

    • Marubuci, اولگ چرنیش
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, سرویس اوکراینی بی‌بی‌سی
    • Aiko rahoto daga, کی‌یف
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ƙasashen yanin Gabas ta Tsakiya da na yankin Gulf da ma Amurka sun buƙaci Ukraine ta sayar wa ƙasashen makaman kakkaɓo jirage marasa matuƙa na ''Shahid' da Iran ke ƙerawa.

Duk da bayar da damar fitar da makamai daga Ukraine da aka yi a baya-bayan nan, Kyiv ba ta bayar da damar sayar da makaman ba.

Sai dai ƙasashe dama musaman na yankin Gulf na cikin zakuwar sayen makamai domin kare kansu daga hare-haren da Iran ke kai musu abaya-bayan nan.

Wani wakilin kamfanin da ke ƙera jiragen ya shaida wa BBC cewa tawagogi da dama daga ƙasashen yankin Gulf na ta zuwa Ukraine domin tattaunawa da jami'an ƙasar game da cinikin makaman.

Ukraine ta samu fasahar ƙera makaman kakkaɓo jirage marasa matuƙar samfurin Shahid da Iran ke ƙerawa, sakamakon yawaitar hare-haren da Rasha ke kai mata da makaman.

Ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun jima suna bin Ukraien domin sayar musu da makaman tun gabanin fara yaƙin.

A ranar 12 ga watan Fabrairu ne babban sakataren majalisar tsaron Ukraine, Rustam Umarov, ya ce ƙasar ta samu lasisin sayer da makaman ga ƙasashen waje.

Sai dai har yanzu ba a samu lasisin fara fitar da makaman ba.

Kafofin yaɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa, Amurka ta nuna sha'awar makaman bayan da Iran ta kai wa mafi yawan sansanonin sojinta a yankin Gabas ta Tsakiya da jiragen marasa matuƙa.

Sakataren harkokin tsaron Amurka, Pete Hegsett ya tabbatar da cewa jiragen marasa matuƙa da na ''hatsarin gaske'' fiye da yadda ake zato.

A ranar 5 ga watan Maris ne shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce ƙasarsa ta samu buƙata ta musamman daga Amurka na taimaka wa tsaronta saboda hare-haren jiragen marasa matuƙa a Gabas ta Tsakiya.

'Wasiƙar sirri'

A farkon watan Maris ne kamfanonin ƙera makamai na Ukraine suka samu sakonnin imel na buƙatar sayen makaman daga Gabas ta Tsakiya.

Wani ɗan kasuwa ya shaida wa BBC cewa sun samu wasiƙar daga wata hukuma da ya bayayna da ''manyan ƙawaye''

Sai dai a cewar wani rahoto na sashen bincike na sojin ƙasar, ''ɗaya daga cikin hukumomin tsaro'' ta rubutoi wasiƙar.

Sai dai wasiƙar ga gargaɗi kamfanonin ƙera makaman kada ya saɓa ka'idojin fitar da damakaman da gwmantin ke iko da su, kada su faɗa hannun ɓata gari.

Ko shakka babu a yanzu haka ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya na cike da kishirwar irin waɗannan makamai na kariya sakamakon jerin hare-haren jirage masara matuƙa da na makamai masu linzami da Iran ke kai musu.

'Tsananin buƙatar makaman'

Kamfanonin Ukraine masu ƙera makaman kakkaɓo jirage marasa matuƙa sun shaida wa BBC cewa wakilan ƙasashen Gabas ta Tsakiya sun tuntuɓe su game da sayen makaman.

To amam sun ce hukumomin Ukraine sun sanya dokoki masu tsauri game da yiwuwar ƙullar yarjejeniyar cinikin.

"Ƙasashen sun nuna sha'awa, amma kowa ya sani irin wannan cinikayya ba za a iya ƙulla shi ba ba tare da sanin gwamnati ba'', a cewar ɗaya daga cikin shugabannin kamfanonin ƙera makaman.

Ɗaya daga cikin kamfanonin na cewa kamfaninsa zai iya ƙera makaman kakkaɓo jiragen na shahid da aka bukata a ilahirin yankin Gabas ta Tsakiya, ba tare da cutar da tsaron Ukraine ba.

Kawo yanzu dai UKraine ba ta bayyana dalilin jan ƙafarta wajen sayar da makaman ga ƙasashen na yankin Gulf ba.

Sai dai wasu na ganin tana yin hakan ne saboda rashin ɗaukar matsayi da mafi yawan ƙasashen suka yi a yaƙin da take yi da Rasha.

Mataimakin shugaban kamfanonin tsaron Ukraine, Sergey Vysotsky, ya shaida wa BBC cewa makaman Ukraien na da farin jini tsakanin ƙasashe tun ma kafin fara yaƙin Iran.

Ya ƙara da cewa an gano haka ƙarara a lokacin bikin baje kolin makamai da aka gudanar a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya a farkon watan Fabrairun da ya gabata.

"Yana da kyau mu ƙara inganta hakan domin bai wa sauran ƙasashe damar hadin gwiwa don mallakarsu,'' in ji shi.

"A yanzu duniya na ƙara nuna sha'awar mallakar makaman Ukraine, musamman yankin Gabas ta Tsakiya, inda Iran take''.

Kawo yanzu dai gwamnatin Ukraine ba bayar da lasisin fitar da makaman ga kamfanonin da ke ƙera makaman ba.