'Martanin Kashim Shettima kan Kemi Badenoch ba zai sa ta sauya manufa kan Najeriya ba'

Asalin hoton, PA
Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun ce kalaman da Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi a matsayin martani ga shugabar jam'iyyar Conservative a Birtaniya Kemi Badenoch "ba za su sa ta sauya ra'ayi ba".
Da yake jawabi yayin wani taro kan cirani da gudun hijira da aka shirya a fadar shugaban Najeriya ranar Litinin ne, Shettima ya ce Kemi wadda 'yar asalin Najeriya ce na ƙasƙantar da ƙasar tata ta asali.
'Yarmajalisar Birtaniyar da ta zama shugabar Conservative a watan Nuwamba ta yi shuhura wajen sukar 'yansiyarsar Najeriya, da 'yan ciranin Afirka tun kafin a zaɓe ta a matsayin shugabar jam'iyyar ta masu ra'ayin riƙau.
Shettima ya bayyana alfahari da Kemi a matsayinta na 'yar Najeriya, kafin ya mayar da martanin yana mai cewa: "Muna alfahari da kasancewar Kemi Badenoch a matsayin shugabar jam'iyyar Conservative a Birtaniya, duk da kaskantar da kasarta ta asali da ta ke yi."
Bayan zaɓen Kemi a watan Nuwambar 2024, shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta Nidcom, Abike Dabiri-Erewa, ta ce hukumarta ta yi ta tuntuɓar Kemi amma ba ta amsa ba.
"Tana da damar bayyana ra'ayinta a kan komai, kai har ma da cire Kemi daga cikin sunanta kuma hakan ba zai rage wa Najeriya matsayinta na ƙasar bakar fata mafi girma a duniya ba," in ji mataimakin shugaban ƙasar.
Wannan ne karon farko da wani babban jami'i a Najeriya ya mayar da martani game da kalaman na Kemi.
'Abin da aka zaɓe ta ta yi kenan'

Asalin hoton, State House
Jam'iyyar Conservative ta masu ra'ayin riƙau, ita ce ke adawa yanzu a Birtaniya bayan Labour ta doke ta a zaɓen da aka yi a watan Yulin 2024.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga cikin manyan manufofinta akwai ƙyamar baƙi da ke shiga ƙasar daga sassan duniya, waɗanda cikinsu akwai 'yan Najeriya da ƙasashen Afirka da dama.
An haifi Kemi a birnin Landan a shekarun 1980 kafin daga baya ta koma Legas, inda ta yi yarintarta. Ta koma Birtaniya daga baya inda ta zauna tare da ƙawar mahaifiyarta.
Naziru Mika'ilu tsohon babban editan jaridar Daily Trust ne a Najeriya kuma ɗalibi mai karatun digiri na uku a Birtaniya. Ya ce abin da Kemi ke yi na cikin aƙidun jam'iyyarta.
"Babu mamaki yanzu kalaman da mataimakin shugaban ƙasa ya yi su sa ɗan sassauta musamman kan abin da ya shafi Najeriya, saboda su ma 'yan jam'iyyarta ba za su so su alaƙanta kansu da abubuwan da take faɗa ba," a cewarsa.
"Amma dai matsayinta a kan baƙin haure da wasu abubuwa da suka shafi harkokin cikin gida ba za su sauya ba, saboda shi ne matsayin 'yan jam'iyyarta, waɗanda akasarinsu fararen fata ne masu ra'ayin riƙau.
"Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa masu goyon bayan jam'iyyarta suka zaɓe ta shi ne alƙwarin da ta yi na dawo da farin jininta, da kuma mayar da ita kan mulki. Saboda haka za ta ci gaba da yaɗa waɗannan manufofi."










