Biden na fuskantar ƙarin bijirewa a cikin gida kan yaƙin Isra'ila a Gaza

    • Marubuci, Daga Barbara Plett Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden na fuskantar ƙaruwar matsin lamba don ya tilasta wa Isra'ila ta dakatar da yaƙin da take yi da Hamas a Gaza.

Ƙaruwar alƙaluman fararen hula da ke mutuwa, da kuma tsanantar buƙatun jin kai, suna tayar da hankulan Larabawa abokan ƙawancen Amurka, sannan kuma sun janyo wata irin suka ko caccaka da ta wuce misali a cikin gwamnatinsa.

"Na ɗimauta kan tsananin (hare-haren)," a cewar Aaron David Miller, wanda ke aiki a matsayin mashawarci kan hulɗa tsakanin Larabawa da Isra'ila tsawon shekara 25 a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.

"Ban taɓa ganin wani abu, irin wannan ba."

An aika wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka ɗumbin takardun bayanan hukuma a cikin gida, ta wata kafa da aka ɓullo da ita bayan yaƙin Vietnam, wadda ke bai wa ma'aikata damar nuna ƙin amincewa da wata manufa.

Akwai kuma wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ke yawo a Hukumar raya Ƙasashe ta Amurka (USAID). Haka zalika jami'ai masu muƙaman naɗin siyasa da ma'aikata daga gomman hukumomin gwamnati, sun aika da irin wannan wasiƙa zuwa fadar White House. Ma'aikatan majalisa, su ma, sun aika da tasu wasiƙar.

Mafi yawan wannan bijirewa da ake nunawa, abu ne na sirrin mutum, sannan sa hannun da ake yi sau da yawa, ba a ambatar suna saboda damuwar da ake da ita cewa nuna adawar na iya shafar aikin mutum, don haka babu masaniya ƙarara a kan cikakken girman adawar da ake nunawa.

Sai dai, a cewar wasu bayanan da aka tsegunta, waɗanda rahotanni da dama suka ambata, ɗaruruwan mutane ne suka sa hannu kan wannan guguwa ta adawa.

Wani jami'in mulki ya faɗa wa BBC cewa damuwar ta gaske ce matuƙa, kuma akwai tattaunawa wurjanjan da ake yi game da hakan.

Mafi ƙaranci, wasiƙun na neman Shugaba Biden ya buƙaci a tsagaita wuta cikin gaggawa, kuma ya ƙara takura wa Isra'ila ta bari a kai ƙarin kayan agaji Gaza.

A wasu lokuta, furucin da ake amfani da shi, yana da ƙarfi, suna jaddada gugar zanar matasa 'yan fafutukar siyasa, kuma ga alama suna fito da, wani ɓangare na rarrabuwar kan da ake da shi tsawon lokaci, da ya fi suka ko ƙwanƙwasar Isra'ila, tare da nuna tausayin Falasɗinawa.

Wasiƙun dai suna yin tofin alla-tsine ga aika-aikar da Hamas ta aikata a harinta na bazata na ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin hallaka kimanin mutum 1,200, akasari fararen hula.

Isra'ila ta halaka fiye da mutum 12,000 a Gaza tun bayan wancan hari, a cewar alƙaluman baya-bayan nan daga ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin jagorancin Hamas. Isra'ila ta ce tana ƙoƙarin ganin ta rage yawan fararen hula da ake kashewa a Gaz, amma ba tare da yin nasara ba, inda ta ɗora alhakin haka a kan Hamas.

Wannan lamarin a Gaza wani "makwantar bacin rai" ne a gwamnati, cewar Gina Abercrombie-Winstanley, wata tsohuwar jami'ar diflomasiyyar Amurka wadda yanzu take shugabancin Majalisar tsara Manufofi kan Gabas ta Tsakiya.

Goyon bayan da gwamnatin Amurka ke nunawa kan matakin sojin Isra'ila ga dukkan alamu a wajen mutane da yawa "ya yi matuƙar nuna fifiko ga ɓangare ɗaya, a matsayin gwamnatin Amurka", in ji ta.

Misis Abercrombie-Winstanley ta sa hannu kan saƙonnin hukuma na nuna bijirewa a lokacin da take aiki, kuma ma'aikata a yanzu suna tuntuɓar ta a kan ko su ma suna iya yin hakan a yanzu.

Yadda Biden ke maida martani

Misis Abercrombie-Winstanley ta yi imani kururuwar ɓacin ran da ake nunawa ta ba da gudunmawa wajen samun gagaruman sauye-sauyen a kalaman da Amurka ke amfani da su, da kuma ƙarfafawar da take yi kan saƙonninta, tun cikin 'yan kwanaki ƙalilan bayan harin Hamas, lokacin da Shugaba Bide ya yi alƙawarin bai wa Isra'ila goyon baya babu yankewa a wani jawabi mai cike da kukan zuci.

Harzuƙa kan ruguje-ruguje a Gaza da ƙaruwar nuna fushin ƙasashen Larabawa, sun sa gugar zanar gwamnatin kan buƙatar kare fararen hula ta daɗa zama mai cike da jaddadawa. "An kashe Falasɗinawa masu matuƙar yawa" a Gaza, Mista Blinken ya ce cikin 'yan kwanakin nan.

