Ƴan jihar Kano uku da suka rasa muƙamansu saboda siyasa

..

Asalin hoton, BBC collage

Lokacin karatu: Minti 4

Masu nazarin siyasa na ganin cewa idan dai har ba ƴan siyasar jihar Kano ba su gyara zamansu ba da haɗa kai, to jihar ka iya fuskantar koma-baya ta fuskar wasu muƙaman gwamnatin tarayya.

Rikicin siyasa tsakanin jiga-jigan ƴan siyasar jihar ya janyo kodai wasu yin asarar wani muƙami sakamakon sauya su ko kuma jihar ta rasa baki ɗaya.

Rashin jituwa tsakanin ƴan siyasa a jihar ya janyo mummunar taƙaddama da aka daɗe ba a gani ba a baya-bayan nan inda har yanzu ake da mutum biyu da ke iƙrarin sarautar jihar.

Irin wannan rikici a baya-bayan nan ne ya so ya tayar da zaune tsaye lokacin da ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje ya yi ƙoƙarin kafa rundunar Hisba wadda ɓangaren gwamna, Abba Kabir Yusuf ke ganin za ta kishiyanci hukumar Hisba da ke ƙarƙashin gwamnatin jiha.

BBC ta yi nazari wasu muƙamai da aka yi dambarwa a kansu inda aka samu sauyin waɗanda aka naɗa ko kuma aka rasa kujerar kwata-kwata.

Maryam Shetty

..

Asalin hoton, BBC COLLAGE

A watan Agustan 2023 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga Kano, a matsayin wadda za a naɗa kan muƙamin minista, inda ya maye ta da sunayen mutum biyu.

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da haka a wata wasiƙa da shugaban ƙasar ya aika wa majalisar kuma ya karanta yayin zaman majalisar.

Sunayen mutum biyu da Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar sun haɗar da Festus Keyamo da kuma Dr. Mariya Mairiga wadda ita ma daga jihar Kano take.

To sai dai daga baya bayanai suka nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya nemi a sauya ta da sunan Dakta Mariya Mairiga.

Tsohon shugaban Jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce wasu 'yan ba-ni-na-iya ne suka bayar da sunan Maryam Shetty don naɗa ta minista daga Kano ba tare da saninsa ba.

Ganduje ya ce shi ne ya sanar da Tinubu rashin cancantar Maryam Shetty.

''Ya ce min ga fa abin da ke faruwa, shin kai ka bayar da sunanta? Sai na ce masa a'a sam sam, ba ni ba ne, ban ma sani ba, daga nan ya ce to ya ka gani? akwai buƙatar a canja?, sai na ce masa ƙwarai da gaske kuwa'', in ji tsohon gwamnan na Kano.

Abdullahi Tijjani Gwarzo

..
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani ɗan jihar Kano da ya ga samu ya ga rashi sakamakon rikicin siyasa shi ne tsohon ƙaramin ministan gidaje, Abdullahi T. Gwarzo wanda ya yi kawai a kan mulki kafin cire shi daga ministan a 2024.

Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa.

Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi , T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, saboda a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi.

''Batun ya zo min da mamaki, domin ba na tunanin wani abu mai kama da wannan zai faru da ni'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi la'akari da tarayyarsu tun ta da can wajen naɗa shi muƙamin.

Ya ce fiye da shekara 14 suna tare da Tinubu tun a jam'iyyar ACN, shi da Nuhu Ribadu da Sanata George Akuwam - da ke riƙe da muƙamin sakataren gwamnati a yanzu.

Sai dai ya ce Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karɓe a duk lokacin da ya so, don haka ya ce yana gode wa shugaban ƙasar, bisa damar da ya ba shi a gwamnatin tasa.

To sai dai a watan Okotoban 2024 sai Shugaba Tinubu ya naɗa Abdullahi Ata wanda shi ma ɗan jihar Kano ne domin ya maye gurbin Abdullahi Gwarzo.

Daga baya an jiyo magoya bayan Abdullahi Tijjani Gwarzo na zargin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da hannu a sauke shi, to amma magoya bayan Barau Jibrin sun musanta.

Injiniya Abdullahi Ramat

..

Asalin hoton, Ramat/Facebook

Kujerar da jihar Kano ta rasa baki ɗaya ita ce ta shugabancin hukumar da ke sa ido kan harkar wutar lantarki wato NERC sakamakon rikicin siyasa da ƴan jihar da dama suke zargi.

Shugaba Bola Tinubu ya maye gurbin Injiniya Abdullahi Ramat da Dakta Musliu Olalekan Oseni a matsayin shugaban hukumar da ke sa ido kan harkar wutar lantarki wato NERC bayan majalisar dattawan ƙasar sun amince da naɗin a ranar 16 ga watan nan na Disamba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, Bola Tinubu ya kuma naɗa Dakta Yusuf Ali a matsayin mataimakin shugaban hukumar ta NERC.

A watan Agusta ne dai shugaba Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Ramat, mai shekaru 39 a matsayin shugaban hukumar.

Kuma jim kaɗan bayan naɗinsa ne Injiniya Ramat tare da magoya baya da jami'an tsaro suka yi dafifi zuwa hedikwatar hukumar domin kama aiki, tun kafin a rantsar da shi.

Magoya bayan Injiniya Ramat sun zargi mataimakin majalisar dattawa, Barau Jibrin da hannu a rashin rantsar da Ramat da kuma maye gurbinsa. Sai magoya bayan Barau Jibrin sun ce babu ruwan uban gidan nasu.