Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta rufe kofa kan ficewar Chiesa,Ortega zai ci gaba da taka leda a Man City
Liverpool ta rufe kofa kan zawarcin da kungiyar Besiktas ta kasar Turkiyya ke yi wa dan wasanta Federico Chiesa duk da cewa ba ta saka dan wasan Italiya mai shekara 27 a cikin 'yan wasanta na gasar zakarun Turai.(Liverpool Echo, external)
Watakila golanJamus Stefan Ortega mai shekara 32, ya ci gaba da zama a Manchester City har zuwa watan Janairu bayan kungiyar Trabzonspor, Ta Turkiyya da ake danganta da shi da ita ta yanke shawarar daukar golan Manchester United da Kamaru Andre Onana mai shekara 29. (Manchester Evening News, external)
Arsenal na kan gaba a kungiyoyin da ke rige-rigen siyan dan wasan tsakiya na Stuttgart Angelo Stiller bayan yunkurin daukarsa da Manchester United ta yi a bazara ya gamu da cikas. Sai dai Bayern Munich da Real Madrid na sha'awar dan wasan kasar Jamus mai shekara 24. (Express, external)
Tottenham ta yi yunkurin daukar dan wasan Paris St-Germain Senny Mayulu, mai shekara 19, kafin a rufe kasuwar cefanar da 'yan wasa kuma Chelsea da Manchester City suma suna zawarcin dan wasan na Faransa. (Teamtalk), external
Real Madrid na shirin zawarcin dan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, wanda ke shekara ta karshe a kwantiraginsa da Bayern Munich. (Bild - in German), external
Wolverhampton Wanderers na kyautata zaton ba bu wata matsala da za ta kunno kai a tattaunawar kulla sabuwar yarjejeniya da Jorgen Strand Larsen, mai shekara 25, sai dai yarjejeniyar za ta kunshi lokacin da kungiyar za ta salami dan wasan kasar Norway bayan ya yi watsi da tayin fan fiye da miliyan 50 da Newcastle ta yi masa har sau biyu a bazara. (Telegraph - subscription required), external
Newcastle da Manchester United da Aston Villa na son su dauko dan wasan Athletic Bilbao Daniel Vivian kuma watakila su iya cimma kudin Siyan dan wasan Sfaniya kan fan miliyan 35 a bazarar badi .(Fichajes - in Spanish, external)
Kawo yanzu Chelsea na son golan AC Milan Mike Maignan mai sheakara 30, duk da cewa sun gaza cimma matsaya daukar dan wasan Faransa a bazara kuma sun bayana jin dadi kan damar da suke da ita na samunsa a shekarar 2026 saboda a wannan lokaci ba shi kwatarangi da wata kungiya. (TBR Football, external)
Dan wasan Lyon da Belgium Malick Fofana, mai shekara 20, ya ja hankalin Chelsea da Liverpool a kasuwar sayar da 'yan wasa da aka yi a bazara. (Teamtalk), external
Tottenham na ci gaba da bin diddigin dan wasan Sunderland Dennis Cirkin kuma watakila za su sake siyan dan wasan baya na Ingila mai shekara 23, wanda ya fito daga kwalejin kwallon kafa ta Spurs, a watan Janairu. (TBR Football, external)
Shi ma dan wasan Osasuna, Flavien Enzo Boyomo na jan hankalin kungiyoyin kwallon kafa na firimiya kuma watakila ta sayar da dan wasan kasar Kamaru kan fan milyan 22 a kasuwar bazarar badi. (Fichajes - in Spanish, external)