Abin da ya sa Yahudawan Birtaniya ke fuskantar sauyi mafi girma a shekara 60

Abin da ya sa Yahudawan Birtaniya ke fuskantar sauyi mafi girma a shekara 60
    • Marubuci, Aleem Maqbool
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Religion editor
    • Marubuci, Catherine Wyatt
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Religious Affairs producer
  • Lokacin karatu: Minti 8

Shugaban kwamitin wakilai na Yahudawan Birtaniya Phil Rosenberg ya ce "Shekara biyun da suka gabata ne masu matuƙar wahala." "Ina tunani Yahudawa sun ɗanɗana kuɗarsu a baya-bayan nan."

Ya ce rikici a Gabas ta Tsakiya ya yi tasiri sosai ga al'ummar Yahudawan Burtaniya.

"Hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba kowa yaji a jikinsa saboda akwai Yahudawa ƴan Birtaniya da aka kashe a harin farko akwai kuma mutanen da aka yi garkuwa da su.

"Yaƙin da ya biyo bayan ɓarnar da aka yi a Gaza ya yi muni. Sannan akwai ƴan ta'adda da suka dabaibaye rikicin an kuma samu ƙaruwar ƙyamar baƙi lamarin da ya haifar da hare-hare masu tsanani."

Harbin da aka yi a gaɓar tekun Bondi a ƙarshen makon da ya gabata, wanda ya shafi al'ummar Yahudawa a lokacin bukukuwan Hanukkah da kuma harin da aka kai wata majami'a a Manchester a rana mafi tsarki a kalandar Yahudawa Yom Kippur, tare da abubuwan da suka faru a Gabas ta Tsakiya cikin shekara biyu da suka gabata, sun yi tasiri mai yawa ga Yahudawan Birtaniya da yawansu ya kai kimanin 300,000.

Tun bayan yaƙin shekara ta 1967 a Gabas ta Tsakiya ba a yi tunanin Yahudawan Birtaniya za su fuskanci irin wannan matsin lamba ba.

An samu ra'ayoyi daban-daban daga al'ummar Yahudawa, da dama daga cikin sun bayyana yadda suka fuskanci sauyin rayuwa cikin shekara biyu da suka gabata.

Laifukan cin zarafi da ƙyamar Yahudawa

Ben Dory mai shekara 33 da ke zaune a Landan ya ce: "Akwai matakin da ake ganin kamar masu abota da Yahudawa za su fi fahimta." "Na samu abokai Yahudawa da dama."

Kazalika na kai ga samun babban matsayi a wurin ibadar Yahudawa lamarin da ya sa na ƙara jajircewa wajen yaƙi da ƙyamar Yahudawa.

"Na san Yahudawan da idan za su je wurin Ibada, za su ajiye kippah (hular su) a cikin aljihu har sai sun shiga idan zasu fita kuma sai si sake cire hular.

Bayan harin da aka kai Australia a ƙarshen makon da ya gabata, Ben ya faɗa mani cewa "ya firgita amma lamarin bai ba shi mamaki ba," ya ce abin da ya faru "tsari ne na ƙyamar Yahudawa da ke faruwa a duniya".

Ya ce "Tun da jimawa akwai fargaba yayin duk taron da ke da alaƙa da Isra'ila. Amma yanzu Yahudawa suna jin cewa a kowanne lokaci suna cikin barazana, har ma a wuraren tarurrukan al'adu da addini da kuma siyasa," in ji shi.

Ya ƙara da cewar shekaru biyun da suka gabata sun mayar da shi ɗan siyasa-kuma mai goyon bayan Isra'ila sakamakon ƙaruwar da aka samu ta ƙyamar Yahudawa.

Ofishin al'amuran cikin gida na Birtaniya ya ce an samu rahoton kalaman ɓatanci ga Yahudawa da yawansu ya kai 1,543 a Ingila da Wales cikin watan Maris na shekara ta 2023, al'amarin ya ƙaru zuwa 3,282 a watan Maris na shekara ta 2024.

Wata cibiya mai kula da al'amuran tsaro tare da sanya ido kan ƙyamar da Yahudawa ke fuskanta a Birtaniya kusan shekaru 40, ta ce an samu tsananin ƙaruwar kalaman ɓatanci da kuma ƙyamar Yahudawa a shekaru biyu.

"Yahudawan da na sani sun fi damuwa da tsaro a Isra'ila saboda buƙatar tserewa idan ta taso ," in ji Ben.

