Waiwaye: Ƙarin farashin fetur da komawar manyan hafsoshin soji Sokoto
Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

A ranar Talatar makon nan ne Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya sanar da sabon farashin litar man fetir.
A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, kamfanin ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.
Tuni dai wasu gidajen maI a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a ranar ta Talata.
Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashi ne.
Kotu ta tura masu zanga-zangar #EndBadGovernance zuwa gidan yarin Kuje

A cikin makon ne kuma wata babbar kotun tarayya a Abuja ta tura wasu daga cikin waɗanda suka gudanar da zanga-zangar tsananin rayuwa zuwa gidan yarin Kuje, bayan sun ƙi amsa tuhumar laifin cin amanar ƙasa.
A zaman kotun, mai shari'a Emeka Nwite ta bayar da umarnin a ajiye su har zuwa lokacin da za a saurari ƙara dangane da bayar da belin su a ranar 11 ga watan Satumba.
Mutanen da ake tuhumar dai sun musanta dukkan laifukan da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke tuhumar su da aikatawa guda shida da suka jiɓanci ta'addanci.
Mahaifiyar Umaru Yar'Adua Hajiya Dada ta rasu

Asalin hoton, Sagil Royal Photograpy
A cikin makon ne dai mahaifiyar tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar'Adua ta rasu tana da shekara 100.
Hajiya Fatima - wadda aka fi sani da Dada - ta rasu ne da yammacin ranar Litinin, kamar yadda iyalanta suka tabbatar wa BBC.
A 'yan shekarun nan, an ga yadda manyan 'yansiyasar Najeriya suka dinga tururuwar gaishe ta duk lokacin da suka shiga garin Katsina.
Ɗanta Umaru Musa ya rasu yana kan gadon mulkin Najeriya a watan Mayun 2010 bayan shafe watanni yana jinya. Kafin haka, yayansa Shehu Musa Yar A'dua wanda tsohon mataimakin shugaban mulkin soja ne ya rasu a watan Disamban 1992.
Hafsoshin Najeriya sun is Sokoto domin kawar da ƴan bindiga

Asalin hoton, Ministry of Defence
Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle tare da Babban Hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa sun isa jihar Sokoto domin ba da gudummawa wajen murƙushe ƴan fashin daji da ke addabar yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya bai wa ministan da manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin mayar da ayyukansu zuwa Sokoto bayan ƙaruwar ayyukan ƴan fashin daji a baya-bayan nan.
Ƙaramin ministan tsaron ya ce zuwan su Sokoto zai bunƙasa ayyukan dakarun Najeriya masu yaƙi da ƴan bindiga da suka addabi al'ummar yankin Arewa maso Yamma.
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 31 tare da rusa gida 5,000 a jihar Kano

Asalin hoton, NEMA
Duk dai a cikin makon, aƙalla mutum 31 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon ambaliyar ruwa da ta auka wa ƙananan hukumomin jihar Kano 21, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.
Babban sakatare na hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa reshen Kano, Isyaku Kubarachi, ya ce ambaliyar ta kuma rusa gidaje 5,280 a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.
"Mutum 31,818 lamarin ya shafa da kuma rusa gidaje 5,280," in ji shi. "Bala'in ya kuma lalata gonaki 2,518 da suka kai faɗin hekta 976."
Ya ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ne ya jawo ambaliyar, kuma akasarin gidajen da lamarin ya shafa na ƙasa ne.
Gwamnatin Najeriya ta kwaso 'yan ƙasarta 167 da suka maƙale a Libya

Asalin hoton, NEMA
A ranar Larabar da ta gabata ne kuma gwamnatin Najeriya ta sanar da kwaso 'yan ƙasarta 167 da suka maƙale a ƙasar Libya.
Sanarwar da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa, Nema, ta fitar a yau Laraba ta ce mutanen sun isa filin jirgin sama na Legas da misalin ƙarfe 3:51 na ranar Talata.
Nema ta ce an yi aikin kwaso su ne bisa taimakon ƙungiyar 'yan cirani ta duniya wato International Organisation for Migration (IOM).
Mutanen sun ƙunshi maza 77, da mata 69, da yara 10, da kuma jarirai 11.











