Yadda ‘tarkon soyayya’ ke jefa mutane cikin ƙuncin rayuwa a Indiya

    • Marubuci, Shruti Menon
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify, Delhi

Wata fahimta mai cike da rudani da kungiyoyin addinin Hindu suke kira da ‘Jihadin soyayya’-wanda ake cewa maza Musulmi suna jan hankalin matan addinin Hindu da soyayya wajen Musuluntar da su-ya dade yana yawo a tsakanin mutanen Indiya na tsawon shekaru, duk da cewa babu wata takamaimiyar hujja.

Yanzu kuma akasin hakan aka samu, inda ake cewa mazan addinin Hindu suna jan hankalin matan Musulmi ne a wata al'ada da ake kira “Bhagwa Love Trap” ne yake tashe a kafafen sada zumunta, wanda shi ma babu wata takamaimiyar hujja, amma duk da hakan, bai hana shi fara neman jawo rikici da sabani ba.

“Lamarin akwai ban mamaki. Da farko ban yarda abin da idona ya gani ba,” inji Maryam, wata Musulma ’yar Arewacin Indiya a lokacin da take bayyana irin cin mutuncin da ta fuskanta a intanet.

Maryam-ba asalin sunanta ba ne-ta sha fama da batanci, inda aka bayyana wasu muhimman bayanai a game da ita a kafafe sadarwa. Aka yada hotunanta tare da wani mutum mai bin addinin Hindu a tsaye, inda aka rika amfani da shi ana zarginta da soyayya da wanda ba addininsu daya ba-wanda ba karamin abin kyama ba ne ga masu caccakarta din a kafofin sadarwa.

Lamarin ba gaskiya ba ne

Mazan da suke cikin hoton abokanta ne kawai, ba na soyayya ba, amma duk da hakan, wannan bai hana masu zarginta su cigaba da sukarta ba, “sun ce wai ina kwanciya da maza masu bin addinin Hindu. Sun rika cin mutuncin iyayena, tare da sukar tarbiyar da na samu,”inji ta.

Har yanzu soyayya tsakanin addinai mabanbanta abar kyama ce a gidajen Indiya masu ra’ayin rikau.

Bisa la’akari da sunayen shafukan da suke yada ta, Maryam ta yi amannar cewa maza Musulmi ne suke yada zargin na cewa ta fada cikin tarkon kauna na "Bhagwa Love Trap".

"Bhagwa" na nufin kalar saffron, wadda kala ce da ake alakantawa da ra’ayin Hindutva, wanda ra’ayi ne-a wajen masu sukarsa-da ke fafutikar addinin Hindu zalla. A nan, Bhagwa daidai yake da Hindutva.

“Tarkon kaunar Bhagwa” na nufin mazan da suka aminta da ra’ayin addinin Hindu zalla suna jan hankalin mata Musulmi, suna janye su daga cikin al’ummarsu. Musulmi ne kan gaba wajen yada lamarin, musamman masu fargabar lallai ana yin haka.

BBC ta samu zantawa da wasu masu shafuka a kafofin sadarwa da suke yada irin wannan fahimtar, sannan ta auna wasu daga cikin misalan da suka gabatar mata. Sai dai ba mu gano wata hujjar cewa akwai wata makarkashiya ba. Amma ana cigaba da yada fahimtar a kafafen sadarwa-daga watan Maris zuwa yanzu kadai akalla an yi amfani da jalmar sau 20,000.

Fahimtar na neman jawo rikici a zahiri

A watan Mayu, wani faifan bidiyo da aka nada a Madhya Pradesh da aka daura a intanet. A ciki akwai wasu daliban aikin jinya guda biyu, Musulma da wani mai bin addinin Hindu suna dawo daga makaranta a kan babur kirar scoota.

An nuna a ciki inda wasu, wadanda ake kyautata zaton maza Musulmi ne sun zagaye su, suka tsare matar suna sukarta da cewa tana jawo wa addinin abin kunya. “Ba za mu bari ki jawo wa Musulunci kaskanci ba,”inji daya daga cikin matasan, sannan wasu suka ci zarafin dan Hindun.

BBC ta ga sama da faye-fayen bidiyo 15 da suke nuna irin hakan a Indiya. Bidiyoyin da suke nuna irin wannan zargin da suka nuna irin wadannan rikicin da wasu daban, an kale su sau sama da miliyan 10 a YouTube da Instagram da X, inda yake samun rakiyar #BhagwaLoveTrap.

Wannan fahimtar, kusan martani ce a kan tsohuwa kuma wadda ta fi tashe wato “Jihadin soyayya”, wadda ke da ma’ana da ta yi hannun riga da ya yanzu, inda ake cewa mazan Musulmi suna jan hankalin matan Hindu, sannan mutanen Hindu sun dade suna yadawa a kafafen sadarwa na tsawon shekaru.

Kamar “Tarkon kaunar Bhagwa”, wadannan zarge-zargen ana yada su ne ba tare da wata hujja ba, sannan sun jawo sabani sosai a zahiri.

Akwai karancin auratayya a tsakanin addinai daban-daban a Indiya, inda da yawan mutane suka gwammace shirya auren kwantiragi.

Haka kuma wasu binciken da wasu kafafen yada labarai guda biyu na Indiya sun gaza kawo hujjoji gamsassu a game da fahimtar.

