Yadda ICPC ta bankaɗo ɗaruruwan badaƙalar ayyukan mazaɓu a Najeriya

Asalin hoton, ICPC
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ta ce ta bankado, tare da kwato kusan Naira miliyan 350 na kudaden ayyukan mazabun yan majalisar dokokin kasar.
Shugaban hukumar Dr Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana hakan a taron hukumar na ƙarshen shekara game da nasarorin da suka samu, inda ya ce hukumar ta hana zirarewar kuɗin gwamnati a 2024 da suka kai naira biliyan 400.
Malam Hassan Salihu shi ne mataimakin darakatan a hukumar ta ICPC, ya ce sun bibiyi ayyukan mazaɓu 1,500 a jihohi 22 a faɗin Najeriya, inda a nan ne suka gano wannan badaƙala.
''Ba'ayi aikin da aka tsara yi da wadannan kuɗaɗe ba, don haka muka kwato su, dama kuma wannan shine aikinmu, tabbatar da cewa talaka ya amfana da kudinsa ba a karkatar da su ba'' inji shi.
Malam Hassan Salihu, ya ce wannan daya ne kacal daga cikin tarin nasarorin da suka samu a wannan shekara da ake shirin bankwana da ita, kuma suna alfahari da hakan.
Ya kara da cewa a duk shekara suna sanar da irin nasarorin da suka yi wajen yaki da cin hanci, don haka a wannan shekara ma akwai ayyuka da suke bibiya da bangaren zartarwa ke gudanarwa da kuma na mazabun yan majalisa.
''Mun yi bibiya a kan ayyukan da kudinsu ya kai Naia biliyan dari shida da goma, kuma an samu kudade da yawa a cikinsu, sannan akwai kadarori da yawa da muka kama, sannan mun hana sace kudaden da aka so sacewa sun fi Naira biliyan talatin'' a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa akwai wasu hukumomi da suka karrama bisa hadin kan da suke ba su, inda a wannan shekarar hukumar shirya jarrabawar Jamb da suka zo na daya, sai hukumar sufurin jirgin kasa da suka zo na biyu, da hukumar sayar da lantarki ta kasar da suka zo na uku.
Ya ce akwai nasara a ayyukan da hukumar ta su ke ci gaba da gudanarwa a duk shekara ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa a ƙasar.











