Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda annobar tsutsa ta afka wa gonakin tumatir a Najeriya
Ƙungiyar masu noman tumatir a Najeriya ta bayyana fargabar samun ƙaranci da tsadar tumatir, saboda barnar da wata tsusa ta yiwa dumbin gonakin da ake noma shi a sassan kasar.
Dubban manoma ne al'amarin ya shafa wadanda suka zuba kudinsu wajen yin noman tumatir din amma hatsabibiyar tsutsar ta mamaye shi, inda kungiyar ta ce tuni suka fara ganin tasirin ta'adin da tsusar ta yiwa gonaki.
Kungiyar manoman tumatir ta kokawa cewa tun farkon watan Maris din shekarar nan suka fara ganin bullar fitinanniyar tsutsar timatir din da ake kira Tuta Absaluta, inda ta yiwa dumbin gonaki mummunar barna a wasu jihohin arewacin Najeriya.
Wasu manoman sun rasa illahirin abin da suka noma na milyoyin naira.
Alhaji Sani Danladi Yada-Kwari shi ne shugaban kungiyar manoma timatir na jihar Kano, kuma sakataren kungiyar na kasa. Ya ce tsutsar ta yi mummunar illa a jihohin Kano da Jigawa da kuma Bauchi.
''Musamman a nan jihar Kano, ta y imana ta'adi matuƙa duba da yadda duk wanda ya zama timatirinsa bai fara ɗibar shi ba, wanda ya dasa shi daga watan 11, watan 12 wallahi bai sami komai a gonarsa ba.''
Alhaji Sani Yada-Kwari ya ƙara dacewa ''akwai wanda ya gama aikinsa gaba ɗaya, yana tunanin zai ɗiba, timatirin ya ƙone. Wani ya je gonarsa ya ga timatir ɗin amma a kwana uku gaba ɗaya tsutsar nan ta lalata shi''
A kan haka ne ma ƴan kasuwar ke hasashen cewa a bana za a samu tsadar timatir sosai domin tsutsar ta yi illa sosai a gonaki.
Dangane da girman ɓarnar da manoman suka yi kawo yanzu kuwa, Alhaji Sani Yada-Kwari ya ce har yanzu suna tattara alƙalumma, ''amma ina tabbatar maka a nan jihar Kano, manoma sun yi asarar da ba ta gaza naira biliyan 20 ba.''
Yanayin zafi na cikin abubuwan da ke sanya tsutsar tumatir din ta'azzara, kuma tana da wuyar magani, kasancewar ta na bijirewa maganin da ake fesa mata.
Shima sakataren kungiyar masu hada-hadar tumatir a kasuwar Ƴan Kaba, Alin Bello ya ce yanzu haka akwai ƙarancin timatir a kasuwanni saboda wannan matsala.
Ya ce ''Basoda bay a da kyau, mutane da yawa ba su sayen shi kuma ya zamo ɗan kaɗan, idan aka kawo shi kasuwa kuma baka sayar ba, kafin yamma tsutsar ta gama cinye shi ya gama lalacewa. Haka ya janyo babu mai kyau a yawancin sassan Kano.''
Tsutsa Tuta Absaluta dai ta na da matukar hadari, inda Alhaji Sani Danladi Yada-Kwari shugaban kungiyar manoma tumatir na jihar Kano, ya shawarci manoman, da su rika daukar mataki cikin gaggawa da zarar sun ganta a gonakinsu tare da kiran gwamnati ta kawo musu dauki.