Wace fallasa aka yi wa Trump, Bill Gates da ɗan Sarauniyar Ingila a cikin sabbin bayanan Epstein?

Wasu shugabanni

Asalin hoton, Alex Wong/Getty Images, Max Mumby/Indigo/Getty Images, Tom Brenner/Getty Images

    • Marubuci, Sakshi Venkatraman
    • Marubuci, Kwasi Gyamfi Asiedu
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta sake fitar da wasu miliyoyin takardu masu alaƙa da fitaccen kawalin nan Jeffrey Epstein, adadi mafi yawa na takardun da gwamnati ta fitar tun bayan doka ta tilasta fitar da takardun a shekarar da ta gabata.

Sabbin bayanan da aka fitar a ranar Juma'a sun ƙunshi shafuka miliyan uku da hotuna 180,000 a bidiyoyo 2,000.

Fitar da bayanan na zuwa ne mako shida bayan cikar wa'adin da ma'aikatar shari'ar Amurka ta bayar na yin hakan, wanda Trump ya sanyawa hannu kan tilasta fitar da bayanan Epstein ga duniya.

"Fitar da takardun a ranar Juma'a ya kawo ƙarshen shiryayyen tsarin tantance daftarin don tabbatar da gaskiya ga jama'ar Amurka da bin ƙa'ida," in ji mataimakin babban mai gabatar da kara Todd Blanche.

Takardun sun ƙunshi bayanin lokacin da Jeffrey Epstein ya kwashe a gidan yari - cikin har da rahoton lafiyar ƙwaƙwalwarsa - da mutuwarsa a gidan yarin da bayanan bincike game da Ghislaine Maxwell, mutumin a da aka samu da laifin taimaka wa Epstein wajen yaudarar ƙananan ƴan mata.

Haka kuma bayanan sun ƙunshi musayar saƙonin imel tsakanin Epstein da wasu manyan mutane.

A 2008 kotun wata kotu a Florida ta same shi da laifin kawalcin wata yarinya ƴar shekara 14.

A watan Agustan 2019 ya mutu a gidan yari, bayan da ka ɗaure shi kan laifin kawalcin ƴanmata.

A close photo of Jeffrey Epstein. He sits down and looks at the camera, wearing a dark coloured shirt

Asalin hoton, Getty Images

Epstein ya gayyaci 'Yarima' ya yaɗu da ƴar Rasha

Takardun sun nuna wata fallasa ga wasu manya a Birtanita.

Ciki har da na musayar imel tsakanin Epstein da wani mai suna "Yarima" - Da aka yi amanna cewa Yarima Andrew Mountbatten-Windsor - da aka tattauna cin abincin dare a Fadar Buckingham, inda aka gudanar da "wasu abubuwan sirri".

Wani saƙon da aka samu daga Epstein ya ƙunshi tayin gabatar wa "Yariman" wata yar Rasha mai shekara 26.

Sakon mai nuna aikata baɗala ba.

BBC ta tuntuɓi Andrew, da a baya aka fi sani da Yariman York, don jin ta bakinsa.

Mountbatten-Windsor ya fuskanci shekaru na bincike kan alaƙarsa da Epstein. Kodayake ya sha musanta aikata laifi.

Haka an musayar wasu saƙonnin Imel tsakanin Epstein da Sarah Ferguson, toshuwar matar Andrew.

Ɗaya daga ciki da aka yi ranar 4 ga Afrilun 2009, an kammala shi da "Masoyiya, Sarah, Mai jan kai.!!"

Ta kira shi da ''jarumi'' sannan ta ce ''Ina alfahari da kai''.

Epstein ya aika wa mijin Mandelson kuɗi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu saƙonnin imel ɗin sun nuna yadda Epstein ya aika £10,000 ga Reinaldo Avila da Silva, mijin Lord Peter Mandelson a 2009.

A cikin emel ɗin Epstein, da Silva sun yi cinkin yin tausa, inda ya aika lambar bankinsa ga kawalin.

Sa'o'i bayan haka Epstein ya ba shi amsa da cewa zai nemo rancen kuɗin domin bai wa SIlda, wanda ya auri Mandelson a 2023.

A wani saƙon an buƙaci Lord Mandelson ya tsaya a ɗaya daga cikin gidajen Epstein.

An aika saƙonin ne rana 16 ga watan Yunin 2009, lokacin da Epstein ke zaman kaso saboda samunsa da laifin kawalcin wata yarinya ƴar ƙasa da shekara 18.

Mafi yawan ɗaure Epstein da aka yi ana barinsa ya yi aiki a ofishinsa da rana, in dare ya yi a mayar da shi fursun ya kwana.

A watan Disamban 2024 aka naɗa Lord Mandelson jakadan Birtaniya a Amurka, to amma aka kore shi ƙasa da shekara guda, bayan da aka gano ya taɓa aika wa Epstein saƙon ƙarfafa gwiwa bayan samunsa da laifi.

Lord Mandelson ya sha nanatawa yin da-na-sanin abota da Epstein, wanda a baya ba a sani ba, ya ce bai taɓa gani Epstein ya aikata laifi ba.

Ambata sunan Trump ba adadi

An ambata sunan Shugaban Amurka sau ba adadi cikin sabbin takardun.

Trump ya yi abota da Epstein a baya, amma ya ce dangantarsu ta yi tsami shekaru da yawa da suka gabata kuma ya musanta cewa ya san laifukansa da suka shafi kawalci.

Daga ciki har da jerin sunayen da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta tattara a shekarar da ta gabata na zargin Trump da masu kiran waya suka yi wa Cibiyar Barazana ta kasa suka yi.