Duk da rashin hujjojin, batun na “Jihadin soyayya” ya zama ruwan dare a siyasar Indiya. Fitattun ‘yan siyasa daga jam’iyyar Firayi ministan Narenda Modi, BJP da wasu mambobinta da suke da irin ra’ayin suna yawan tattauna batun.

An fi yayata batun na “Tarkon kaunar Bhagwa”a kafofin sadarwa, a lokuta da dama ta hanyar amfani da wasu shafukan da ba a iya tantance su ba, amma wasu daga cikin manyan jagororin Musulmi na kasar sun taimaka wajen rura wutar fahimtar.

Shoaib Jamai,wani babban malamin addinin Musulunci ne da yake yawan tattauna batutuwa a kafafen yada labaran Indiya wanda ya bayyana kan shi a matsayin daya daga cikin masu kyamar al’adar a kafafen yada labaran kasar, amma ya ce bai aminta da rikicin da lamarin ke neman jawowa a duniya ba.

“Ba na goyon bayan Musulmi masu daukar doka a hannunsu. Wannan kasa ce da akwai doka,” inji shi.

Amma a game da gaskiyar al’adar, Malam Jamai ya ce lallai ana yi, inda ya ce matasan addinin Hindu, “suna ruduwa” da “fahimtar addinin Hindu zalla,” inji shi, “domin jawo hankalin mata Musulmi zuwa gare su.”

Malam Jamai da wasu fitattun masu yada batun suna kafa hujja ne da wasu faye-fayen bidiyo da aka yada a kafafen sadarwa da suke nuna jagororin fafutikar addinin Hindu zalla suna karfafa gwiwar mazan Hindu da su rika bin matan Musulmi-kamar yadda fahimtar “Tarkon kaunar Bhagwa” take nuna wa.

Daya daga cikin su ya nuna Yogi Adityanath, wanda daya ne daga cikin jagorin Jam’iyyar BJP yana bayani a wajen wani yakin neman zabe a shekarar 2007 cewa. “Idan Musulmi ya dauke mana mace guda daya,” inji shi, “za mu dauki mata Musulmi guda 100,” inji shi, sannan taron mutanen suka tafa masa.

Mista Adityanath yanzu haka ya zama babban majistare a yankin Uttar Pradesh. BBC ta tambaye shi ko har yanzu yana da irin wannan ra’ayin, amma bai ba da amsa ba.

Mun duba wasu misalai guda 10 da Malam Jamai da wasu masu fahimtar ana al’adar “Tarkon kaunar Bhagwa” suka ba mu a kokarinsu na gamsar da mu.

Masu amannar ra’ayin suna cewa mazan Hindu suna kulla alakar soyayya ko aure da mata Musulmi da gangan ne domin su juya musu tunani ko su cutar da su saboda addininsu.

Duk da cewa dukkan misalan da aka kawo mana sun nuna soyayya tsakanin mazan Hindu da mata Musulmi, a biyu daga ciki, matan ba su canja addinsu ba.

A guda shida daga ciki kuma da aka ce mazan Hindun sun kashe matan saboda bambancin addini, hudu daga ciki rikicinsu ya samo asali ne daga rikicin ma’aurata da talauci, inda ya yi sanadiyar kisa kamar yadda ’yan sanda suka bayyana.

Sauran guda hudun kuma babu tabbaci a kansu daga labarai ko bayanan ’yan sanda, amma babu wata alama ko hujjar cewa tarkon kaunar Bhagwa na da alaka da su.

Haka kuma akwai wasu faye-fayen bidiyo da suke kara karfafa fahimtar wadanda kafar bin diddigin Indiya, Boom Live ta bibiya tare da karyatawa.

Kungiyoyi ra’ayin Hindu zalla sun karyata samuwar tarkon kaunar

“Babu wata hujja cewa mazan Hindu suna wannan al’adar,” inji Alok Kumar, shugaban Visha Hindu Parishad, wadda kungiya ce ta ra’ayin Hindu zalla, sannan ya kara da cewa hujjar da malam Jamai yake bayyanawa, “ba su da karfi,” inji shi.

Sai dai kuma Mista Kumar ya yarda cewa “jihadin soyayya” gaskiya ne. “Akwai maza Musulmi da dama da suke jan hankali matan Hindu zuwa gare su,” inji shi.

“Ana amfani da jihadin soyayya a siyasa sosaj,” inji Fatima Khan, daya daga cikin ‘yan jaridar farko-farko da suka fara rubutu a game da “Tarkon kaunar Bhagwa” a lokacin da take bayyana irin goyon bayan da al’adar ke samu daga babbar jam’iyyar Indiya mai mulki.

“A daya bangaren kuma, Tarkon kaunar Bhagwa wata sabuwar al’ada ce. Ba ta da goyon bayan ’yan siyasa.”

Kamar sauran muhawarori da ake tafkawa a kasar, wannan ma akwai siyasa a ciki-amma a fili yake-cewa bambancin addini a Indiya suna taimakawa wajen irin wadannan matsalolin su rika samun gindin zama a kafafen sadarwa, sannan suke neman zama rikici a duniya.

Maryam, wadda aka yada ta wannan hanyar abar misali ce a wannan tsarin. Ta shiga matukar damuwa da sakonnin da ake aiko mata da dole sai da ta karbi hutu a wajen aiki domin guje wa fada wa cikin harin makiya.

“Lokacin ne karon farko da na shiga fargabar rayuwata. Na kasance cikin tsoro da fargabar fita waje,” inji ta. “Kun ce kuna kare mutuncin mata ne ta hanyar bata rayuwarsu.”