Tun bayan da Isra'ila ta kafa ƙasa ra'ayin samar da "tsaro a Isra'ila" ya zama aƙida a zuciyar Yahudawa da dama, aƙidar ta ƙaru a yanzu sakamakon abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, kamar yadda wasu suka bayyana.

Dame Louise Ellman wata tsohuwar ƴar majalisa ta ce "Ban taɓa jin ƙasƙanci a matsayin Bayahudiya ba kamar yadda na ke ji yanzu," kuma duk Yahudawa haka suke ji .

Ta bar jam'iyyar Labour ne a shekarar 2019 saboda damuwar da ta nuna ta ƙin jinin baƙi a jam'iyyar inda ta sake komawa a shaekara ta 202, ta kasance shugabar majalisar wakilai mai zaman kanta ta hadin gwiwa wata babbar ƙungiya mai wakiltar Yahudawa a Burtaniya.

Dame Louise tana halartar wurin ibadar Yahudawa wato Synagogue da ke Arewacin Manchester. A can ta yi aure kuma a can ta haifa ɗanta Bar Mitzvah.

A can ne kuma aka kai harin watan Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu yayinda wasu uku suka jikkata.

Kusancinta da wurin ibadar Yahudawan ya ƙaru saboda tsoron da ta ke ji, ta ƙara da cewa. "mutane sun firgita kowanne lokaci suna ji kamar basu da kowa,"

"Wannan lamari yana matuƙar damuna."

Faruwar wannan al'amari ya ƙara sanya ta tsananin goyon bayan Isra'ila. "Na san akwai bambanci game da yadda mutane da dama musamman matasa ke kallon wannan lamari, to amma fa tsiraru ne.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka cimma matsaya ta daban game da Isra'ila ita ce Tash Hyman darektan fina-finai mai shekaru 33 daga London.

Ko da yake a cikin shekaru biyu da suka gabata ta ce tana da alaƙa da Yahudawa - misali ta fi karkata ga al'adun gwagwarmayar Yahudawa - sai dai bata goyon bayan Isra'ila.ba ta jin babban goyon baya ga Isra'ila.

Ta ce: "Na girma ne a inda Yahudanci ya ke danganta komai da Isra'ila, amma abubuwan da Isra'ila ke yi ya fara hana ni kwanciyar hankali.

Ta yi watsi da ra'ayin cewa Isra'ila "mafaka ce ga Yahudawan Birtaniya."

''Ina jin ƙasƙanci a Birtaniya saboda abin da Isra'ila ke yi a Gaza.'' ta yi watsi da batun cewar Isra'ila ce mafakar Yahudawan Birtaniya.

Aƙalla mutum 1,200 aka kashe da Hamas ta kai hari Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 an kuma yi garkuwa da sama da mutum 250. Tun daga wannan lokacin, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza sama da Falasɗinawa 70,000 ne suka mutu sakamakon harin da sojojin Isra'ila suka kai.

A yanzu tana halartar majami'a amma ta kewaye kanta da masu ra'ayi iri ɗaya na siyasa - tana mai nuni da cewa hare-haren Hamas da yaƙin Gaza sun haifar da zazzafar muhawara tsakanin Yahudawan Burtaniya game da Isra'ila.

Yahudanci: Rabuwar kai tsakanin al'umma

Cibiyar binciken tsare-tsaren Yahudawa a Birtaniya ta fidda rahoton da ya ce tun kafin harin da aka kai Manchester akwai rabuwar kai tsakanin Yahudawa game da Isra'ila.

Bincike ya nuna tsakanin Yahudawa 4,822 ƴan sama da shekara 16, kashi 64 ne suka amince su Yahudawa ne, amma tsakanin masu shekara 20 zuwa 30 kuwa kashi 47 ne suka amince su Yahudawa ne yayin da kashi 20 na rukunin masu wannan shekaru ba sa bayyana kawunan su a matsayin Yahudawa.

Adadin Yahudawan da suke Allah-wadai da tsarin Isra'ila tun shekara ta 2022 ya ƙaru tsakanin matasa da tsoffi, misali kashi 30 na ƴan shaekaru 50 zuwa 59 ne suke ƙin tsarin Yahudanci.

a shekara ta 2024 kashi 7 na ƴan shekaru 50 zuwa 59 ne suka ce basa goyon bayan tsarin Yahudawa.

Robert Cohen ɗalibi a King's College da ke London ya gudanar da binciken sa game da Yahudawan Burtaniya waɗanda a yanzu suke sukar yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, da kuma dalilansu na ɗaukar wannan matsaya.

