Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ma'anar Ramadan da abun da ya kamata mai azumi ya sani
Latsa alamar hoton sama domin kallo da sauraron Sheikh Jabir Maihula
Dr Jabir Sani Maihula ya ce asalin kalmar Ramadan ta zo ne daga kalmar Larabci ta 'Ramaz' wadda ke nufin tsananin zafin rana saboda watan Ramadana na zuwa ne lokacin zafi tun kafin zuwan Musulunci.
Allah ubangiji ya kuma wajabta azumin na Ramadan a shekara biyu bayan Hijra daga Makka zuwa Madina.
Sheikh Maihula ya ce kafin a wajabta shi ga kowa an bi mataki-mataki kafin nan.
"An wajabta azumin Ramadan da farko tare da bayar da zabin yin azumin ko kuma ciyarwa. Sai dai an kara da cewa yin azumin shi ne ya fi alkairi."
To amma daga baya sai aka soke wancan zabi inda aka azumin ya zama tilas illa dai ga wadanda ba za su iya yi ba.
Watan Ramadan ne Allah Ubangiji ya saukar da littafi mai tsarki na Qur'ani sannan kuma a watan ne ake kankare zunubai ga bayi.
Dr Jabir Maihula ya kara da cewa yana daya daga cikin manyan alfanun yin azumi samun ceto ranar kiyama sakamkon azumtar watan Ramadan, baya ga kasancewarsa daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.