Yadda za a fafata a zagaye na biyu na gasar Euro 2024

A ranar Asabar za a ci gaba da zagaye na biyu na sili ɗaya ƙwala bayan kammala wasannin cikin rukuni a gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024 a ranar Laraba.

Tawagogi biyu na saman kowane rukuni ne suka wuce zuwa zagaye na biyun, sai kuma huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na uku.

Ga yadda teburin rukunnan suka kasance da kuma waɗanda suka tsallake.

Jadawalin wasannin zagaye na biyu

Asabar, 29 ga watan Yuni

  • Switzerland v Italy - (5:00)
  • Germany v Denmark - (8:00)

Lahadi, 30 ga watan Yuni

  • England v Slovakia - (5:00)
  • Spain v Georgia - (8:00 )

Litinin, 1 ga watan Yuli

  • France v Belgium - (5:00)
  • Portugal v Slovenia - (8:00)

Talata, 2 ga watan Yuli

  • Romania v Netherlands - (5:00)
  • Austria v Turkey - (8:00)

Rukunin A - Germany da Switzerland sun tsallake

Scotland ce ta ƙare a ƙasan rukunin da maki ɗaya bayan Hungary ta doke ta a wasan ƙarshe na rukunin. Duka su biyun sun koma gida.

Jamus ce ta jagoranci rukunin yayin da Switzerland ta biye mata a mataki na biyu.

Rukunin B - Spain da Italy ne suke wuce

Sifaniya da Italiya ne suka tsallake daga wannan rukuni.

Sifaniya ce kaɗai tawagar da ta ci wasanninta uku kuma ba a zira mata ƙwallo ba.

Sai kuma Croatia da Albania da suka koma gida.

Rukunin C - England da Slovenia da Denmark

Ingila ta tsallake ne bayan ta kammala a saman teburin rukunin duk da buga canjaras har biyu tsakaninta da Slovenia (0-0) da Denmark (1-1).

Sai dai kuma Serbia ce kawai ta koma gida daga wannan rukuni, yayin da Ingila da Denmark da Slovenia suka tsallake.

Ingila ce ta ɗaya, Denmark ta biyu, sai kuma Slovenia da ta tsallake a matsayin 'yar alfarma.

Rukunin D - Austria, France, Netherlands

A wannan rukunin ma, tawaga uku ce ta tsallaka zuwa zagayen 'yan 16.

Austria ce ta ɗaya, Faransa ta biyu, sai kuma Netherlands da ta tsallake a matsayin ɗaya daga cikin tawagogi huɗu da suka gama a matsayi na uku amma kuma sun yi ƙoƙari.

Poland ce kaɗai ta koma gida daga rukunin.

Rukunin E - Nan ma uku ne suka tsallake

Duka ƙungiyoyin wannan rukuni sun kammala ne da maki hurhuɗu, yawan ƙwallaye ne kawai ya bambanta su, kuma karon farko kenan da hakan ta faru a tarihin gasar.

Romania ta kammala a saman teburin, Belgium ta rufa mata baya, sai kuma Slovakia da ta wuce a matsayin 'yar alfarma.

Rukunin F - Portugal, Turkiye, Georgia

Portugal ce ta ɗaya a rukunin, Turkiyya ta take mata baya, Georgia kuma ta uku.

Haka suka ɗunguma duka ukun zuwa zagaye na gaba, amma Georgia ta wuce ne a matsayin haziƙa amma kuma ta ƙare a mataki na uku.

Su wa aka yi wa alfarma?

  • Netherlands daga Rukunin D
  • Georgia daga Rukunin F
  • Slovakia daga Rukunin E
  • Slovenia daga Rukunin C

Ƙasashen da suka koma gida

Rukunin A

  • Hungary
  • Scotland

Rukunin B

  • Croatia
  • Albania

Rukunin C

  • Serbia

Rukunin D

  • Poland

Rukunin E

  • Ukraine

Rukunin F

  • Czech Republic