Wane ne yariman Birtaniya da aka tuɓe wa rawani kuma me zai faru da shi?

Lokacin karatu: Minti 9

Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da tafkawa, a yanzu an tuɓe shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko muƙami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda ɗa ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II.

Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da hakan.

A yanzu "za a riƙa kiransa da tsuran sunansa, wato Andrew Mountbatten Windsor," in ji sanarwar.

Masarautar na fatan wannan mataki nata zai kawo ƙarshen muhawara kan jerin abin kunyar da ake zargin yariman ya aikata waɗanda ake alaƙantawa da masarautar.

Yanzu an tuɓe masa, ƙarfi da yaji, duk wasu sarautu da ke kansa, kamar yariman York da sauran su.

Alfarma ɗaya da ta rage masa ita ce zai ci gaba da kasancewa cikin jerin magadan sarauta, kuma alamu na nuna cewa majalisa, idan ta ga dama tana iya soke sunansa a cikin jerin.

Haka nan bayan shekara ɗaya ana cece-ku-ce, Andrew zai rasa damar da yake da ita ta ci gaba da zama a gidan hutawa na masarauta, inda zai koma wani gida na daban, mallakin Sarki Charles da ke yankin Sandringham.

Me ake zargin Andrew da aikatawa?

Ana zargin Andrew ne da hannu a cin zarafi ta hanyar lalata a wata shari'a da ake gudanarwa a Amurka.

An samu tsohuwar ƙawarsa, Ghislaine Maxwell da laifi a shari'ar, inda aka gano ta riƙa nemowa da kuma safarar ƙananan yara mata tana kai wa marigayi Jeffrey Epstein, wanda hamshaƙin mai kuɗi ne da aka kama da laifin lalata ƙananan yara, kuma amini ne ga Andrew.

A cikin tarkardun kotu, wata mata mai suna Virginia Giuffre ta ce tana daga cikin yara mata da Jeffrey Einstein ya ci zarafinsu ta hanyar lalata tun tana ƴar shekara 16.

Kuma a cikin zarge-zargen da ta yi har da cewa an kuma miƙa ta ga wasu zaman - ciki har da Andrew.

Virginia Giuffre ta ce Andrew ya ci zarafinta ta hanyar lalata sau uku a lokacin ba ta kai shekara 18 ba.

Lokaci na farko da ya yi hakan shi na a shekara ta 2001 a birnin Landan.

A wata fira da BBC, matar ta ce marigayi Eipstein da Ghislaine Maxwell ne suka gabatar da ita ga Andrew a wani kulob ɗin dare.

Giuffre ta ce za ta iya tuna lokacin da Ghislaine ta ce mata, a lokacin tana ƴar shekara 17, cewa wajibi ne "ki yi wa Andrewa irin yadda kike wa Jeffrey".

Virginia Giuffre, wadda ta kashe kanta a farkon wannan shekara ta wallafa ƙarin bayani kan cin zarafin lalata da ta zargi Andrew da aikatawa a kanta a wani littafi da ta rubuta.

Kwana huɗu gabanin wallafa littafin, Andrew mai shekara 65 a duniya, ya sanar da ajiye muƙaminsa na Yariman York, bayan tattaunawa da yayansa Sarki Charles III - wanda sarauta ce da mahaifiyarsa marigayiya Sarauniya Elizabeth ta naɗa shi.

Yariman ya sha musanta zarge-zargen Ms Giuffre, kuma a shekarar 2019 ya shaida wa BBC cewa ba zai iya tuna cewa ya taɓa ganin ta ba.

A shekarar 2022, ɓangarorin biyu sun yanke shawarar sasantawa a wajen kotu, inda ya biya ta wasu kuɗaɗe da ba a ayyana yawansu ba, ba tare da amincewa cewar ya aikata laifin ba.

Me Virginia Giuffre ta ce kan Yarima Andrew?

A cikin littafin da ta rubuta Giuffre ta ce tana fargabar cewa "za ta kasance baiwar lalata har mutuwarta" a hannun Epstein da mutanensa.

A watan Maris ɗin 2001, Maxwell ta tayar da ita daga bacci ta ce mata yau za ta haɗu da wani "kyakkyawan yarima", kamar yadda Giuffre ta rubuta a littafinta.

A lokacin da suka haɗu, ta ce ta tuna yadda Maxwell ta ce wa Andrew ya canki shekarunta.

