'Har yanzu hankalinmu bai kwanta ba bayan gudun hijira na kwana 200'

Wani kango
Bayanan hoto, Mutanen garin sun tarar da kangwaye bayan shafe watanni ashiri suna gudun hijira

Al’ummar garin Shimfida da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina na kokawa da halin da suka samu garinsu bayan gwamnati ta mayar da su daga zaman gudun hijira da suka yi a sakamakon matsalar tsaro.

Al’ummar garin gaba daya sun watse inda suka yi gudun hijira a sakamakon hare-haren barayin daji masu garkuwa da kuma kisan mutane.

Sama da dubu goma sha biyu ne suka yi gudun hijira a garin Jibia yayin da wasu sama da dubu hudu kuma suka ketara zuwa Jamhuriyar Nijar, inda har yanzu bayanai suka nuna suna can.

Bayan da wadanda suke zaman gudun hijirar ne a garin Jibia su sama da dubu goma sha biyu suka koma garin nasu a ranar Litinin ne sai suka iske cewa bisa ga dukkan alamu ba a gyara musu muhallin nasu ba yadda ya kamata.

Daman jama’ar wadda ta kunshi mata da maza da yara kanana sun koma ne bisa karfin hali da jajircewa ganin cewa sun shafe sama da shekara daya a garin na Jibia.

Daya daga cikin magidan da suka koma Ibrahim Roddi ya sheda wa BBC cewa yadda suka samu garin nasu al’amarin ya sanyaya musu gwiwa.

Wani gida

Ya ce gwamnati ta sake musu rufin gidajen da suka kwaye amma kuma sun tarar ba a sa kyaure ba, wanda hakan zai shafi jin dadin zamansu a gidajen da kuma fargaba.

Haka makarantun garin da asibitin duka ba wanda aka gyara suna kware ba rufi, wanda hakan ke nuna cewa hukumomi kamar sun yi gaggawar mayar da ‘yan gudun hijirar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka kuma ya ce hukuma ba ta samar musu da katifu da sauran abubuwa da za su iya zama cikin kwanciyar hankali da jin dadi ba a gidajen.

A fannin abinci ma, bayanai sun nuna gwamnati ta samar wa wannan tarin jama’a kusan dubu goma sha biyu buhun shinkafa dubu biyu ne kawai mai nauyin kilogirma 10.

Kodayake wasu bayanai na cewa wai shugaban karamar hukumar ya ce za a kai musu kari, wanda har lokacin hada wannan labari ba a kai musu ba.

Duk da cewa gwamnati ta girke sojoji a garin, to amma mutanen sun ce har yanzu suna cikin fargaba ganin yawan jami’na tsaron bai isa su samu kwanciyar hankali yadda ya kamata ba.

Suna cewa ya kamata a kara yawansu saboda wannan yanki nasu wuri ne da ke fama da wannan matsala ta barayin daji.

Haka kuma al’ummar garin na Shimfida na kokawa da rashin hanya a yankin nasu baya ga wadannan matsalaoli na tsaro da ke addabar yankuna da dama n jihar ta Katsina da ma wasu jihohin musamman na arewa maso yamma a kasar ta Najeriya.

Martanin gwamnati

Dangane da wadannan matsaloli da mutanen garin na Shimfida suke nunawa, hukumomin jihar ta Katsina sun ce daman na mayar da mutanen gida ne kafin a san irin sauran abubuwan da ya kamata a sama musu ta yadda rayuwarsu za ta koma kamar da cikin walwala, kamar yadda mai bai wa gwamnan jihar shawar kan harakar tsaro Ibrahim Ahmed Katsina ya sheda wa BBC.

Jami’in ya ce komawar tasu ma ta tabbata ne bisa abin da ya kira kokarin gwamnati na hada kai tsakaninta da kananan hukumomi da jami’an tsaro da masarautu da kuma ita al’umma.