Saudiyya ta yunƙuro domin kawo ƙarshen yaƙin Yemen

Asalin hoton, EPA
Saudi Arabia ta ɗauki matakin kawo ƙarshen yaƙin da take jagoranta da 'yan Houthi da ke mulki a Yemen tun 2015.
Makwabciyar ta Yemen ta aika wa 'yan Houthin goron gayyata, zuwa birnin Riyadh domin tattaunawar da za ta kai ga dakatar da bude wuta ta dindindin da kuma tabbatar sasanto da zaman lafiya.
Wasu rahotanni daga kafofin da ke da alaka da ‘yan Houthi na cewa, an riga an dauki ‘yan tawagar zuwa babban birnin Saudiyyar domin fara wannan tattaunawa.
Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya wadda ta fitar da sanarwar ta ce an gayyaci tawagar ‘yan Houthin zuwa kasar ta Saudiyya ba wai kawai domin tattaunawar da za ta kai ga dakatar da bude wuta dindindin ba, har ma da nemo mafita ta siyasa da za ta kasance karbabbiya ga dukkanin bangarorin da ke rikicin a Yemen.
Wannan ita ce ziyara ta farko ta ‘yan Houthin a Saudiyya tun 2014, lokacin da hukumomin Saudiyyar suka kaddamar da yaki domin mayar da gwamnatin Yemen wadda suke mara wa baya, wadda ‘yan Houthi da ke samun goyon bayan Iran suka hambarar.
Bayan mummunan rikicin da aka shafe shekaru ana yi, kusan a iya cewa an dakatar da dukkanin wani babban gumurzu, duk da cewa a kwanan nan ne wa’adin yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta baya-bayan nan ya kawo karshe.
Tattaunawar za ta hada da biyan albashin ma'aikata 'yan Yemen da sake bude filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa da sakin fursunoni da tsararru da kuma sake gina kasar ta Yemen.
Watanni da dama da suka wuce an ga jerin matakai da bangarorin ke dauka na neman sasantawa, matakan da suka hada da musaya fursunonin yaki masu yawa abin da sa har ake ganin cewa bisa ga dukkan alamu kila yakin ya kama hanyar zuwa karshe.
Wannan mataki na diflomasiyya da ta aika da goron gayyata ga jami’an Houthi zuwa birnin Riyadh, ba shakka zai farfado da wannan fata, duk kuwa da cewa har yanzu akwai manyan batutuwa da ba a kai ga magance su ba, kuma ana ganin ba lalle ba ne Yemen ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali na dindindin a nan kusa.










