Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ana rusa wuraren haƙo abubuwan tarihi domin sace su a Afghanistan’
- Marubuci, Kawoon Khamoosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Ana rushe gwamman wuraren da ake haƙo abubuwa masu daɗaɗɗen tarihi domin yin sata a Afghanistan, a cewar masu bincike na jami’ar Chicago ta Amurka.
Inda suka ce nazarin hotunan tauraron ɗan adam ya tabbatar da samun hujjoji na farko ƙwarara na hotunan yadda aka dinga yin satar tun a zamanin gwamnatin da ta shuɗe, kuma aka ci-gaba bayan Taliban ta karɓe mulki a shekarar 2021 a ƙasar.
Wurare masu tsohon tarihin tun zamanin kaka-da-kakanni zuwa lokacin da ake amfani da tagulla da lokacin da aka fara amfani da karfe, zuwa shekaru 1000 kafin haihuwar Annabi Isa (AS) na daga cikin wuraren da masu binciken suka ce an lalata.
Mafiya yawa daga wuraren da suka gano suna arewacin Afghanistan ne a yankin Balkh, wanda fiye da shekaru 2000 da suka wuce ya kasance cibiyar Bactria.
Yankin ya kasance mafi arziki kuma mafi suna a cikin duka yankunan ƙasar ta Afghanistan a zamanin daular Achaemenid, a cikin ƙarni na 6 kafin haihuwar Annabi Isa.
A shekarar 327 kafin haihuwar Annabi Isa ne, sarki Alexander ya ci yankin da yaƙi kuma ya auri wata ƴar asalin yankin mai suna, Roxana bayan ya yi nasara a kan shugaban daular Achaemenid.
Wurin na kan babbar hanyar Silk wadda ke gabas-maso-yammacin babban birnin yankin Bactra – wanda daga baya ake kira Balkh –yankin da ya kasance cibiya na koyar da addinin Zoroaster da kuma na Bhuda.
Sai dai daga baya ya koma wani muhimmin birnin Musulunci.
Masu binciken a cibiyar da ke kula da adana muhimman kayan tarihi da ke jami’ar Chicago sun gano wuraren haƙo kayayyakin tarihi 29,000 a fadin ƙasar ta Afghanistan da taimakon hotunan tauraron ɗan Adam da wasu abubuwa.
Sai dai daga shekarar 2018 zuwa shekarun da suka biyo shi, sun fara lura da wani abun da ke faruwa daki-daki a yankin na Balkh.
Sun ce sun fara ganin wasu abubuwan da suka yi amanna cewa motocin rusau ne a cikin hotunan saboda yadda suke zuwa kuma suke ɓacewa lokaci-lokaci da kuma shatin hanyar da suke bari.
Sai kuma hotuna na gaba su nuna wurin a rushe da ramukan da masu satar suka haƙa, kamar yadda farfesa Gil Stein, daraktan cibiyar ya bayyana.
“Abun da ke faruwa shi ne mutane na rushe wani babban wuri domin bayar da damar yin satar sannu-a-hankali, in ji shi.
Tawagar masu binciken ta ce an lalata wuraren tarihi 162, inda aka lalata guda ɗaya a kowane mako daga shekarar 2018 zuwa 2021.
Sannan an ci-gaba da lalata wasu wurare 37 a karkashin mulkin Taliban.
Masu binciken sun ce ba za su faɗi daidai inda hakan ke faruwa ba, saboda kaucewa bayar da bayanai ga wasu masu niyar sata.
Ana matakan farko na tattara bayanai kan wuraren da abun ya shafa.
Kuma abun da hakan ke nufi shi ne, masu binciken ba su san ainihin me ke binne a wadannan wuraren ba, waɗanda suka hada da tuddan ƙasa da ganuwa da wuraren da matafiya ke yada zango su huta a gefen hanyoyi da kuma hanyoyin ruwan da aka tsattsara.
Sai dai mil 60 daga nan ne, Tela Tepe, inda a shekarar 1978 aka gano tulin zinaren Bactra da ya kai shekara 2000.
"Dutsen zinare" ya ƙunshi abubuwan zinaren da ba kasafai ake samun irinsu ba har 20,000, waɗanda suka haɗa da kayan ƙawa na zinare da kambin zinare da sulallan zinare waɗanda aka yi wa laƙabi da dukiyar Afghanistan da ta ɓata.
"Za ka iya tono hawa-hawa na zamani daban-daban a cikin kowanne tudun ƙasa," a cewar Said Reza Huseini, wani mai bincike a jami'ar Cambridge.
An haife shi a Balkh, kuma lokacin da ya wuce shekara 20 ya dinga taimakawa a matsayin ɗan sa-kai ga masu binciken wuraren haƙo abubuwan tarihi a arewacin Afghanistan, ciki har da wasu wuraren da masu binciken suka ce an rusa. Ya kaɗu matuƙa da ya ga hotunan jami'ar ta Chicago.
