Wane ne Masood Azhar, mutumin da ke shirin jefa Indiya da Pakistan cikin yaƙi?

Masood Azhar na jawabi a abun magana yayin da ya ke zaune a akan kujera a Islamabad, Pakistan August 2001. Yana sanye da tabarau da bakin gemu da saje. Ya rufe kansa d farin hirami, yana sanye da riga Taguwa. A kusa da shi wani mutum ne zaune da baƙin gemu da farar taguwa da fararhula. sai sauran mutane da ke zaune a bayansu.

Asalin hoton, SAEED KHAN/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Masood Azhar na cikin wadan majalisar ɗinkin duniya ta bayan a matsayin ƴan ta'ada a duniya
    • Marubuci, BBC Urdu
  • Lokacin karatu: Minti 5

A farkon makon nan, Indiya ta ƙaddamar da wani harin makami mai linzami a wurare 9 da ke cikin ƙasar Pakistan, a matsayin martani kan wani mummunan hari kan masu yawan buɗe ido a yankin Kashmir, makonni biyu da suka gabata, wanda da ya yi sanadiyyar mutum 26.

Ta ce wadannan wurare "matattara ce ta ƴan ta'adda" kuma ta kai hari kan masallacin Subhanallah da ke Bahawalpur, da ke gabashin Pakistan, da hukumomin Indiya suka bayyana a matsayin cibiyoyin "ƙyanƙyasa sojoji masu aƙidar ƴan ta'adda" da mayaƙan sa kai na Jaish-e-Mohammed (Jem).

Wacce ce ƙungiyar da aka haramta, kuma wane ne shugabanta Masood Azhar, da aka bayyana shi a matsayin ɗan ta'adda da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta yi - sannan harin da aka kai ya halaka ƴan'uwansa masu yawa?

Waye Masood Azhar?

An fi sanin Masood Azhar a duniya a matsayin mai ra'ayin riƙau da ke da ƙarfin faɗa a ji a tsakanin Musulman duniya, da su yi kisa, da sauran ayyukan ta'addanci da sunan jihadi.

An haife shi a shekarar 1968, ya kuma fito cikin iyalai masu riƙo da addini, a birnin Bahawalpur. Mahaifinsa ya yi aiki a bangaren likitanci da kuma falsafa.

Bayan makarantar Firamare, ya ci gaba da karatu a jami'ar Uloom-ul-Islamiya, wata jami'ar Islama da ke Banoori, Karachi - birni mafi girma a Pakistan. Bayan ya kammala, aka ba shi aikin koyarwa a matsayin malami a wata jami'ar musulunci da ke Banoori.

A cewar ɗaya daga cikin makusantansa Tahir Hameed, ya ambato Risaal -e-Jihad, wata jaridar ’yan tayar da ƙayar baya, ta ce Masood Azhar ya zauna tsawon lokaci a Afghanistan yana aiki tare da masu iƙirarin jihadi a 1989.

Bayan ya koma gida daga Afghanistan, Masood Azahar ya ci gaba da kira da tashin hankali a birane kamar Karachi, da Hyderabad, Sukkur, da Khupru, da Nawabshah da sauransu.

Ya kuma yi wani rubutu don bayyana ra'ayinsa kan ɗabbaƙa tsattsauran ra'ayin jihadi, wanda a cikin watan Janairun, 1990, ya fara buga jaridarsa ta wata wata da ya yi wa laƙabi da Sadae Mujahid "Muryar Mujahidai".

An ce dai ta samu goyan bayan ƙungiyar nan da aka haramta Harkat-ul-MUjahideeb, tsohuwar kungiyar masu tayar da ƙayar baya a Pakistan da ke ayyukansu a Kashimir.

‘Yan jarida da ƙwararru sun ce Masood Azhar ya rubuta littatafai 30 a kan jihadin, tarihi, da horo akan jihadi da yadda ake tafi da shi, yana mai jaddada mahimmancin Afghanistan don kare manufofin jihadi.

Kama shi da sakin sa da aka yi a Indiya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu daga cikin makusantansa sun ce ya ziyarci Indiya, da Bangladesh, da Saudiya, da Zambia da Birtaniya. A shekarar 1994, an kama shi a yankin Kashmir da ke ƙarƙshin ikon Indiya, kan zargin hannu a ayyukan ta'adanci da hukumomin Indiya suka yi masa.

A wata sanarwa da hukumar tattara bayanan sirri CBI ta Indiya ta fitar a lokacin da ya ke ɗaure, Masood Azhar ya ce ya je Indiya ne don dubawa ko akwai "jihadi" da za su iya yi a ƙasar, a cewar wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai a lokacin. Ya fara zuwa Bangaladesh, sannan ya wuce zuwa Delhi, babban birnin Indiya, da fasfon Portugal.