Shi da sauran jami'ai a yanzu, suna ɗaukar batun samar da tallafin jin ƙai ba kawai a matsayin wani wajibcin ya kamata ba, har ma da muhimmancin ayyukan soji.

Wannan wani abu ne da Mista Blinken ya nunar lokacin da yake ganawa da ma'aikatan da suka fusata, a wani zaman sauraron batutuwa, cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje Matthew Miller.

Ya nunar ƙarara cewa "Amurka ce, ba wata ƙasa ba, za ta iya samu a cimma yarjejeniya don kai tallafin jin ƙai cikin Gaza" da kuma "samu a dakatar da faɗa don muradin jin ƙan ɗan'adam".

Sakataren harkokin wajen ya kwan da sanin guna-gunin da ke tasowa a ginin ma'aikatarsa, kuma ya yi nuni da ƙoƙarin shawo kan lamarin.

"Muna sauraro," ya rubuta bayan ya dawo daga tafiyarsa ta baya-bayan nan zuwa Gabas ta Tsakiya, a wani saƙon imel da BBC ta samu. "Abin da kuka gabatar shi ne faɗakarwa kan manufarmu da kuma saƙonninmu."

Amma bai canza yadda muke tunkarar muhimman manufofinmu ba, kuma babu alamun sun yi wani gagarumin tasiri a kan yaƙin da Isra'ila take yi.

Gwamnatin Biden ta ƙara zama mai fitowa fili tana bayyana ƙarin rarrabuwar kan da ta samu da Isra'ila. Mista Blinken cikin sani ya tsara ƙa'idojin tafiyar da harkokin Falasɗinawa da kuma 'yancin ƙasarsu a "washe garin ranar" a Gaza, amma gwamnatin Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi ta ƙi yarda.

Shugaban ƙasar a kai-a kai yana magana ta wayar tarho da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da manyan jami'ai don tabbatar amon ziyarce-ziyarcensa a yankin, da matsa wa Isra'ila lamba ta tabbatar da bin dokokin yaƙi.

Sai dai, babu batun gwamnatin Biden na tunanin amfani da babbar damarta, na gindaya sharuɗɗa a kan ƙasurgumin tallafin soji da take bai wa Isra'ila, wanda ta ƙara yawansa bayan harin da Hamas ta kai.

Kuma Biden ya nunar da alama a wannan mako cewa Amurka ta bai wa Isra'ila wa'adi, don ta kawo ƙarshen hare-haren sojinta a Gaza.

Za a kawo ƙarshensu lokacin da Hamas "ta rasa ƙarfin kai hari don aikata kisan kai, tozartawa da kuma yin miyagun abubuwan tashin hankali" ga Isra'ila, shugaban ya ce.

Muhimmin abu dai shi ne, Amurka da Isra'ila na da buri iri ɗaya, a cewar Miller, tsohon mai ba da shawara ga ma'aikatar harkokin waje. Dukkansu na son ruguza ƙarfin Hamas a matsayinta na ƙungiya mai ƙarfin soji, ta yadda ba za ta iya sake ƙaddamar da hari irin na 7 ga watan Oktoba ba.

Da wannan tunanin, ya ce, cikakkiyar tsagaita wuta da za ta kawo ƙarshen gaba, ba ta da wani kan gado a siyasance ko a aikace.

Kawai dai za ta jinkirta yaƙi ne, cewar Mista Miller,"saboda ba za ka taɓa samun ƙarshen wannan lamari ta hanyar tattaunawa ba".

To mene ne taƙamaimai zai tursasa wa Shugaba Biden ya canza tsari?

Abu mafi yiwuwa ba dai adawar cikin gida da yake fuskanta ba. Duk da ƙarfin da take daɗa yi, adawar a cikin gwamnatin ba ta zama wani bore ba. Jami'i ɗaya ne kawai a ma'aikatar harkokin waje a bainar jama'a ya yi murabus.

Mista Miller ya nunar hakan sai mai yiwuwa ya samu aukuwar wani lamari daga waje, kamar sakin dukkan mutanen da ake garkuwa da su ba tare da wani sharaɗi, ko kuma wani matakin sojin Isra'ila ɗaya da ya yi sanadin asarar ɗumbin Falasɗinawa.

Akwai kuma haɗurran siyasa ga Mista Biden a salon da yake amfani da shi yanzu. A goyon bayansa ga Isra'ila, yana tare da 'yan jam'iyyar Republican da kuma 'yan Demcrat masu matsakaicin ra'ayi, sai dai damuwa a tsakanin matasa kuma masu ƙarin ra'ayin sassauci a jam'iyyar Democrat tana ƙaruwa.

Tsoffin ma'aikatan yaƙin neman zaɓensa sun aika tasu wasiƙar ga shugaban ƙasa, don ya yi kiran a tsagaita wuta.

Gwen Schroeder, wadda ta yi aiki a cikin ayarin dijital ɗin Biden a lokacin zaɓen 2020, tana cikin waɗanda suka sa hannu.

Ta ce "mayar da martani ninkin-ba-ninki" da Isra'ila ke yi a Gaza ya nuna cewa rayukan Falasɗinawa "ba su kai darajar na 'yan Isra'ila ƙawayenmu ba".