"A lokacin da na ji labarin sai na ji tamkar ana zare min numfashi," in ji shi.
Babu wasu bayanai na haƙiƙa da ke nuna ko su wanene ke lalata wuraren.
Farfesa Stein ya ce yana da muhimmanci sanin cewa an fara wannan al'amarin ne tun lokacin shugaba, Ashraf Ghani kuma aka ci gaba a lokacin Taliban.
Gwamnatin Ghani tana da rauni kuma ba ta da cikakken iko a kan wasu sassan ƙasar.
Balkh da birni mafi girma a arewacin Afghanistan na Mazar-i-Sharif, na daga cikin wuraren farko da Taliban ta fara ƙwacewa kafin ta ƙwace Kabul, babban birnin ƙasar a 2021.
Farfesa Stein ya yi amanna cewa wasu masu kuɗi ko masu ƙarfin da ke iya sayen manyan kayan aikin ɗiban ƙasa ko su yi hayarsu ne ke yin sata a wuraren kuma suke ɗiban ƙasar zuwa yankunan karkara "inda babu wanda zai dame su."
Mista Huseini ya ce ana sata a wasu irin waɗannan wuraren haƙo abubuwan tarihin tun a 2009 kafin ya bar ƙasar.
"Babu wanda zai haƙo ko ya yi tono ba tare da izinin mutane masu ƙarfi a yankunan ba, ko kuma ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai," ya bayyana.
"Tarihin wurin bai dame su ba, suna haƙawa ne su lalata don ko za su gano wani abu. Na shaida hakan da idona-suna yin amfani da rariyar tankaɗen ƙasa don gano abubuwa. "
Ya ce akwai lokacin da ya taimaka aka kaiga wani wurin haƙo abubuwan tarihi da wani jagoran ƙungiyar masu ɗauke da makamai ke amfani da wurin don shuka opium.
A shekarar 2001, Taliban ta razana duniya a lokacin da ta tarwatsa gunkin addinin Bhuda da ya kai shekara 1,500 da ke jikin tsauni -, wanda shi ne gunkin Bhuda mafi girma a duniya a lokacin da suka karɓe iko da ƙasar a karon farko.
Amma bayan dawowarsu a karo na biyu sun ce za su girmama abubuwan tarihi na ƙasar.
Muƙaddashin mataimakin ministan watsa labarai da al'adu, Atiqullah Azizi, ya musanta cewa ana sata a waɗannan wurare, inda ya ƙara da cewa an sanya mutane 800 don bai wa wuraren tarihin kariya.
Ya shaida wa BBC cewa wasu ƙungiyoyi sun aika wa ma'aikatar hotunan motocin rusau da ke yawo da mutane masu ɗiban ƙasa, amma sai ya ce "mun aika da tawagogi da dama domin su duba wuraren kuma zan iya tabbatar muku da cewa ba a ƙara samun haka ba ko da kuwa a wuri daya."
Haka kuma ma'aikatar tsaro ta Taliban ta ce an kama mutane uku a watan Satumba waɗanda ake zargi sun yi yuƙurin fasaƙwaurin wasu abubuwan tarihi da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 27, da suka haɗa da gumaka da gawawwakin da aka sanyawa maganin hana ruɓewa da kambin zinare da littafi da kuma takubba.
Ma'aikatar ta ce an miƙa kayan ga gidan ajiye kayan tarihi na ƙasa kuma ana ci-gaba da bincike.
An gaya wa farfesa Stein abun da Mista Azizi ya ce.
"Ban san dalilin da ya sa mutane za su musanta ba, sai dai idan suna jin kunyar fuskantar hujjojin, " in ji Farfesan.
"Za mu iya nuna cewa an ci gaba tun lokacin wata gwamnati zuwa wata."
Farfesan ya yi amanna cewa abubuwan tarihin ana fasaƙaurinsu ne zuwa wasu ƙasashe kamar Iran, Pakistan da wasu ƙasashe, inda suke ƙarewa a nahiyar Turai da arewacin Amurka da gabas mai nisa.
Akwai kuma yiwuwar ana gwanjon wasu ba tare da an bayyana su ba, ko tsawon shekarunsu a gidajen adana kayan tarihi a faɗin duniya.
Ya kuma ce da wuya a iya gano inda suke saboda ba a ɗauki bayanansu ba tun da fari - amma yana ganin ya kamata a gwada kuma a yi ƙoƙarin kare wuraren da za a iya samun ƙarin abubuwan tarihin.
"Abubuwan tarihin Afghanistan wani ɓangaren tarihin duniya ne kuma a gaskiya abu ne da mallakarmu ne gaba daya" a cewar Farfesa Stein.