‘Yadda muka maƙale a tsakiyar teku bayan man jirgi ya ƙare’

Doudou Diop na zaune da mahaifiyar sa da kanin sa
Bayanan hoto, Doudou Diop (tsakiya) ya dawo Kafoutine yana tare da iyalinsa bayan ya bace tsawon mako guda yana kokarin isa tsibirin Canary
    • Marubuci, Nicolas Negoce
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, Kafountine, Senegal

"Mun kai wajen mutane 140 da muka hau jirgin ruwa a gabar tekun da tsakar dare, da misalin karfe 2 na dare."

Doudou Diop, mai shekaru 30 daga kasar Senegal, ya yi sallama ransa a kan tafiya mai hatsarin gaske cikin wani kwale-kwale zuwa Turai, inda ya yi tafiyar kilomita 1,700 daga Senegal zuwa tsibirin Canary na Spain.

Wannan hanya ta tekun Atlantika ta kasance cikin labarai bayan wata kungiya mai zaman kanta ta bayyana cewa wasu jiragen ruwa guda uku dauke da mutane akalla 300 sun bace tun karshen watan Yuni.

"Na yi tafiya zuwa kauyen kamun kifi mai nisa da ake kira Kafountine a kudancin Senegal, inda daga nan ake fara tafiya."

Wuri ne da daruruwan mutane ke tashi ko wace shekara don neman ingantaciyar rayuwa a Turai.

Na ci karo da Doudou Diop yana zaune a bakin barandar gidansa a cikin lokacin da ake zabga ruwan sama da tsawa, dukan matan danginsa sun taru a kusa da shi.

"Mun tashi ba tare da wata matsala ba kuma mun yi nasarar zuwa Morocco," in ji shi.

"Muna da nisan kilomita 500 daga tsibirin Canary sai kwatsam injinmu ya tsaya. Man fetur ya kare kuma muka makale a tsakiyar teku inda muka kasa ci gaba."

Ya ce hukumomin kasar Moroko sun dauko dukkan su 140 tare da kai su birnin Nouadhibou mai tashar jiragen ruwa mafi kusa da ke kasar Mauritania.

..

"Sun dauki sunayenmu da shaidarmu kuma suka sanya mu a cikin motocin da za su komar da mu gida Senegal."

An yi Sati ɗaya da ɓacewarsa saboda haka danginsa sun ji daɗin dawowar sa cikin ƙoshin lafiya.

Babu tabbas ko an ambaci jirgin ruwan da yake ciki a wata sanarwar da aka fitar.

A halin da ake ciki kuma, takaddama ta barke tsakanin gwamnatin Senegal da wata kungiyar 'yan gudun hijira da ake kira 'Walking Borders' game da bakin haure nawa aka yi hasara a teku.

Batun ya bazu a kafafen yaɗa labarai

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wadda ta kafa kungiyar 'Walking Borders', Helena Maleno, ce ta fara ankarar da mutane a ranar tara ga watan Yuli.

Ta ce ta tuntubi hukumomi a Senegal da Mauritania da Morocco da Spain, inda ta bukace su da su shiga aikin neman jiragen ruwan da suka bata.

Hukumomin kasar Spain sun ceto bakin haure 86 daga cikin kwale-kwalen da ya taso daga tsibirin Canary a lokacin da suke aikin neman mutanen da suka bata a kwale-kwalen.

Daga nan ne ma'aikatar harkokin wajen Senegal ta fitar da sanarwa.

"Binciken da aka gudanar ya nuna cewa wadannan bayanan ba su da tushe," in ji ta, ta kara da cewa an ceto 'yan kasarta 260 a yankin ruwan Maroko tsakanin 28 ga watan Yuni zuwa 9 ga Yuli.

Daga nan ne kungiyar 'Walking Borders' ta fitar da wani karin bayani, inda ta ce ta samu damar tabbatar da cewa wadanda aka ceto da gwamnatin Senegal ta ambata sun yi daidai da sauran jiragen ruwa "wadanda su ma suka bar gabar tekun Senegal amma ba kwale-kwalen da ke dauke da mutane 300 ba".

A ranar 13 ga watan Yuli, wani jirgin ruwa dauke da bakin-haure 41 da suka tashi daga kasar Senegal ya sauka a tsibirin Canary.