Tsakanin watan fabrairun shekara ta 2023 zuwa Oktoban shekara ta 2024, ya yiwa mutane 21 da suka ɗauki wannan mataki tambayoyi, ya yi ƙarin haske game da abinda ya sa aka samu giɓi a tsakanin al'umma.

''Mun san ƴan zamani watau Gen Z na da ɗabi'ar son shiga a dama da su kuma suna son sanin gaskiyar lamari sannan suna da damuwa da abinda ya shafi shari'a." A binciken da na gudanar na fahimci har yanzu akwai al'adun su na Yahudawa cikin rayuwarsu.."

Wasu daga cikin waɗanda na yi magana da su da suka haɗa da Ben Dory, sun ce an samu rabuwar kai ne saboda matasa ba su da masaniya game da kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa.

Robert Cohen ya ce Yahudawan Birtaniya da ya tattauna da su na sona fitowa fili su soki Isra'ila game da Gaza amma za su so yin hakan tare da Yahudawan da za su fahimce su.

Bayan shekaru biyu matasan Yahudawan Birtaniya da dama sun koma goyon bayan Isra'ila.

'Ƙawayena sun juya min baya'

An haifi Lavona Zarum a Isra'la kafin a mayar da ita Burtaniya. Lokacin harin ranar 7 ga watan Oktoba tana ɗaliba kuma an naɗa ta shugabar ƙungiyar Yahudawa a jami'ar Aberdeen.

"Sannu a hankali ƴan matan da ke cikin ƙungiyar ƙawayena suka juya min baya."

Ta tuna yadda ta yi rayuwar kaɗaici da irin wahalar da ta ke fuskanta wajen ɗaliban da ba Yahudawa ba ne game da yadda suka kalli harin da aka kaiwa Isra'ila.

"Mutane ba sa iya bayyana ra'ayin su, tilas na dakatar da tambaya ko neman tattaunawa da su."

Lavona na da shekaru 21 yanzu. Ta mayar da hankalinta ga ƙawaye masu fahimta ko da akwai bambamcin ra'ayi

Rikici cikin hukuma

A cikin shekara biyu da suka gabata kwamitin majalisar wakilan Yahudawan Birtaniya na fuskantar ƙiki-ƙaka game da yadda za a gudanar da muhawara kan Isra'ila.

A farkon wannan shekara mambobin kwamitin 36 suka rattaba hannu kan wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da aka buga a jaridar Financial Times, inda suka bayyana rashin jin daɗi game da " tsaurin ra'ayin gwamnatocin Isra'ila" da kuma rashin kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tun ranar 7 ga Oktoba.

Wasiƙar ta ce'' muna fargabar makomar Isra'ila''

An dakatar da mambobi 5 na kwamitin saboda shirya wasiƙar.

Phil Rosenberg ya ce abin da ya fi damunsa shi ne tsaron Yahudawan Birtaniya da kuma yadda kwamitin ke duban kanta.

''Ya ƙara cewar abin takaici ne a ce muhimmin bikin Yahudawa a wannan ƙasa shi ne ranar tunawa da kisan kiyashi. Sannan ilimi mai muhimmanci da ake koyarwa shi ne na kisan kiyashi, dukkan waɗannan abubuwa suna da amfani amma ba su kaɗai ba ne irin gudummawar da Yahudawa suka bayar a tarihi ba.''

A watan Mayun shekara ta 2024 lokacin da ya fara zama shugaban hukumar, Phil Rosenberg ya yi magana game da neman ƙarin bikin gudummawar da Yahudawa suka bayar ga rayuwar Birtaniyya.

"Tabbas yaƙi ya ƙara haifar da matsala saboda da ka buɗe kafar yaɗa labaran Yahudawa labarin da zaka gani na tashin hankali ne.

"Yanzu a Burtaniya a matsayina na Bayahude ba na jin daɗi."

Game da rabuwar kai tsakanin Yahudawan Burtaniya kuwa, Robert Cohen ya yi hasashen makoma ta dogara ne kan sakamakon da zai biyo bayan halin da ake ciki a Gabas ta tsakiya.

A ɓangaraen Ben Dory,musamman bayan harin da aka kai Bondi da Manchester damuwar sa ita ce tsaro.

"Ina ganin Yahudawan Birtaniya na tsaka mai wuya," in ji shi.

"Yadda Birtaniya za ta ɗauki matakan da suka dace cikin ƙanƙanin lokaci, shi zai tabbatar ko Yahudawa zasu samu cikakken tsaro a gaba.''