Yawancin waɗannan da alama sun dogara ne kan shawarwarin da ba a tabbatar da su ba da hukumar ta samu kuma an yi su ba tare da wata shaida ba.

Jerin ya ƙunshi zarge-zarge masu yawa na cin zarafin lalata da aka yi wa Trump da Epstein da sauran manyan mutane.

Trump ya sha musanta aikata ba daidai ba a alaƙarsa da Epstein kuma ba wadda ta taɓa zarginsa cikin waɗanda Epstein ya yi kawalcinsu.

Da aka tuntuɓe su kan sabbin zarge-zarge, Fadar White House da ma'aikatar shari'ar Amurka sun nuna wani layi cikin sanarwar da suka fitar.

"Wasu daga cikin takardun sun ƙunshi bayanai na ƙarya da aka ƙirƙira don Shugaba Trump da aka aika wa hukumar FBI tun kafin zaɓen 2020," a cewar ma'aikatar shari'ar Amurka.

"A gaskiya, ikirarin ƙarya ce tsagoranta, kuma in dai babu tabbaci a cikinsu to ma iya cewa an ƙirkire su ne domin ɓata wa Trump suna."

Epstein gayyaci Elon Musk 'wildest party' a tsibirinsa

Sabbain bayanan sun nuna musayar sakon imel tsakanin Epstein da Elon Musk.

Fitaccen biloniyar, wanda ba a zarge shi a aikata laifi ba, a baya ya ce Epstein ya gayyace shi zuwa tsibirinsa amma ya ƙi.

Sabbin bayanan sun nuna yadda Musk ya riƙa tattauna bulguronsa har fiye da sau ɗaya ciki har da wanda ya tambayi Epstein "YAushe za a yi partyn tsibirinsa da rana ko dare?

An ga yadda Epstein ya tambayi Musk kan adadin mutanen da zai je da su a jirginsa mai saukar ungulu, inda ya ce shi kaɗai zai je sai matarsa a lokacin, Talulah Riley.

Bill Gates ya 'ƙaryata' iƙirarin Epstein

Wani mai magana da yawun Bill Gates ya mayar da martani kan zarge-zargen da ke kunshe a cikin sabbin takardun - ciki har da cewa ya kamu da wata cuta ta hanyar jima'i - yana kiran kiran bayanan da "shirme da tsagwaron ƙarya".

Imel guda biyu da aka rubuta ranar 18 ga Yuli 2013 sun bayyana Epstein ne ya tsara su da nufin aika wa Gates, amma ba a sani ba ko an taɓa aika masa.

Dukansu an yi musayarsu tsakanin imel biyu na Epstein, yayin da babu asusun imel da ke da alaƙa da Gates da ke bayyane kuma duk imel ɗin ba sa hannu.

Akwi kuma wani imel na wasiƙar ajiye aiki a Gidauniyar Bill da Melinda Gates, inda a ciki aka koka game da sayan magani ga Gates "don magance wata cutar da ya ɗauka saboda jima'i da 'yan matan Rasha".

Sukar bayyana waɗanda aka ci zarafinsu

Gloria Allred, mai fafutikar kare ƴanci kuma lauyar da dama cikin waɗanda suka rufta komar Epstein ta shaida wa BBC cewa am bayyana sunayen waɗanda lamarin ya shafa da dama cikin sabbin takardun, ciki har da waɗanda ba a taɓa ambatarsu ba a baya.

Yawancin takardun da aka fitar ranar Juma'a sun ƙunshi tacewa mai girma. Dokar ta ba da umarnin cewa za a iya tace bayanan don kare waɗanda abin ya shafa ko bayanan da ake bincike a kai.

Har ila yau, ya ba da umarnin taƙaita abubuwan da aka yi da kuma tace su don shari'a.

Mataimakin babban mai shari'a Blanche ya ce matakin da aka ɗauka da nufin kare wadanda abin ya shafa kuma ma'aikatar shari'a ta sanya ɗaruruwan ma'aikatan da ke tantance takardun sama da watanni biyu don ganin an fitar a su cikin gaggawa.

Shin an kammala fitar da bayanan Epstein?

Babu tabbas ko wannan ya zama na ƙarshe game da fitar da bayanan Epstein.

Blanche ya ce fitarwar da aka yi ranar Juma'a "ya nuna ƙarshen cikakken tsarin tantance daftarin aiki da nazari" wanda ke nuna cewa abin da ya shafi ma'aikatar shari'ar Amurka, aikin ya ƙare.

To amma ƴan jam'iyyar Democrat na da ja, inda suka zargi ma'aikatar da ci gaba da riƙe wasu takardun - da ta ce mai yiwuwa za su kai miliyan biyu da rabi - ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba.

Dan majalisar wakilai na Democrat Ro Khanna - wanda tare da ɗan majalisar Republican Thomas Massie suka jagoranci ƙudirin dokar bayyana gaskiyar Epstein - ya ce yana da shakku.

"Ma'aikatar shari'ar ta ce ta gano fiye da shafi miliyan 6 na bayanan, amma sun fitar da miliyan 3.5 bayan sake nazari da tace su,'' in ji shi.

"Wannan ya haifar da tambayoyin cewa, ina sauran da aka riƙe. Zan jajirce don ganin ko ma'aikatar za ta sake fitar da wasu a nan gaba.''

Sai dai, duk da haka ko da wannan batu ya wuce a haka.

Mutane da dama - ciki har da makusanan Trump - za su jima suna imanin cewa akwai haɗin baki da aka yi don kare masu arziki da manyan mutane da ke a alaƙa da Epstein.