Yadda rijistar ƴan jam'iyyar ADC ke gudana a Najeriya

ADC

Asalin hoton, X/ADC

Lokacin karatu: Minti 2

An fara aikin rijistar mambobin jam'iyyar ADC a sassan Najeriya.

Jam'iyyar ta ce aikin wanda za a shafi ƙwanaki 90 ana yi a faɗin kasar ya ƙunshi rijistar sabbin mambobi da kuma sabunta ta tsofaffin mambobin jam'iyyar.

Wannan dai a cewar jam'iyyar sharar fage ne ga babban taron ta na ƙasa, wanda zai samar da zaɓaɓɓun shugabanninta a matakin ƙasa.

Tun daga ranar Asabar 13 ga watan Dismbar 2025, ne aka fara aikin rijistar mambobin jam'iyyar ta ADC a Najeriya, bayan wata sanarwa da sakataren ta na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fitar.

A cikin sanarwar Bolaji Abdullahi ya yi bayanin cewa an cimma matsayar gudanar da wannan aikin ne tun a babban taron kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ranar 27 ga watan Nuwambar 2025.

Faisal Kabiru Malam Madori, na daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ADC, ya shaida wa BBC yadda tsarin nasu ke tafiya.

Ya ce,"Dukkan 'yan jam'iyyarmu da ke jihohin Najeriya 36 da kuma Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya za su je inda yak e dangwala kuri'arsa wato akwatinsa ya je ya yi rijista ya zama dan jam'iyya sannan ya karbi katinsa na jam'iyya."

Faisal Kabir, ya ce," Ta hanyar wannan rijistar ne zamu samu damar sanin mutanen da ke cikin jam'iyyarmu da kuma wanda zasu zabi wakilai na jam'iyya a akwatuna, saboda mu a ADC ana fara zaben shugabanci ne daga akwati bad aga mazaba kamar yadda aka saba."

Mai magana da yawun jam'iyyar ADCn ya kuma yi bayanin yadda babban taron jam'iyyar tasu na ƙasa zai kasance a nan gaba.

Ya ce," Za ayi zabe na akwatuna da kananan hukumomi da kuma na jiha a cikin watan Janairu, sai ranar 12 ga watan Fabrairu na 2026, za ayi babban taron jam'iyyarmu na kasa."

Jam'iyyar ADC dai ta ce ta na sane da muhimmancin yin taka tsan-tsan a yanayin da take ciki a halin yanzu, don haka ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin cimma nasarar aikin rijistar mambobin nata ba tare da wata tangarɗa ba.

Ana dai sa ran a ƙarshen wannan aiki ne jam'iyyar za ta fitar da alƙaluman yawan mambobinta a sassan Najeriya, da kuma ci gaba da shirye-shiryen fuskantar babban zaɓen ƙasar na 2027.