Ƙalubalen da ke gaban sabon shugaban NNPCL da Tinubu ya naɗa

Asalin hoton, Socila Media
A ranar Laraba ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin kamfanin mai na ƙasar na NNPCL, inda ya maye gurbinsa da Injiniya Bashir Bayo Ojulari.
Haka nan, Shugaba Tinubu ya rushe hukumar gudanarwar kamfanin ƙarƙashin shugabancin Cif Pius Akinyelure.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta yi ƙarin bayani dangane da kafa sabuwar hukumar gudanarwar kamfanin mai mutum 11 ƙarƙashin jagorancin Injiniya Ojulari, da kuma Ahmadu Musa Kida a matsayin shugaba maras cikakken iko.
A zamanin Kyari aka yi sauye-sauye da dama kan harkokin gudanar da kamfanin, babban daga ciki shi ne mayar da kamfanin zuwa na kasuwanci wanda ke aiki domin samar da riba.
Haka kuma a zamaninsa ne gwamnatin Najeriya ta shiga yarjejeniyar sayar wa matatar mai ta Dangote ɗanyen mai a naira, wanda hakan ya sauƙaƙa farashin fetur ɗin a Najeriya a lokacin.
To ko wane irin ƙalubale sabon shugaban na NNPCL zai iya fuskanta a zamaninsa?
Saita farashi da kyautata alaƙa da matatar Dangote

Asalin hoton, Getty Images
Cikin manyan ƙalubalen da ake tunanin sabon shugaban zai fuskanta akwai kyautata alaƙa tsakanin matatar mai ta Dangote da kamfanin na gwamnati.
Wannan alaƙar na da alaƙa kai-tsaye da farashin da 'yan Najeriya za su dinga sayen man fetur.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanin harkokin makamashi Injiniya Yabagi Sani ya ce babban ƙalubalen ya fi girma a ɓangaren yarjejeniyar sayar wa Ɗangote ɗanyen mai a naira.
"Ko a lokacin da ake sayar wa Dangote ɗanyen mai a naira akwai wasu manyan kamfanonin kasuwancin man fetur da manyan ƴankasuwar ɓangaren da suke adawa da hakan," in ji shi.
"Yanzu ana zargin cikin manyan jagororin kamfanin na ƙasa akwai waɗanda dama tun farko suna adawa da sayar wa Dangote ɗanyen man a naira."
Shi ma Farfesa Ahmed Adamu - ƙwararre a ɓangaren tattalin arzikin man fetur a jami'ar Nile da ke Abuja - ya ce lallai ƙalubalen ya zo daidai lokacin da yarjejeniyar ta ƙare.
"Ya zo a lokacin da ake ganin farashin ya fara komawa gidan jiya bayan ya ɗan yi ƙasa a baya. Kuma ya fara tashi ne biyo bayan ƙarewar yarjejeniyar sayarwa Dangote ɗanyen mai ɗin a naira domin shi ma ya riƙa sayarwa da naira," a cewar farfesan.
Farfesa Adamu ya ce idan aka koma cinikayya da dala, lallai farashin man zai ƙaru a lokacin sabon shugaban na NNPCL.
"Amma wannan tsari ne na gwmamnati. Shugaban ƙasa ko jami'an gwamnatinsa ne suka tsara kuma su ne za su iya cewa a koma a ci gaba. Iyaka dai a tuntuɓi kamfanin na NNPCL kan ko yana da isasshen mai da kuma isasshiyar dala, don haka yana tsakiya."
Farfesa Adamu ya ƙara da cewa za a iya ganin tashin farashin a sanadiyar cinikayya da dala, "saboda shugaban kamfanin ba shi ba ne yake da wuƙa da nama".
Sai dai ya ce sabon shugaban ƙwararre ne.
"Duk da cewa ba daga cikin NNPC ɗin aka ɗauko shi ba, amma lallai ya san harkar sosai. Cikin manyan abubuwan da ake buƙata daga sabon shugaban akwai haɓaka samar da ɗanye mai a Najeriya, da farfaɗo da matatu, da samar da iskar gas. Duk zai iya yi saboda ba baƙonsu ba ne."
"Zuwansa daga wajen NNPC zai taimaka wajen samun sababbin tsare-tsare a kamfanin."
Cin gashin kai
Da yake yi wa BBC ƙarin haske kan sauran ƙalubalen, Injiniya Yabagi Sani ya ce sabon shugaban zai iya fuskantar katsalandan daga gwamnati.
"Babu wani abin da zai sauya kawai don an canza shugaban kamfanin. Shi dai sabon shugaban ƙwararre ne, amma damuwar ita ce har yanzu kamfanin ba shi da cikakken iko. Har yanzu gwamnati ce ke da damar naɗa masu tafiyar da harkokinsa, idan kuwa aka ci gaba a haka, siyasa za ta iya shiga ciki," in ji Yabagi.
Ya ce idan siyasa ta shiga, "ba dole ba ne a samu abin da ake nema".
Yabagi ya ce sabon shugaban hukumar ɗankasuwa ne kamar sauran ƴankasuwar man fetur, "mutumin da ke kasuwancin fetur a ce yana shugabantar kamfanin fetur na ƙasa, da wanne zai ji? haɓaka arzikin kamfaninsu ko na ƙasar?"
Sai dai a nasa ɓangaren, Farfesa Ahmed Adamu ya ce da ma a al'adance gwamnatin ce ke da alhakin naɗawa da sauke shugabancin NNPCL.
"Ai kamfani ne na gwamnati. Ma'aikatar kuɗi da ta fetur ne suke da mallakin kamfanin, kuma duk suna ƙarƙashin shugaban ƙasa ne," in ji shi.
Haka nan, Farfesa Ahmed na ganin ɗankasuwa ne ya fi cancanta ya ja ragamar kamfanin.
"Gaskiya ɗankasuwa ne [Injiniya Bayo], amma da ma al'adar da ya kamata a ɗaura kamfanin a kai kenan ta yadda zai dinga gogayya da kamfanoni da burin cin riba, da fafatawa da sauran kamfanoni wajen samar wa gwamnati kuɗin da za ta yi wa al'umma aiki."











