Wane ne yariman Birtaniya da aka tuɓe wa rawani kuma me zai faru da shi?

Britain's Prince Andrew leaves the coronations of King Charles III and Queen Camilla, at Westminster Abbey, in central London, on 6 May 2023. Andrew is wearing a ceremonial jacket embroidered with gold symbols. There are raindrops on the window of the car.

Asalin hoton, Toby Melville / Getty Images

Lokacin karatu: Minti 9

Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da tafkawa, a yanzu an tuɓe shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko muƙami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda ɗa ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II.

Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da hakan.

A yanzu "za a riƙa kiransa da tsuran sunansa, wato Andrew Mountbatten Windsor," in ji sanarwar.

Masarautar na fatan wannan mataki nata zai kawo ƙarshen muhawara kan jerin abin kunyar da ake zargin yariman ya aikata waɗanda ake alaƙantawa da masarautar.

Yanzu an tuɓe masa, ƙarfi da yaji, duk wasu sarautu da ke kansa, kamar yariman York da sauran su.

Alfarma ɗaya da ta rage masa ita ce zai ci gaba da kasancewa cikin jerin magadan sarauta, kuma alamu na nuna cewa majalisa, idan ta ga dama tana iya soke sunansa a cikin jerin.

Haka nan bayan shekara ɗaya ana cece-ku-ce, Andrew zai rasa damar da yake da ita ta ci gaba da zama a gidan hutawa na masarauta, inda zai koma wani gida na daban, mallakin Sarki Charles da ke yankin Sandringham.

Me ake zargin Andrew da aikatawa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana zargin Andrew ne da hannu a cin zarafi ta hanyar lalata a wata shari'a da ake gudanarwa a Amurka.

An samu tsohuwar ƙawarsa, Ghislaine Maxwell da laifi a shari'ar, inda aka gano ta riƙa nemowa da kuma safarar ƙananan yara mata tana kai wa marigayi Jeffrey Epstein, wanda hamshaƙin mai kuɗi ne da aka kama da laifin lalata ƙananan yara, kuma amini ne ga Andrew.

A cikin tarkardun kotu, wata mata mai suna Virginia Giuffre ta ce tana daga cikin yara mata da Jeffrey Einstein ya ci zarafinsu ta hanyar lalata tun tana ƴar shekara 16.

Kuma a cikin zarge-zargen da ta yi har da cewa an kuma miƙa ta ga wasu zaman - ciki har da Andrew.

Virginia Giuffre ta ce Andrew ya ci zarafinta ta hanyar lalata sau uku a lokacin ba ta kai shekara 18 ba.

Lokaci na farko da ya yi hakan shi na a shekara ta 2001 a birnin Landan.

A wata fira da BBC, matar ta ce marigayi Eipstein da Ghislaine Maxwell ne suka gabatar da ita ga Andrew a wani kulob ɗin dare.

Giuffre ta ce za ta iya tuna lokacin da Ghislaine ta ce mata, a lokacin tana ƴar shekara 17, cewa wajibi ne "ki yi wa Andrewa irin yadda kike wa Jeffrey".

Virginia Giuffre, a woman with blonde hair tied back, wearing a white blouse and holding up a photograph of herself as a teenager.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Virginia Giuffre, riƙe da hotonta lokacin tana matashiya, ta ce sau uku ana tilasta mata kwanciya da Yarima Andrew

Virginia Giuffre, wadda ta kashe kanta a farkon wannan shekara ta wallafa ƙarin bayani kan cin zarafin lalata da ta zargi Andrew da aikatawa a kanta a wani littafi da ta rubuta.

Kwana huɗu gabanin wallafa littafin, Andrew mai shekara 65 a duniya, ya sanar da ajiye muƙaminsa na Yariman York, bayan tattaunawa da yayansa Sarki Charles III - wanda sarauta ce da mahaifiyarsa marigayiya Sarauniya Elizabeth ta naɗa shi.

Prince Andrew wearing a blue shirt with black trousers, standing next to Virginia Giuffre, with his arm around her waist. Ms Guiffre is wearing a tight tank top, revealing her lower stomach and multicoloured trousers with purple and pink patterns on them. Ghislaine Maxwell is standing behind them, leaning backwards a little. She is wearing a white top with a large circular collar that reveals her arms from her shoulders. All three are smiling.

Asalin hoton, US Department of Justice

Bayanan hoto, Yarima Andrew tare da Virginia Giuffre (tsakiya) da Ghislaine Maxwell, wadda aka ɗaure bayan samun ta da laifin kawalcin ƴan mata ga attajiri marigayi Jeffrey Epstein
A side shot of Prince Andrew speaking to Emily Maitlis during the recording of the 2019 BBC Newsnight interview reported worldwide. Large lights on large stands tower above them and another light is at their head level, in the centre of a window bay with large blue curtains drawn. A man wearing a waistcoat is in the corner of the shot, tending some equipment. A table with two glasses and a bottle of water is between Maitlis and the prince.

