Joe Biden ya soki Rasha kan harin da ya hallaka fararen hula

Shugaban Amurka Joe Biden ya jagoranci suka da Allah-wadaran da kasashen duniya ke yi kan harin makami mai linzamin da aka kai kan wata tashar jirgin kasa a gabashin Ukraine, harin da ya hallaka farar hula sama da hamsin.

Wannan na kasancewa ne yayin da jami'an kasashen yamma ke cewa Rasha ta sake tsarin shugabacin sojinta a Ukraine inda ta sanya wani janar a wanda ya jagoranci dakarun Rashar a yakin Syria, a kan shugabancin.

Shugaba Biden ya bi sahun masu zargi da sukar Rasha da kai harin, da cewa ta kai wannan mummunan hari ne na tsabagen mugunta, a lokacin da ta harba makami mai kinzami kan tashar jirgin kasan a gabashin Ukraine a lokacin da take makare da fararen hula, inda ta kashe mutane akalla hamsin.

Wadanda harin ya rutsa da su a tashar wadda a lokacin dandazon mutanen ya kai dubu hudu, yawancinsu mata ne da kananan yara da tsoffi, wadanda ke shirin tserewa daga tsammanin zuwan dakarun Rasha da ke durfafar yankin gabashin Donbas.

A wani taron manema labarai Sakatariyar Watsa Labarai ta fadar gwamnatin Amurkar, White House Jen Psaki, ta ce irin abin abin da Rasha ke tafka wa ba komai ba ne face laifukan yaki:

Ta ce, ''Abin da muka gani a cikin sati shida da y gabata, ko sama da haka, abu ne wanda shi kansa Shugaban ya bayyana a matsayin laifukan yaki, wanda shi ne kai hari kan farar hula da niyya.

Wannan karin tsabagen mugunta ce me tayar da hankali, da Rashawa suka aikata, kai farmaki kan fararen hula da ke neman gudu su tsira.''

''Inda muke a yanzu shi ne mu taimaka wa kokarin gudanar da bincike kan wannan hari a yayin da muke tattara bayanai kan abubuwan da Rasha ta yi, mu bincike su da laifin. Za mu ci gaba da bayar da karin taimako da bayar da makamai domin taimaka wa Ukraine kare kasarsu.''

Yayin da ake wannan, ita kuwa Rasha ta musanta alhakin kai harin, inda a wata sanarwa kakakin ma'aikatar tsaron kasar, Igor Konashenkov, ya ma dora laifin a kan sojin Ukraine.

Ya ce, ''Sojojin Ukraine ne suka kai hari kan tashar jirgin kasan a Kramatorsk da makami mai linzami sanfurin Tochka-U. Tarkacen makami mai linzami na Tochka-U, da aka samu a kusa da tashar jirgin kasan ta Kramatorsk sun tabbatar da haka, domin dakarun Ukraine ne kadai suke amfani da irin makamin.''

Babban jami'in harkokin wajen Tarayyar Turai Josep Borrell, wanda ya je Ukraine din ya gaya wa BBC cewa harin wani yunkuri ne Rasha na ganin ta karya wa Ukraine kwarin guiwa, bayan da sojin Rashar suka g cewa sun kasa samun nasara ta hanyar yakar sojin Ukraine.

Firaministan Ukraine Denys Shmyhal, shi kuwa ya bayyana Rasha a matsayin kasa 'yar ta'adda, yayin da shi kuwa Shugaba Zelensky, ya zargi Moscow da ta'annati kan fararen hular Ukraine a fakaice.

A wani taron manema labarai a hedikwatar Majalisar dinkin Duniya, mai magana da yawun majalisar, Stephane Dujarric, ta yi Allah-wadai da harin

Ta ce, ''Harin da aka kai tashar jirgin kasa ta Kramatorsk a gabashin Ukraine yau (Juma'a), wanda ya kashe tare da jikkata fararen hula wadanda suke jira a kwashe su, da dama, da suka hada da mata da yawa da yara da tsofaffi, hadi da sauran hare-hare a kan farar hula da kayayyakin more rayuwa na farar hula, gaba daya ba za a yarda da su ba.''

Tsabagen saba wa dokoki ne na duniya da kuma 'yancin dan-Adam na duniya, wadanda dole ne a hukunta wadanda suka aikata." in ji ta.