"Ya canka daidai - shekara 17", kamar yadda Giuffre ta bayyana, tare da ce mata: "Ƴaƴana [Gimbiya Beatrice da Gimbiya Eugenei] kin girme su da kaɗan."

A wannan dare ita da Esptein da kuma Maxwell sun tafi kulof ɗin dare yariman, wanda ''yake zubar da zufa a lokacin,'' in ji Ms Giuffre.

Sannan yayin da su duka huɗun suka koma gidan Maxwell, an zargi Maxwell da faɗa mata: "Idan muka isa gid, za ki yi masa yadda kika yi wa Jeffrey."

"Mutum ne mai farna-farn, amma yana ji a jikinsa cewa kwanciya da ni tamkar wani haƙƙi ne nasa,'' in ji Ms Giuffre.

"Washe gari, Maxwell a kirata da sunan ƙawar yarima, saboda ta faɗa min cewa kin yi ƙoƙari. Yarima ya ji daɗi.''

Wata guda bayan nan, ta ce ta sake jima'i da yariman a karo na biyu, a New York, wato garin su Epstein.

Karo na uku da aka yi zargin yariman ya yi jima'i da ita shi ne a wani tsibiri da ke New York, a wani abu da Ms Guiffre ta bayyana da ''baje-kolin jima'i''.

"Epstein, da kimanin wasu ƴan mata takwas da ni duka mun yi jima'i tare,'' in ji ta.

"Sauran ƴan matan duka ba su kai shekara 18 ba, kuma ba sa iya magana da turanci''.

"Epstein ya yi dariya kan ta yaya aka shawo kansu har suka yarda duk kuwa da ba sa iya magana da turanci, yana mai cewa su ne ƴan matan da ya fi samun saukin shawo kansu'',

Wata majiya a fadar Buckingham ta shaida wa BBC cewa karɓar littafin da jami'an fadar suka yi na nufin ''za a fuskanci kwanaki masu tsauri a fadar''.

Wane ne Jeffrey Epstein, mene ne kuma alaƙarsa da Yarima Andrew?

Epstein mai kula da wani asusun ya rasu a 2019 a gidan yari, bayan samunsa da laifin safarar ƴan mata domin yin lalata da su. Likitan da ya duba gawarsa ya bayyana cewa shi ya kashe kansa.

A 2005 iyayen wata wata yarinta ar shekara 14 sun shaida wa ƴansanda cewa Epstein ya doki ƴarsu a wurin shakatwar da ke gidansa.

Binciken ƴan sanda ya gano hotunan yarinyar da yawa a cikin gidansa.

Daga nan aka yanke masa hukuncin ɗaurin wata 18 a gidan yari, inda aka sake shi bayan wata 13.

Yarima Andrew ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Newsnight cewa ya yanke alakarsa da tsohon abokinsa tun watan Disamban 2010, bayan ganawarsu a wani wurin shaƙatawa a New York.

To sai dai an samu wasu sakonnin email da suka nuna cewa yariman ya tuntubi Epstein watanni bayan haka.

Me ƴansanda ke bincike?

Ƴansandan birnin London na "gudanar da cikakken bincike kan" jaridar da ta bayar da rahoton cewa Yarima Andrew ya buƙaci jami'in da ke tsaronsa da ya ''zurfafa bincike'' kan Ms Giuffre a 2011.

Rahoton ya ce yariman ya bai wa jami'in tsaron cikakkun bayananta domin gano ta taɓa aikata wani laifi ko wasu bayanai da ka iya ɓata mata suna.

Majiyoyin fadar Birtaniya sun ce zarge-zargen da aka yi wa yariman ana ''ɗaukarsu da matuƙat muhimmanci''.

Tun a shekarar 2019 Yarima Andrew ya daina aiki da fadar - kuma daga nan Fadar Buckingham ba ta fitar da bayanai a kansa.

Shi za a iya tuɓe wa yarima Andrew sauran muƙamansa?

A matsayinsa na ɗan sarauta, ana kiranmsa da yarima tun lokacin haihuwarsa.

Amma a yanzu za a raba shi da wannan matsayi, amma sai sarki ya sanya hannu kan takardun umarnin.

An yi ta kiraye-kirayen Yarima Andrew da tsohuwar matarsa Sarah Ferguson su fice daga gidan sarauta da suke zaune a ciki, wanda ke kuda da majami'ar Windsor.