Asalin hoton, Mark Harrison / BBC

Bayanan hoto, A wata fira da BBC a shekarar 2019, Yarima Andrew ya shaida wa ma'aikaciyar BBC Emily Maitlis cewa ba zai iya tuna cewa ya taɓa haɗuwa da Giuffre ba

Yariman ya sha musanta zarge-zargen Ms Giuffre, kuma a shekarar 2019 ya shaida wa BBC cewa ba zai iya tuna cewa ya taɓa ganin ta ba.

A shekarar 2022, ɓangarorin biyu sun yanke shawarar sasantawa a wajen kotu, inda ya biya ta wasu kuɗaɗe da ba a ayyana yawansu ba, ba tare da amincewa cewar ya aikata laifin ba.

Me Virginia Giuffre ta ce kan Yarima Andrew?

Lawyer David Boies walks down the street with Virginia Giuffre on 27 August 2019. He is wearing a blue suit and blue tie. She is wearing a blue jacket and white-and-red patterned blouse, with a blue handbag looped over her left arm.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Virginia Giuffre a kusa da kotu a birnin New York tare da lauyantaDavid Boies, domin wani zama bayan mutuwar Jeffrey Epstein

A cikin littafin da ta rubuta Giuffre ta ce tana fargabar cewa "za ta kasance baiwar lalata har mutuwarta" a hannun Epstein da mutanensa.

A watan Maris ɗin 2001, Maxwell ta tayar da ita daga bacci ta ce mata yau za ta haɗu da wani "kyakkyawan yarima", kamar yadda Giuffre ta rubuta a littafinta.

A lokacin da suka haɗu, ta ce ta tuna yadda Maxwell ta ce wa Andrew ya canki shekarunta.

"Ya canka daidai - shekara 17", kamar yadda Giuffre ta bayyana, tare da ce mata: "Ƴaƴana [Gimbiya Beatrice da Gimbiya Eugenei] kin girme su da kaɗan."

Ghislaine Maxwell and Jeffrey Epstein on board a plane. Epstein is lounging in a seat with his legs stretched out. Maxwell is leaning forwards in a seat opposite him. She is smiling, while he has his mouth closed. Maxwell is wearing a white top and blue jeans. Epstein is wearing a grey hooded sweatshirt and black trousers.

Asalin hoton, US Department of Justice / PA Media

Bayanan hoto, An kama Ghislaine Maxwell da laifin yin kawalcin yara mata domin lalata ga attajiri Jeffrey Epstein

A wannan dare ita da Esptein da kuma Maxwell sun tafi kulof ɗin dare yariman, wanda ''yake zubar da zufa a lokacin,'' in ji Ms Giuffre.

Sannan yayin da su duka huɗun suka koma gidan Maxwell, an zargi Maxwell da faɗa mata: "Idan muka isa gid, za ki yi masa yadda kika yi wa Jeffrey."

"Mutum ne mai farna-farn, amma yana ji a jikinsa cewa kwanciya da ni tamkar wani haƙƙi ne nasa,'' in ji Ms Giuffre.

"Washe gari, Maxwell a kirata da sunan ƙawar yarima, saboda ta faɗa min cewa kin yi ƙoƙari. Yarima ya ji daɗi.''

Wata guda bayan nan, ta ce ta sake jima'i da yariman a karo na biyu, a New York, wato garin su Epstein.

VIctoria Guiffre standing in the sea, wearing a pink dress with splashes on the lower part. Her hands are held to her hips. She is looking at the camera with hair tied back. The sea is grey and there are clouds in the sky. The photo is within a photo binder.

Asalin hoton, Family via Penguin Random House

Bayanan hoto, Hoton Victoria Guiffre, a lokacin ana kiranta da suna Victoria Roberts

Karo na uku da aka yi zargin yariman ya yi jima'i da ita shi ne a wani tsibiri da ke New York, a wani abu da Ms Guiffre ta bayyana da ''baje-kolin jima'i''.

"Epstein, da kimanin wasu ƴan mata takwas da ni duka mun yi jima'i tare,'' in ji ta.

"Sauran ƴan matan duka ba su kai shekara 18 ba, kuma ba sa iya magana da turanci''.

"Epstein ya yi dariya kan ta yaya aka shawo kansu har suka yarda duk kuwa da ba sa iya magana da turanci, yana mai cewa su ne ƴan matan da ya fi samun saukin shawo kansu'',

Virginia Giuffre speaking at a podium outdoors, surrounded by a number of people.

