Bambancin ƴaƴan maraina na maza da na birrai

Asalin hoton, Getty Images
Ƴaƴan maraina da ke jikin maza na da ƙanƙanta idan aka kwatanta su da na wasu dangin birrai. Sai dai akwai ayar tambaya kan wasu sassan jiki.
Jikin ɗan'adam dai yana kunshe da ƙwayoyin halitta, idanu, hanta da ƙwaƙwalwa da sauransu - ya fuskanci sauyi daban-daban cikin tsawon shekara biliyan huɗu da suka wuce.
Sai dai, masana na ci gaba da buƙatar son sanin abin da ya sa sassan jikinmu yake a yanayinsa. Alal misali, baya ga nauyin jiki, shin marainan maza sun fi na goggan birrai girma ne har ninki uku, amma sau biyar ƙasa da na dangin birrai na chimpanzees?
Kamar yadda na bayyana a cikin littafina mai taken, "Itacen rayuwa," muna ci gaba da neman amsar waɗannan tambayoyi. Mun fara samun wasu.

Asalin hoton, Getty Images
Misali, mu ƴan adam muna cikin wani na'ui na dangin dabbobi, ciki har da birrai.
Dangogi da muke tare da su sun nuna yadda sassan jikinmu yake.
Akwai hanyar da za a bi wajen nazarin sassan jikin mu, sai dai hakan zai iya yiwuwa ne kaɗai idan waɗannan sassa suka sauya sama da sau ɗaya a tsawon rayuwa.
Girma yana da muhimmanci yayin sauyi
Amma sauyawar zamani yana zama mai amfani idan muka kalle shi a matsayin wani nau'in gwaji.
Misali shi ne yadda ƴaƴan marainan wasu birrai ke da girma.
Mutanen da suka balaga waɗanda ke dangi ɗaya da birran colobus, girman marainan su iri ɗaya ne.
Sai dai kamar na'uin birrai na chimpanzees, mutane, da kuma na'uin gorilla, suna da mabambantan maraina.
Ƴaƴan marainan birrai na'uin Colobus yana da nauyin giram 3, yayin da na wasu kuma ya kai har giram 48.
Ana samun dangin birrai masu girman maraina ne daga waɗanda suka fi yawan jima'i.
Za a iya samun bayanai da yawa kan wannan. Alal misali, manyan maraina, na iya zama wata hanya ta jawo hankalin mata, kamar jelar dawisu.
Namijin biri na'uin colobus yana fafatawa sosai don samun damar saduwa da macen da za su yi aure.
Birrai na'uin Macaques, suna zaune cikin lumana haɗe da birrai kusan 30 kuma suna da wata hanya ta daban ta yin soyayya.

Asalin hoton, Getty Images
Idan muka yi duba kan ɗaukacin yanayin rayuwa da ya ƙunshi dabbobi masu shayarwa, mun ga cewa akwai ƙungiyoyin shayarwa da dama da suke da bambancin girman ƴaƴan maraina.
A nan, yawancin an fi samun masu girman ƴayan maraina wajen waɗanda suka fi buƙatar jima'i, ƙanana kuma ga wasu.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mun samu damar gano bambanci tsakanin girman maraina da kum salon jima'i a cikin ɗaukacin dangin dabbobi masu shayarwa.
Amma a cikin mutane, girman maraina yana wani wuri a tsakanin.
Haɓar ɗan'adam ta zama abin cece-kuce da masana kimiyya ke tababa a kai.
Kamar yadda yake da ƴaƴan maraina, akwai ra'ayoyi da suka bayyana yadda haɓar ɗan'adam ta fara har zuwa sauyi.
Zai yiwu ta samo asali don ƙarfafa muƙamuƙin namiji idan an yi faɗa. Hakanan zai iya zama ya girma ne don sanya gemun mutum ya zama cikakke. Ko kuma yana iya kasancewa sakamakon cin abincin da aka sarrafa, wanda ba dole ba ne ya haifar da raunin muƙamuƙi.
Duk da haka, abin sha'awa, babu wani dangin dabba mai shayarwa da ke da haɓa.
Amma saboda chin da ke cikin Homo sapiens ya bambanta a tsakanin dabbobi masu shayarwa, ba mu da yadda za mu gwada kowace irin waɗannan ka'idoji.
Watakila wasu sassa na yanayin ɗan'adam Allah ya halicce su ne ta yanda yana da matukar wahala a yi bayani mai gamsarwa kansu har abada.











