Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Isra'ila ba ta son makwaftanta su mallaki makamin nukiliya duk da ita tana da su?
A yanzu haka Isra'ila ce ƙasa ɗaya tilo da aka yi amannar ta mallaki makamin nukiliya a Gabas ta Tsakiya, duk da cewa ba ta tabbatar ko kuma musanta hakan ba.
Ana ƙiyasin cewa Isra'ilar ta mallaki mankaman nukiliya aƙalla guda 90.
A shekarar 1986, wani masani kan makamin nukiliya ɗan Isra'ila, Mordecai Vanunu ya fito ƙarara ya bayyana cewa ƙasarsa ta gina tukunyar sarrafa nukiliya har ma ta haɗa bam ɗin nukiliya a asirce.
Ya tsere ya bar ƙasar domin gudun kada a cutar da shi kasancewar ya fallasa wani sirri da ƙasar ta kwashe shekaru tana ɓoyewa. Sai dai jami'an tsaron Isra'ilar sun kama shi inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 18 bayan zargin sa da laifin cin amanar ƙasa da fallasa bayanan sirri na gwamnati.
Bayan zaman shekara 18 a gidan yari an kuma haramta masa fita daga ƙasar.
Kasancewar Isra'ila ta mallaki makamin nukiliya wasu na ganin bai kamata a ce ita ce za ta hana wasu su samu ba. To sai dai a tsawon shekaru Isra'ila ta riƙa tosma baki cikin lamurran ƙasashe a asirce da kuma a bayyane. Me ya sa take hakan?
A lokuta daban-daban, Isra'ila ta kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliya na ƙasashe uku a Gabas ta Tsakiya, wato a Iraqi da Syria da kuma Iran.
Babban abin da Isra'ila ke cewa tana dogaro da shi wajen daƙile yunƙurin ƙasashe na mallakar makamin shi ne "dalilai na tsaro".
An samar da ƙasar Isra'ila ne a shekarar 1948 inda ta yi yunƙurin ƙulla alaƙa da ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya. Kuma ta yi yaƙi da ƙasashen na Larabawa.
Kai tsaye Isra'ila ta yaƙi ƙasashe irin su Masar da Syria da Lebanon da Jordan, sannan a wannan shekarar ta yi yaƙin kwana 12 da Iran.
Duk da cewa an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Masr da Isra'ila, amma har yanzu babu wata alaƙa ta diflomasiyya tsakanin Isra'ilar da ƙasashen Syria da Iran.
Isra'ila na matuƙar adawa da Iran, tana cewa matakin Iran na inganta makamashin Uranium barazana ce gare ta.
Bari mu duba wasu ƙasashen da Isra'ila ta kai wa hare-hare sanadiyyar ayyukansu na nukiliya.
Iraqi – Operation Opera
Isra'ila ta yi katsalandan a shirin nukiliyar Iraqi, kasancewar ƙasar ta Iraqi ta samar da rundunar soji mai ƙarfi a lokacin mulkin Saddam Hussein.
Dakarun sojin Iraqi sun samu wannan ƙarfin ne ta hanyar mallakar jiragen yaƙi da makamai masu linzami daga ƙasar Rasha - wani abu da ya zama abin fargaba ga Isra'ila.
A ɓangare ɗaya kuma shirin inganta makamashin nukiliyar Iran ya zamo barazana ga Isra'ila. Iraqi ta kasance tana gudanar da aikin inganta nukiliyar ne a wani wuri da yake da nisan kilomitoci kadan daga Baghdad, babban birnin ƙasar.
Gwamnatin Saddam Hussein ta cimma yarjejeniya da Faransa domin samar da cibiyar inganta makamashin uranium. A dalilin haka ne masana kimiyya na Faransa suka fara aikin gina wata cibiyar nukiliya da aka sanya wa suna Osiraq, a kusa da babban birnin ƙasar.
Duk da cewa Iraqi ta bayyana cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, amma Isra'ila ta ƙaryata hakan.
Daga nan ne Isra'ila ta yanke shawarar ɗaukar mataki kan Iraqi, inda ta yi amfani da rikicin Iraqi da Iran a matsayin wata dama.
A cikin shekarar 1981, jiragen yaƙin Isra'ila na F-15 da F-16, ƙarƙashin abin da suka yi wa lakabi da 'Operation Opera' suka kai hari tare da lalata cibiyar ayyukan nukiliyar Iraqi.
Wannan ne lokaci na farko da wata ƙasa ta daban ta kai wa wata ƙasa farmaki kan cibiyar ayyukan nukiliya. An bayyana cewa harin ya wakana ne bayan kammala samar da cibiyar ta nukiliya.
