Ƴan Najeriya sun bayar da cin hancin naira biliyan 721 a 2023, me hakan ke nufi?

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ce dai ta fitar da alƙaluma cewa 'yan Najeriya sun bai wa jami'an gwamnatin ƙasar naira biliyan 721 kwatankwacin dala biliyan 1.26 a matsayin cin hanci a 2023.
Rahoton ya ce ƴan Najeriyar sun bayar da rashawa sau miliyan 87, amma adadin ya yi ƙasa idan aka kwatanta da miliyan 117 da suka bayar a 2019.
Cikin duka ƴan Najeriyan da suka ga aƙalla wani jami'in gwamnati ɗaya cikin wata 12 kafin gudanar da binciken a 2023, kashi 27 sun bai wa jami'in cin-hanci.
Idan aka kwatanta da abin da aka saba gani a baya, hakan na nufin yawan biyan cin-hanci a Najeriya ya ragu kaɗan zuwa kashi 23 tun daga 2019, lokacin da aka samu kashi 29 da suka bayar da cin hanci.
A wuraren da kuma aka tambayi cin-hanci amma mutane suka ƙi bayarwa, an ba da cin-hancin fiye da sau ɗaya cikin haɗuwa uku (kashi 34 cikin 100) a 2023.
Sai dai kuma kashi 70 cikin 100 na mutanen da aka nemi su bayar da cin hancin a 2023 sun ƙi bayarwa sama da sau ɗaya.
Kazalika, binciken ya gano cewa raguwar bayar da cin-hancin ta fi yawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya da kashi 76, duk da cewa sauran yankunan sun samu sama da kashi 60 cikin 100.
Waɗanne hanyoyi aka bi wajen tattara alƙaluman?

Mun tambayi Dakta Kole Shettima, shugaban Gidauniyar MacArthur Foundation a Najeriya, wadda da haɗin gwiwarta ne hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS, ta samar da wannan rahoto.
"An tambayi mutane 34,000 waɗanda ba a san su ba a fadin Najeriya abin da ake kira da "systematic randomised sampling" da turanci. Kuma ta haka ne muka iya fahimtar yawan kuɗaɗen da aka kashe."
Sai dai kuma dakta Kole ya ƙara da cewa "waɗannan alƙaluma ba su ke nan ba. Wannan na ƙananan rashawa ne da ke faruwa yau da kullum. Ba rashawar da ake ci da biro ta manyan ma'aikata ba.
To amma abin da nake so a fahimta an samu ragi a yanzu fiye da a baya." In ji Dakta Kole Shettima.
Me hakan yake nufi ga Najeriya?
Masu fafutukar yaƙi da rashawa da cin-hanci a Najeriya, irin su Awwal Musa Rafsanjani sun ce al'amari ne "mai ban takaici" da ke nufin kusan duk wani abu da za a yi sai an bayar da na goro wanda kuma ke ƙara zubar da kimar ƙasar a idanun duniya.
"Hakan na nufin duk abin da za ka yi a Najeriya sai ka bayar da cin-hanci. Idan kana neman aiki sai ka bayar da cin hanci. Idan kana neman ƙarin girma a wurin aiki sai ka bayar da cin-hanci. Idan zaɓe za ka tsaya sai ka bayar da cin-hanci. Harkar tsaro da ilimi da komai akwai wannan matsala. Kai hatta a wuraren ibada da fadar gargajiya.
Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da martabar Najeriya ta zube saboda yadda aka mayar da cin hanci wani abin ado." In ji Malam Auwal Rafsanjani.
Waɗanne hanyoyi za a wajen magance matsalar?

Auwal Rafsanjani ya ce ba wai aiki ko kuma laifin gwamnati ne ita kaɗai ba. Dole ne al'umma baki ɗaya su tashi tsaye wajen yaƙar rashawa da cin-hanci. Ya kuma lissafa matakai huɗu da ya ce su ne za su tabbatar da kawo ƙarshen matsalar rashawa da cin hanci.
- Ƴan ƙasa su tashi tsaye: Auwal Rafsanjani ya ce "ba zai yiwu ƙasa mai mutum fiye da miliyan 200 a ce jami'an EFCC ko ICPC ko sojoji ko ƴansanda to ba zai yiwu ba. Kowa sai ya yi abin da ya kamata. Kowa sai ya sauke nauyin da ke kansa. Dole ne idan an ba ka ka ƙi ƙarba sannan kai kuma ka da ka bayar kuma idan ka gani ana yi ka kwarmata."
- Zaɓen shugabanni na gari: Dole ne ƴan ƙasa su rinƙa zaɓen mutanen na gari musamman ƴan siyasa saboda idan aka zaɓi baragurbi to za su kau da kai ga barin al'amuran da suka shafi rashawa da cin-hanci.
- Gwamnati ta tabbatar da dokoki: Masanin ya ƙara da cewa dole ne ita kuma gwamnati a nata ɓangaren ta tabbatar da an bi dokoki da hukunce-hukunce kan rashawa da cin-hanci.
- Alƙalai na da rawa: Auwal Rafsanjani ya kuma ce "dole ne alƙalai su rinƙa hukunta waɗanda ake samu da laifukan rashawa da cin-hanci. Bai kamata a rinƙa sassaunata wa mutanen da aka samu dumu-dumu da laifukan almundahana ba."











