Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rwanda na alhinin shekara 30 da kisan kiyashin ƙasar
Rwanda ta fara alhinin cika shekara talatin da kisan kiyashin da ‘yan Hutu masu tsattsauran ra’ayi suka yi wa ‘yan kabilar Tutsi marassa rinjaye da ‘yan Hutu masu sassaucin ra’ayi, wanda a lokacin aka kashe mutum kusan miliyan daya a cikin kwana dari .
A ranar Lahadin nan za a gudanar da taruka a kasar ta gabashin Afirka da sauran sassan duniya domin tunawa da wadanda aka kashe tare da nuna goyon baya ga wadanda suka tsira daga kisan.
Shugaba Paul Kagame zai jagoranci taron inda zai kunna wata wuta ta tunawar a babban birnin kasar Kigali, da ajiye furanni a kan manyan kaburbura, tare da shugabannin kasashen duniya da za su halarta.
Za a fara taron na alhini wanda aka yi wa lakabi da Kwibuka, da ke nufin tunawa, inda za a yi shi cikin jimami da nuna bakin cikin, ba tare da wasu kade-kade ko raye-raye ba na nishadi a fadin kasar ta Rwanda.
Hatta a tasoshin talabijin da rediyo za a dakatar da sanya kade-kade da harkokin wasanni da fina-finai a tsawon mako daya da za a yi na alhini.
Gidajen shan barasa da raye-raye za su kasance a rufe, sannan za a yi kasa-kasa da tutar kasar.
A karon farko ana sa ran Faransa za ta fito fili ta amsa cewa ita da kawayenta da sun hana wannan kisa, amma a lokacin ba ta da niyyar yin hakan.
Ana ganin kasar ta Rwanda ta yi kokari matuka gaya wajen farfadowa daga wannan matsala da kyama da wariya.
To amma ana alakanta burbushin wannan matsala kan korafe-korafen da ba a shawo kansu da magance ba shi ke janyo kisan gilla da danniya da damuwa da rikice-rikice a makwabciya Kongo.
Abin da ya haddasa kisan
Kusan kashi tamanin da biyar na al’ummar Rwanda ‘yan Hutu ne to amma ‘yan Tutsi marassa rinjaye sun mamaye tare da kankane al’amuran kasar.
A shekara ta 1959 sai ‘yan Hutu suka kifar da gwamnatin mulukiya ta ‘yan Tutsi, kuma dubban ‘yan Tutsi suka gudu daga kasar zuwa makwabta ciki har da Uganda.
Daga nan ne kuma sai wasu ‘yan Tutsi da suka yi gudun hijira suka kafa wata kungiya ta tawaye – Rwandan Patrirotic Front (RPF), wadda ta mamayi Rwandan a 1990, ta tayar da kayar baya, aka tika fada har zuwa 1993 lokacin da aka yi sulhu.
To amma a daren 6 ga watan Afirilu na 1994 aka harbo wani jirgin sama da ke dauke da shugaban kasar a wancan lokacin Juvenal Habyarimana da takwaransa na Burundi Cyprien Ntaryamira, wadanda dukkaninsu ‘yan Hutu ne – dukkan mutanen da ke cikin jirgin suka mutu.
Masu tsattsauran ra'ayi 'yan Hutu sun dora alhakin harin a kan kungiyar RPF, kuma tun daga nan suka fara shirin aikata kisan kiyashin.
RPF ta ce 'yan Hutu ne suka harbo jirgin domin fakewa da hakan su aika kisan kiyashin.
Wannan lamari shi ya taso da wannan kisa na kiyashi da aka yi wa ‘yan Tutsi da Hutu masu sausaucin ra’ayi.
Makwabtka sun kashe makwabtansu, hatta wasu mazajen ma sun hallaka matansu ‘yan Tutsi, saboda ana yi musu barazanar kisa idan har ba su kashe matan nasu ba.
A lokacin hatta katin sheda na mutum na dauke da irin kabilarsa, daga nan ‘yan bindiga suka yi shingayen bincike inda aka rika tare ‘yan Tutsi ana yi musu kisan gilla da adda.
An dauki dubban mata ‘yan Tutsi aka mayar da su kwar-kwara.
A lokacin majalisar Dinkin Duniya da Belgium suna da sojoji a kasar ta Rwanda, amma ba a ba wa rundunar damar hana kisan ba.
Kungiyar RPF, tare da goyon bayan sojojin Uganda, ta kame karin yankuna sannu a hankali, har zuwa ranar 4 ga watan Yuli na 1994, lokacin da mayakanta suka shiga babban birnin, Kigali.
'Yan Hutu miliyan biyu wadanda suka hada da farar hula da wadanda suka aikata kisan kiyashin suka gudu, inda suka tsallaka zuwa Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo a lokacin ana kiranta Zaire, saboda tsohon ramuwar gayya.
Wasu kuma suka gudu zuwa makwabtan kasashe -Tanzania da Burundi.
Kungiyoyin kare hakkin dan'Adam sun ce mayakan RPF sun kashe dubban 'yan Hutu fararen hula lokacin da suka kwace mulki. Suka kuma kashe karin wasu 'yan Hutun bayan da suka shiga Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo don farauto su. To amma kungiyar ta musanta wannan zargi.
An samu jumullar mutum 93 da laifi bayan shari'a mai tsawo, kuma an samu gomman jami'an tsohuwar gwamnati da laifin kisan kiyashi wadanda dukkanninsu 'yan Hutu ne.
Hatta malaman coci da mata masu yi wa coci hidima an same su da laifin kisan mutane, wadanda suka hada da masu neman mafaka a coci.
A cikin kasar ta Rwanda an kafa kotuna na al'umma da ake kira Gacaca, domin hanzarta shari'ar dubban wadanda ake zargi da laifin kisan.
Rahotanni sun ce kusan mutum dubu 10 sun mutu a gidan yari yayin da ske jiran shari'a.
An yaba wa Shugaba Paul Kagame, kan yadda ya farfado da 'yar karamar kasar.