Harin da Isra'ilar ta kai ya fusata Faransa, inda tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac ya yi tir da matakin.
Syria – Operation "Outside the Box"
Ƙiyayyar da ke tsakanin Syria da Isra'ila abu ne daɗaɗɗe. Syria na daga cikin ƙasashen Larabawa da suka yaƙi Isra'ila, musamman a yaƙin kwana shida da aka kara da kuma yaƙin da aka yi a 1967 da 1973.
Daga waɗannan rikice-rikice ne Isra'ila ta samu damar ƙwace wasu yankuna na Syria, wato Tuddan Gola, waɗanda har yanzu suke hannun ƙasar ta Isra'ila.
Har yanzu ƙasashen ba su da alaƙa ta diflomasiyya, amma a ɓangare ɗaya Iran na da alaƙa ta ƙut da ƙut da Syria.
A cikin shekara ta 2004, Isra'ila ta samu wasu bayanan sirri da ke cewa Syria ta fara aikin inganta makamashin uranium tare da taimakon wasu da ake zargin masana nukiliya ne daga Koriya ta Arewa.
Bayanan sun tabbatar da cewa ana gina cibiyar nukiliya ta al-Kibar a lardin Deir al-Zour, da ke a nisan kilomita 450 daga Damascus babban birnin ƙasar.
Isra'ila ta tsara wani shiri na na kai hari kan cibiyar nukiliyar ta Syria wanda ta yi wa laƙabi da "Operation Outside the Box".
A cikin dare, ranar 5 ga watan Fabarairun 2007, jiragen yaƙin Isra'ila na F-15 da F-16 suka kai hari.
Domin kauce wa garkuwar hare-haren Syria, jiragen sun ratsa ta saman bahar Maliya suka kai hari kan cibiyar nukiliyar da ke kusa da iyaka da Trukiyya.
Tun daga wancan lokaci da aka lalata mata cibiyar nukiliyar tata, har yanzu Syria ba ta sake komawa kan batun nukiliyar ba.
A wancan lokaci gwamnatin Syria ta fitar da sanarwa inda ta ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari kan wani gini da ke cikin sansanin soji, amma ba su ambaci cewa cibiyar sarrafa nukiliya ba ne.
A nata ɓangaren, ita ma Isra'ila ba ta ce ta kai hari kan cibiyar ayyukan nukiliya ba. Sai dai daga baya, a shekarar 2018, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa harin da ƙasarsa ta kai a 2007 ta kai ne kan cibiyar ayyukan nukiliya ta Syria.
"Gwamnatin Isra'ila da dakarun Isra'ila da kuma hukumar Mossad sun gurgunta duk wani shiri na Syria na mallakar makaman nukiliya," kamar yadda Netanyahu ya rubuta a shafinsa na X, lokacin da yake yaba wa dakarun tsaro na ƙasar.
Iran - Operation Rising Lion
Wannan ne yakin da Isra'ila ta ƙaddamar kan Iran a ranar 13 ga watan Yunin 2025, inda ta kai farmaki a cibiyoyin ayyukan nukiliyar Iran da sansanonin soji da kuma kan masana da ke jan ragamar shirin nukiliya na ƙasar.
Harin da Isra'ilar ta kai ya janyo martani daga Iran ta hanyar harba tarin makamai masu linzami kan biranen Isra'ila.
Ƙasashen biyu sun kwashe kwana 12 suna musayar wuta, lamarin da ya kai ga Amurka ta yi amfani da jiragenta da manyan bama-bamai wajen kai hari kan wasu cibiyoyin nukiliyar Iran.
Lamarin ya ƙara ruruta zaman ɗarɗar da ake yi a Gabas ta Tsakiya inda ƙasashe da dama suka riƙa kira da a kai zuciya nesa domin gudun ƙazancewa da faɗaɗar yaƙin.
A ƙarshe ƙasashen biyu sun amince da batun tsagaita wuta bayan kowane amgare ya yi ikirarin nasara.
Daga baya an yi ta tababa kan ko Isra'ila da Amurkar sun yi nasarar lalata shirin nukiliyar na Iran.
Amurka ta ce bayananta sun nuna cewa ta mayar da shirin nukiliyar na Iran baya da kimanin shekara biyu, sai dai a bangare ɗaya Iran ta ƙi bai wa jami'an hukumar kula da makamashin atam ta duniya damar ziyartar cibiyoyin da aka kai hari.
Wannan ya sanya babu mai cikakkiyar masaniya kan abin da ya faru da cibiyoyin da kuma shirin nukiliya na ƙasar.
Daga ƙarshe ma Iran ɗin ta ayyana yanke hulɗa da hukumar ta IAEA.