'Za a miƙa ɗaliban jihar Kebbi da aka ceto daga 'yan bindiga ga iyayensu'

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris

Asalin hoton, Nasir Idris/X

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Laraba ne ake sa ran gwamnatin jihar Kebbi za ta mika ɗaliban makarantar 'yan matan nan ta garin Maga da aka sace a makon da ya gabata ga iyayensu, bayan da aka sami nasarar karɓo su daga hannun 'yan bindiga a ranar Talata.

Yanzu haka dai murna na nan har kunne a wajen gwamnati da al'ummar jihar da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki, sakamakon nasarar da aka samu ta ceto ɗaliban.

Bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin a hanzarta bin matakan ganin an kuɓutar da yaran, har ya tura ƙaramin ministan tsaro na ƙasar zuwa jihar, Bello Matawalle don ganin an aiwatar da wannan umarni.

A kan wannan nasara da aka samu, gwamnan jihar ta Kebbin, Nasir Idris ya shaida wa wani taron manema labarai a birnin Kebbi, babban birnin jihar, yadda aka karɓo dalibai:

''Shugaban ƙasa ya ba jami'an tsaro umarni ba saboda komai ba saboda su tabbatar da cewa an je an gano inda waɗannan yara suke kuma an amso su.

''Kuma muna tabbatar wa uwayen yaran da al'ummar jihar Kebbi cewwa waɗannan yaran an same su kuma lafiya lau aka same su.

''Kuma muna ƙara gode wa Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu da dukkanin jami'an tsaro da suka kama suka amshi umarnin shugaban ƙasa suka tabbatar cewa waɗannan yara an amso su. ''

Gwamnan ya ƙara da cewa, ''bayanai sun tabbatar mana lafiya suke. Mun aika a ɗauko iyayensu saboda za a miƙa mana su, mu kuma za mu gabatar da su ga uwayensu a maishe su gida su koma cikin iyalensu.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dangane da zargin da ake ta yi, cewa sai da aka biya makudan kudin fansa, kafin a sami nasarar karbo daliban makarantar sakandiren ta garin Maga na jihar Kebbi kuwa, gwamnan jihar ya musanta hakan:

''Bayanan da aka ba mu shi ne cewa ba a biya kuɗin fansa ba aka sake su. Mu dai gwamnatin jihar Kebbi ba mu bayar da ko kwabo ba. Saboda haka su waɗannan jami'an tsaro sun tabbatar mana su ma ba da kuɗi suka je karɓo yaran nan ba,'' in ji gwamnan.

A ranar Litinin ta makon jiya ce dai 'yan bindiga dauke ma miyagun makamaisuka sace daliban su ashirin da biyar, daga makarantar sakandiren 'yan mata ta garin Maga na yankin karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi. Bayan da maharan suka kashe mutum biyu a makarantar.

Ana cikin jimamin aukuwar wannan abin kaico-kaico ne kuma, kwatsam sai ga bullar labarin sace wasu dalibai akalla dari biyu da sittin da biyar daga makarantar sakandiren St Mary da ke garin Kwantagora na jihar Neja, da kuma jerin wasu sace-sacen mutane da dama a jihohin Kwara da Sakkwato da kuma Kano a baya-bayan nan.

Al'amuran da suka tayar da hankulan jama'a matuka, tare da haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Najeriya.