Bikin ranar masoya a yayin takaicin cin zarafin mata cikin hotunan Afirka

.

Asalin hoton, MONICAH MWANGI/REUTERS

Bayanan hoto, A ƙasar Kenya mata sun gudanar da bukin ranar masoya ta duniya cikin alhini saboda cin zarafin da mata suke fuskanta a ƙasar.
.

Asalin hoton, MOHAMED MESSARA/EPA

Bayanan hoto, Oumy Diop 'yar ƙasar Senegal lokacin gasar ninkaya da aka gudanar a Qatar ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, HENRY NICHOLLS/AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin Acaye Kerunen Ayelele 'yar ƙasar Uganda ta na kallon kayan adon ɗakin da ta ƙirƙira a bikin nuna kayan da aka yi da kaba a birnin London.
.

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/AFP

Bayanan hoto, An yi baje kolin kayan da Ismaila Jallow ɗan ƙasar Gambia ya dinka a birnin Abidjan da ke ƙasar Ivory Coast.
.

Asalin hoton, CEM OZDEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Kashegari membobin ƙungiyar 'yan uwa ta Layene sun gudanar da biki karo na 144
.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Ranar Laraba titin Adderley inda ake sayar da furanni a birnin Cape Town ya yi cikar kwari da masu sayen furanni a ranar masoya ta duniya.
.

Asalin hoton, AHMED JALLANZO/EPA

Bayanan hoto, A ranar ne kuma wasu masoya suka yi musayar fure a gaɓar kogin Monrovia babban birnin ƙasar Liberia.
.

Asalin hoton, SIA KAMBOU/AFP

Bayanan hoto, Dubban magoya baya sun yi dandazo a titunan birnin Abidjan don ganin 'yan wasan 'kwallon Ivory Coast ranar Litinin.
.

Asalin hoton, DANIEL BELOUMOU OLOMO/AFP

Bayanan hoto, Ivory Coast ta yi nasara kan Najeriya da ci 2 da 1 lokacin wasan ƙarshe ranar Lahadi.