Birtaniya da Faransa sun gargaɗi Isra'ila kan kawo ƙarshen yaƙin Gaza

IDF sun riƙa kai hari Gaza tare da kashe dubban mutane tun bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Maris

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, IDF sun kai hare-hare a Gaza tare da kashe dubban mutane tun bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Maris
Lokacin karatu: Minti 4

Isra'ila ta fara yakin Gaza ne -bayan da Hamas ta ƙaddamar da hare-hare ranar 7 ga watan Oktoban 2023 - ta amfanai da manyan makamai da galibi saya mata, ko aka ba ta daga Amurka.

Haka ma sauran ƙawayen Isra'ila sun ba ta taimako ta ɓangarensu, musamman nuna goyon baya da nuna cewa suna tare da ita, sakamakon harin Hamas da ya kashe mutum 1,200 mafi yawancinsu fararen hula tare da kama mutum 251 domin yin garkuwa da su a Gaza.

To amma da alama yanzu Isra'ila ta fara rasa gyon bayan wasu manyan ƙawayen nata, bayanta da Birtaniya da Faransa da kuma Canada suka nuna damuwa kan halin da al'ummar Gaza ke ciki.

Ƙasashen uku sun yi kakkausar suka kan yadda Isra'ila ke aiwatar da yaƙin Gaza.

Sun ce dole ne Isr'ial ta dakatar da hare-harenta, wadanda firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce suna kai su ne domin kawar da Hamas, tare da ceto Isra'ilawan da suka rage a hannunta, tare da mayar da ɗaukacin Gaza ƙarƙashin ikon sojojin Isra'ila.

To amma sanarwar haɗakar ƙasashen uku ta yi watsi da iƙirarin Netanyahun tare da kiran tsagaita wuta.

Gwamnatocin ƙasashen uku sun ce ''bisa kakkausar murya suna adawa da matakin faɗaɗa ayyukan sojin Isra'ila a Gaza'', suna masu cewa ''halin wahala da galabaita da al'ummar Gaza ke ciki abu ne da ma za a iya jurewa ba''.

Sun kuma yi kira da a saki sauran Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su, sannan sun amince cewa bayan ''mummunan harin'' da Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba, Isra'ila na da ''damar kare kanta daga ta'addanci. To amma faɗaɗar yaƙin bai dace ba''.

Ƙasashen uku sun ce matakin Netanyahu na bari a shigar da abin da ya kira ''taƙaitaccen'' abinci zuwa Gaza sun ce ''bai wadatar ba''.

Netanyahu ya mayar da martani yana mai cewa "shugabanni a ƙasashen uku na nuna wani babban goyon baya kan harin ƙare dangi da aka kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba tare da kiran aiwatar da ire-iren hakan a nan gaba''.

Ya dage cewa za a ƙare yaƙin ne idan Hamas ta maido da duka Isra'ilawan da suka rage, sannan suka ajiye makamansu, tare da amincewa jagororinsu su tafi zaman gudun hijira sannan kuma a kawar da masu ɗauke da amakamai a Gaza.

''Babu ƙasar da za ta amince da da ƙasa da haka, don haka Isra'ila mba za ta amince ba,'' in ji shi.

Mutane na jiran agaji

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Motocin agaji biyar ne kawai suka shiga Gaza a ranar Litinin
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Netanyahu - wanda yanzu haka ake nema a ƙarkashin sammacin kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya kan zargin aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil Adama, waɗanda ya musanta - na fuskantar matsin lamba daga ƙasashen duniya don kawo ƙarshen hana shigar da kayan agaji, bayan da bincike hukumomin duniya suka yi gargadin cewa za a fuskanci yunwa.

A taron ƙolin da aka yi a birnin London tsakanin ƙungiyar EU da Birtaniya, shugaban majalisar Tarayyar Turai, António Costa, ya kira matsalar jin kai a Gaza, "abin takaici ne inda ake keta tsararrun dokokin duniya, kuma tunkarar dukkan al'ummar yankin da karfin soja da bai dace ba".

"Dole ne a samar da hanyoyin samar da agaji cikin aminci, cikin gaggawa kuma ba tare da tarnaƙi ba," in ji shi.

To sai dai matakin Netanyahu na bari a shigar da ''taƙaitaccen agaji'' zuwa Gaza ya fusknaci adawa daga manyan abokan ƙawancen gwamnatinsa.

Ministan tsaron ƙasar Itamar Ben Gvir - wanda a 2007 aka samu da laifin iza wariyar launin fata da goyon bayan ƙungiyar Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi da Isra'ila ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci - ya yi korafin cewa matakin da Netanyahun "zai bai wa Hamas iskar shaƙa tare da ƙarfafata, yayin da Israwan da ake garkuwa da ke maƙale cikin ramuka''.

Manyan motocin agaji biyar ne kacal suka shiga Gaza a ranar Litinin, yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama da kuma kamana atilare tare da kashe ƙarin Falsɗinawa fararen hula ciki har da ƙananan yara.

Masu adawa da ruguza Gaza da Isra'ila ke yi tare da kashe dubban Falasɗinawa fararen hula za su ce gwamnatocin Faransa da Birtaniya da kuma Kanada sun makara da wanann kira nasu.

Macron da Netanyahu

Asalin hoton, Reuters

Abin da zai fi wa Isra'ila muni game da sanarwar ƙasashen uku shi ne yadda suka ce "ba za mu zuba ido muna ganin gwamnatin Netanyahu ta ci gaba da aiwatar da waɗannan munanan ayyuka ba. Idan Isra'ila ba ta daina kai hare-haren soji ba tare da ɗage takunkumi kan agaji, to za mu ɗauki ƙwaƙƙwaran matakin martani."

Sai dai ba su fayyace irin matakin da za su ɗauka ba. Amma wataƙila yana iya zama takunkumi. Babban mataki da ƙasashen uku za su ɗauka shi ne amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Faransa dai na tunanin shiga cikin jerin ƙasashe 148 da suka amince da hakan a wani taro da za ta jagoranta tare da Saudiyya a birnin New York a farkon watan Yuni.

A baya Birtaniya da Faransa sun yi magana kan amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa.

Isra'ila, wadda ba ta ji daɗin matakin ba, ta ce ƙasashen uku za su bai wa Hamas nasara ne. Sai dai yanayin kalaman da ƙasashen uku suka yi amfani da sua sanarwar tasu, sun nuna cewa Isra'ila ba za ta iya matsa musu ba.