Yadda za ku iya ganin jinjirin watan Ramadan

Lokacin karatu: Minti 3

A Talatar nan ne ƙasashen duniya da dama za su duba jinjirin watan Ramadana, wanda shi ne zai tantance ranar da Musulmi za su tashi da azumi a wannan shekara ta 2026.

Fadar Sarkin Musulmin Najeriya, Mai alfarma Sa'ad Abubakar ta buƙaci al'ummar ƙasar su duba jinjirin wata, kasancewar Talata 17 ga watan Fabarairu ita ce 29 ga watan Sha'aban na shekarar 1447 bayan hijira.

A cikin sanarwar da fadar ta fitar ta ce "a sanar da Sarkin Musulmi" ta hanyar amfani da wasu lambobin waya da ta bayar.

A Saudiyya ma tun ranar Lahadi ne kotun ƙolin ƙasar ta fitar da sanarwar buƙatar al'umma su duba jinjirin watan na Ramadana a ranar Talata.

Musulmai za su tashi da azumi ranar Laraba idan har aka ga aka ga jinjirin watan Ramadana da yammacin Talata. Idan kuwa ba a ga jinjirin watan a ranar Talata ba, hakan nan nufin ba za a tashi da azumi ba sai ranar Alhamis.

Ko kun san yadda za ku iya ganin jinjirin wata da idonku?

Yaya ake ganin jinjirin wata?

Simwal Usman Jibrin, wanda masani ne kan ganin wata, kuma jami'i a kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi a Najeriya ya ce ana neman jinjirin wata ne bayan faɗuwar rana.

"Ana neman jinjirin wata ne bayan faɗuwar rana kasancewar a ranar 29, wata da rana kan ɓullo ne kusan lokaci ɗaya sannan kuma su faɗi a kusan lokaci ɗaya.

"Domin samun ganin jinjirin wata, za a jira zuwa kimanin minti 10 bayan faɗuwar rana, lokacin da sararin samaniya ya fara duhu, domin hakan ne kawai zai bayar da damar ganin watan kasancewar hasken rana na dusashe na wata".

Tsawon wane lokaci ne wata ke yi a ranar farko kafin faduwa?

Masani kan lamarin ganin wata, Simwal Usman ya ce babu ƙayyadadden lokacin da wata ke kwashewa a sararin samaniya a ranar farko bayan faduwar rana.

Sai dai ya ce a ƙiyasi wata "ba ya wuce minti 40 a sama bayan faɗuwar rana a ranar farko".

A wannan shekara Simwal ya bayyana cewa zai yi wahala a iya ganin watan a ranar Talata, bisa lissafi irin na masana ilimin taurari.

Yadda za a iya ganin wata a Najeriya

Simwal ya bayyana cewa ana sa ran "haihuwar jinjirin watan Ramadana na wannan shekarar da misalin ƙarfe ɗaya da minti ɗaya na rana.

"Wannan na nufin cewa a lokacin da rana za ta fadi watan bai cika awa shida da haihuwa ba.

Watan zai faɗi bayan minti 9 da faɗuwar rana a ranar Talata, wanda hakan ke nufin zai yi wahala a ga watan a ranar Talata ba a Najeriya".

Sai dai a cewar Simwal "ba ana dogaro da lissafi ko hisabi ba ne, kamar yadda sunnah ta nuna.

Ya kuma faɗa wa BBC matakan da mutum zai bi idan yana so ya ga watan:

  • A kasance a wuri mai sarari
  • A sanya ido domin ganin faɗuwar rana
  • Bayan minti 10 sai a dubi saitin inda rana ta faɗi

Mene ne ke hana ganin wata a ranar 29 ga Sha'aban?

Akwai dalilai da dama da ke hana a ga jinjirin watan Ramadana ranar 29 ga watan Sha'aban, kamar yadda Simwal ya bayyana wa BBC:

  • Lokacin da rana da wata suka faɗi a kusan lokaci ɗaya
  • Lokacin da ba a samu kimanin minti 10 tsakanin faɗuwar rana da faɗuwar wata ba
  • Lokacin da wata ya shiga tsakanin duniya da rana
  • Lokacin da wata ya riga rana faɗuwa
  • Yanayin hazo