Tekun Atlantika tare da jiragen ruwa na katako a gaba.
Bayanan hoto, Kafountine bakin teku inda da yawa suka fara tafiya

Yayin da nake kokarin tattara bayanai, na samu mace guda a cikin Kafountine wadda ta ce akwai wani a cikin danginta da ya ɓata. Ta so a ɓoye sunanta kuma ta gaya mani cewa ta daina jin duriyar ɗan'uwanta dan shekara 17.

Da alama yana cikin ɗaya daga cikin waɗannan jiragen ruwa uku, "Ina jin tsoro, ba mu da wani labari game da shi," in ji ta. "An yi kwanaki."

Wani jami’in tsaron yankin da bai son shi ma a bayyana sunansa ya shaida cewa, “Akwai matukar rudani game da bacewar mutane 300”.

Jami’in ya kara da cewa, “Baya ga wannan matar, a nan garin babu wanda ya kai wa hukuma ko jami’an tsaro cewa suna neman ‘yan uwansu.

Amma wannan ba abin mamaki ba ne saboda mutane da yawa sun fito daga wasu yankuna ko ma makwabta ne, kuma ba su da alaƙa da ƙauyen.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutane 559 ne suka rasa rayukansu a shekarar da ta gabata a kokarinsu na isa tsibirin Canary daga Senegal.

Kuma a watanni shida na farkon wannan shekara kadai, tsibiran Canary sun karbi bakin haure fiye da 7,000.

Mafarkina bai zama gaskiya ba

Yanayin tattalin arziki mai tsauri yana nufin a kodayaushe akwai tarin mutane masu neman damar samun ingantacciyar rayuwa.

Doudou ya rayu a yankin kudancin Casamance na Senegal duk tsawon rayuwarsa. Bayan mutuwar mahaifinsa, ya ce matsi ya hau kansa kan ɗaukar nauyin iyalinsa a matsayin sa na ɗan fari.

"Ina da burin samun ingantacciyar rayuwa, kuɗi masu yawa don in kula da matata da 'yata, da mahaifiyata da sauran dangina," in ji shi, ya kara da cewa kujera a cikin kwale-kwalen ya kai CFA 400,000 (wato dalar Amurka 682).

“Na tafi ba tare da na sanar da kowa ba, na yi shirin tafiya Turai ne saboda babu komai a nan, ba ni da komai."

"Na ji takaici saboda ina son zuwa Spain, ina da abokai da suke can kuma suna jira na."

A tsakiyar Kafountine, akwai gungun matasa zaune a cikin inuwa. Wasu na yin wasannin allo na gargajiya yayin da wasu kuma ke ta ce-ce-ku-ce kan siyasa.

Mataimakiyar magajin gari sanye da wani koren gyale mai haske a gaban wani jirgin ruwan katako.
Bayanan hoto, Gnara Diabang Ba ita ce mataimakiyar magajin gari kuma tana taimaka wa matsasa masu gajeran hali

Gnara Diabang Ba, tana daya daga cikin mataimakan magajin gari, kuma 'yar jam'iyyar adawa.

“A gaskiya abin ya dame ni, abin bakin ciki ne ganin yadda muka shahara saboda bakin haure da ke tashi zuwa Turai ko kuma kokarin tafiya Turai.

"A matsayina ta zababbiyar jami'ar karamar hukuma, ina jin nauyin da ya rataya a wuyanmu, idan muka ce matasa su zauna, dole ne mu samar musu ayyukan yi, da ilimi mai kyau, idan ba mu yi haka ba, yana nufin mun gaza."

Magajin garin David Diatta ɗan jam’iyya daya ce kuma ya yarda da ra’ayinta, inda ya kara da cewa yanayin tsaro na musamman a yankin shi ma ya taka rawa.

Matasa yan acaba a kan babur suna jiran masu hawa
Bayanan hoto, Matasa na fuskantar rashin tabbas a rayuwa

Rashin aikin yi na matasa ya kai kashi 40 cikin 100, hatta tsakanin wadanda suka kammala jami'a.

"Muna shan wahala a nan, babu ayyukan yi, babu taimako daga hukumomi," in ji Ibrahima ɗan shekara 28 da ya kammala karatun ilimin halayyar ɗan'adam a jami'a.

"Yawancin abokaina sun hau kwale-kwalen kamun kifi don isa tsibirin Canary kuma sun yi nasara. Muna ganin su a shafukan sada zumunta kuma hakan akwai bambanci.

"Da a ce zan iya tafiya wata rana amma ina bukatar kudin."