Jagorar adawa a Birtaniya Kemi ta ce ta daina ɗaukar kanta 'yar Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ottilie Mitchell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugabar jam'iyyar adawa ta Conservative a Birtaniya Kemi Badenoch ta ce ta daina ɗaukar kanta a matsayin 'yar Najeriya kuma rabon da ta sabunta fasfonta tun a shekarun 2000.
Badenoch, wadda aka haifa a Birtaniya, ta girma a Najeriya da Amurka kafin ta koma Birtaniya tana da shekara 16 domin cigaba da karatunta.
Da take magana a shirin podcast na tsohon ɗanmajalisa Gyles Brandreth, ta ce "ta zama 'yar Najeriya kawai saboda kakanninta" amma "indai don al'adu ne, gaskiya ni ba 'yar can ba ce".
A shekarar da ta gabata Badenoch ta fuskanci suka daga Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima, inda ya ce tana "wulaƙanta" ƙasar.
Badenoch ta yi bayani game da tasowarta a Legas da ke kudancin Najeriya.
"Na san ƙasar sosai da sosai, ina da 'yan'uwa da yawa a can, kuma ina bin abubuwan da ke faruwa," in ji ta. "Amma gida a wurina shi ne inda iyalina suke."
Game da ƙin sabunta fasfonta kuma, ta ce: "Na daina alaƙanta kaina da shi yanzu. Na yi akasarin rayuata a Birtaniya kuma ban taɓa jin ina buƙatar na yi hakan ba."
Ta ƙara da cewa: "Na zama 'yar Najeriya ne saboda iyayena, bayan an haife ni, duk da cewa ba a can aka haife ni ba...amma kuma ta ɓangaren al'adu, ni ba 'yar can ba ce gaskiya."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce lokacin da za ta je Najeriya bayan mutuwar mahaifinta, dole sai da ta nemi biza "wanda abu ne mai wuya".
Ta ce zaman da ta yi a Najeriya tun tana ƙarama ya yi tasiri a tunaninta game da siyasa da kuma dalilin da ya sa ta "ƙara tsanar tsarin gurguzu".
"Ina yarinya, ina iya tuna yadda na dinga jin cewa ba wurin zamana ba ne," a cewarta, tana mai cewa "lokacin da na dawo Birtaniya sai na ji nan ne gida".
Ta ce dalilin da ya sa ta koma Birtaniya ba abin ɓacin rai ne. "Kawai iyayena sun ji cewa: 'Ba ki da wata makoma a ƙasar nan'."
Ta ce ba ta taɓa fuskantar wata wariya ba a Birtaniya.
"Na san cewa zan je wurin da zan sha bamban da sauran mutane, saboda haka ban ji wani abu ba.
"Abin da ya fi ɗaukar hankalina shi ne yadda mutane ba su nuna min wani bambanci ba, kuma shi ne dalilin da ya sa nake kare Birtaniya duk lokacin da aka yi zargin nuna wariya."
A shekarar da ta gabata, Badenoch ta sha suka game da kalaman da ta yi cewa ta girma cikin firgici da rashin tsaro a Najeriya, da kuma cin hanci.