Sunan Masood Azhar ya shahara ne a lokacin da aka yi garkuwa da wasu baƙin turawa ƴan yawon buɗe ida, a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin Indiya a 1995. Masu garkuwar dai sun bayyana kansu da Al Faran, sannan sun nemi da a sake shi, wanda gwamantin Indiya ta ƙi.

Ana tunanin an halaka ƴan buɗe idanun, yayin da daya daga cikinsu ya yi unƙurin tserewa.

Bayan haka a ranar 24 ga watan Disamar 1999, aka yi fashin wani jirgin sama da ya taso daga Kathamandu babban birnin Napal, zuwa Delhi. Jirgin ya sauka a Kandahar a Afghanistan, inda Taliban ke mulki.

Wadan da suka yi fashin jirgin sun buƙaci da a saki Masood Azhar, sannan su saki matafiyan su 155 da ke jirgin, wanda bayan doguwar yarjejejniya, aka sako shi tare da wasu biyu Omar Saeed Sheikh da Mustataq Zarga.

Kafa ƙungiyar Jaish-e-Mohammed

Masood Azhar na kallon na'urara ɗaukar hoto a watan Satumba 1999 a gida yarin Jammu na Kot Bhawal. Ya a sanye da tabarau sannan ya yafa hirami a kansa. Yana da gemu da saje baƙi.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, An dai fi sanin Masood Azhar a duniya d mai ra'ayin riƙau da ke da ƙafin faɗa a ji a tsakanin musulman duniya

Gabanin a tsare shi a Indiya, Masood Azhar na cikin Harkat-ul-Mujahideen. Bayan a sake shi, sai ya sanar da kafa Jaish-e-Mohammed "Sojojin Muhammad") a Karachi a shekarar 1999.

Ya yanke alaƙarsa da Harkat-ul-Mujahideen, daga bisani Jem ta kama sansani masu yawa da a baya suke na Harkat-ul-Mujahideen.

A watan Afrulun 2000, wani harin ƙunar baƙin wake da aka kaia mota, a babban ofishin sojoji da ke Badami Bagh a Srinagar, a babban brinin yankin Kashmir da ke ƙarƙshin ikon Indiya. Shi ne harin baƙin wake da aka kai a tarihin Kashimir. Hukumomin Indiya sun ɗora alhakin hakan akan Jaish-e-Mohammed da kai shi.

A shekarar da ta gabata a watan Octoba, aka kai hari Jammu da majalisar Kashmir, a Watan Dismaba ma Disamba a dai shekarar, aka kai hari majalisar Indiya , inda kuma aka ɗora alhakin harin akan ƙungiyar ta JeM, sai dai JeMM ɗin ta musanta zargin.

A 2016, Indiya ta zargi JeM d akai hari kan filin jirgin sama a Pathankot, da ke tsakanin Indiya da Pakistan.

Indiya dai ta zargi JeM da wani hari da akakan ofishin jakadancin Idiya d ke Mazar-e-Shariff a Afganistan, da babban ofishin soji a Uri, da ke yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya, a 2016.

Shekaru uku baya, a cikin watan FAbarerun 2019, ƙungiyar ta kai wani hari na ƙunar baƙin waken da ya yi sanadiyar halaka sojoji 40 a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya.

Ayyana shi a matsayin dan ta'adda

Bayan harin da suka kai a 2001 a kan majalisar Indiya, Amurka ta sanya Jaish-e-Mohammed cikin jerin ƙuniyoyin ta'adda.

Bayan wannan, indiya ta yi ƙoƙarin ganin Mjalsair tsaro ta majalsair ɗinkin duniya ta sanya ƙungiyar cikin jerin ƙungiyoyin ta'adda na duniya, amma China ta hau kujerar naƙi.

Sai dai a wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai a Pulwama da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 40, wasu jami'an tsaron Indiya a watan Mayun 2019, majalisar ɗinkin duniya ta sanya sunan MAsood Azhar cikin jerin sunayen ƴan ta'adda.

Wannan harin dai sai da ya kusa haifar da yaƙi a tsakanin Pakistan da Indiya, bayan da Indiya ta mayar da maratanin hari ta sama Balakot, wanda hakan ya sa pakistan mayar da martani ita ma ta hanyar salon fadan sari ka noƙe.

A farkon shekara ta 2002, zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasar Pakistan Janar Perve Musharraf ya soke ƙungiyar, Jaish-e-Mohammed, sai dai daga bayan ƙungiyar ta ci gaba da harkokinta ƙarƙshin wani sunan Tanzeem Al-FruQan sannan suka kafa ƙungiyar kula d walwala da suka yi mata laaƙabi da Al-Rahmat.