'Yan sanda na riƙe da waɗanda ake zargi da wawure kuɗi a gidan gwamnatin Katsina

Asalin hoton, Katsina State Government
Jami'an tsaro a Jihar Katsina na tsare da wasu ma'aikatan gwamnatin jihar da ake zargi da sace maƙudan kuɗi a gidan gwamnati.
Shugaban sashen hulɗa da jama'a na Gwamnatin Katsina, Al-Amin Isah, ya tabbatar da cewa kusan mako biyu ke nan da faruwar lamarin, ba kamar yadda wasu kafofin yaɗa labarai suke ruwaito ba.
Da yake tabbatar wa BBC Hausa faruwar lamarin, Al-Amin bai bayyana adadin kuɗin ba, yana mai cewa waɗanda abin ya shafa za su yi ƙarin bayani.
Zuwa yanzu an saki wasu daga cikin ma'aikatan sashen kuɗi da masu gadi da aka kama yayin da ake ci gaba da riƙe wasu, waɗanda hukumomi ba su bayyana adadinsu ba.
Kiran da muka yi wa kakakin rundunar 'yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, bai amsa ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Wasu rahotanni da BBC Hausa ba ta tabbatar ba na cewa adadin kuɗin ya kai naira miliyan 31.
"E, gaskiya ne an saci kuɗi kamar yadda kuka tambaya. Tuni muka sanar da jami'an tsaro kuma sun fara gudanar da bincike," a cewarsa. "Sai dai ba zan faɗa muku takamaiman adadin kuɗin ba."
Kakakin gwamnatin ya ce tsabar kuɗi ne da gwamnati ta ajiye don gudanar da ayyuka "kamar aiken direbobi da sallamar ƙananan ma'aikata waɗanda ba zai yiwu a yi su ta banki ba".
Ba wannan ne karo na farko ba
Al-Amin Isah ya tabbatar da cewa irin wannan ta taɓa faruwa a baya amma an gano waɗanda suka aikata hakan kuma an karɓo kuɗin.
"Ko a lokacin da irin wannan ta faru a shekarar da ta wuce jami'an tsaro sun yi bincike kuma an gano waɗanda suka aikata har ma an ƙwato kuɗin."
A wancen loƙacin, rahotanni sun ce wasu mutane ne suka kutsa ofishin tsohon sakataren gwamnati, Mustapha Inuwa, tare da sace naira miliyan 16.