Asalin hoton, Getty Images

Wata majiya a fadar Buckingham ta shaida wa BBC cewa karɓar littafin da jami'an fadar suka yi na nufin ''za a fuskanci kwanaki masu tsauri a fadar''.

Wane ne Jeffrey Epstein, mene ne kuma alaƙarsa da Yarima Andrew?

An undated handout photo made available by the New York State Division of Criminal Justice showing, Jeffrey Epstein, issued on 25 July 2019. Epstein is unshaven, with a grey and black beard, a black moustache, and grey-and-white short hair.

Asalin hoton, New York State Division of Criminal Justice Services / EPA

Bayanan hoto, Epstein ya kashe kansa a lokacin da yake ɗaure a gidan yarin New York, inda yake zaman jiran shari'a daga kotun tarayya.

Epstein mai kula da wani asusun ya rasu a 2019 a gidan yari, bayan samunsa da laifin safarar ƴan mata domin yin lalata da su. Likitan da ya duba gawarsa ya bayyana cewa shi ya kashe kansa.

A 2005 iyayen wata wata yarinta ar shekara 14 sun shaida wa ƴansanda cewa Epstein ya doki ƴarsu a wurin shakatwar da ke gidansa.

Binciken ƴan sanda ya gano hotunan yarinyar da yawa a cikin gidansa.

Daga nan aka yanke masa hukuncin ɗaurin wata 18 a gidan yari, inda aka sake shi bayan wata 13.

Prince Andrew talks to Jeffrey Epstein as they walk. Both are wearing dark coats. Andrew's left hand is gesturing as he talks to Epstein. The ground behind them has grass and brown leaves on it. Someone with blue jeans is behind them and only their legs and waist are visible.

Asalin hoton, News Syndication

Bayanan hoto, An ɗaurki hoton Yarima Andrew da Jeffrey Epstein suna tafiya a wan i wurin shaƙatawa a New York a Disamban 2010.

Yarima Andrew ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Newsnight cewa ya yanke alakarsa da tsohon abokinsa tun watan Disamban 2010, bayan ganawarsu a wani wurin shaƙatawa a New York.

To sai dai an samu wasu sakonnin email da suka nuna cewa yariman ya tuntubi Epstein watanni bayan haka.

Prince Andrew in a top hat and grey suit, laughing. Other men with top hats are beside him and a woman with a brown hat and long brown hair is in the background.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daga yanzu yariman ya koma Mista Andrew Windsor – amma bisa umarnin sarki

Me ƴansanda ke bincike?

Ƴansandan birnin London na "gudanar da cikakken bincike kan" jaridar da ta bayar da rahoton cewa Yarima Andrew ya buƙaci jami'in da ke tsaronsa da ya ''zurfafa bincike'' kan Ms Giuffre a 2011.

Rahoton ya ce yariman ya bai wa jami'in tsaron cikakkun bayananta domin gano ta taɓa aikata wani laifi ko wasu bayanai da ka iya ɓata mata suna.

Majiyoyin fadar Birtaniya sun ce zarge-zargen da aka yi wa yariman ana ''ɗaukarsu da matuƙat muhimmanci''.

Tun a shekarar 2019 Yarima Andrew ya daina aiki da fadar - kuma daga nan Fadar Buckingham ba ta fitar da bayanai a kansa.

Prince Andrew wearing finery in front of a royal guard. The prince has a black hat with a white feathery design. He has a gold sash over his left shoulder and a black jacket. The royal guard is standing to attention, wearing a red tunic with a white sash across his chest. He has a helmet with white feather-like material on the top and falling down the side of his head.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A matsayin ɗan sarauta, Yarima Andrew samu muƙamin yarima bayan haihuwarsa.

Shi za a iya tuɓe wa yarima Andrew sauran muƙamansa?

A matsayinsa na ɗan sarauta, ana kiranmsa da yarima tun lokacin haihuwarsa.

Amma a yanzu za a raba shi da wannan matsayi, amma sai sarki ya sanya hannu kan takardun umarnin.

Prince Andrew in a naval uniform alongside Sarah Ferguson in a white wedding dress riding in an open-topped carriage. Ms Ferguson is waving. Crowds line the street behind them.
Bayanan hoto, Yarima Andrew ya auri Gimbiya Sarah Ferguson daga 1986 zuwa 1996

An yi ta kiraye-kirayen Yarima Andrew da tsohuwar matarsa Sarah Ferguson su fice daga gidan sarauta da suke zaune a ciki, wanda ke kuda da majami'ar Windsor.

The Royal Lodge viewed from the air on 21 October 2025. It is a large rectangular white building with a lower atrium attached, set in luscious grounds. Some trees have brown leaves while others are green as the seasons turn from summer to autumn.
Bayanan hoto, Gidan Yarima Andew da ke cikin lambunan sarauta a kudancin Ingila.