Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda amfani da kalmomin ƙabila ko addini ke ta'azzara matsalar tsaro a Najeriya
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
A Najeriya, amfani da kalmomin ƙabilanci da addini wajen alaƙanta waɗanda suka aikata laifi na cikin abubuwan da ke faruwa akai-akai, lamarin da masana suke ganin cewa aibin shi ya fi alherinsa.
A lokuta da dama, da zarar wani, daga wata ƙabila ya aikata laifi, akan yi amfani da ƙabilarsa wajen alaƙanta laifin da ya yi, inda ake cewa ƴan ƙabilarsa ne suka aikata laifin.
Ana amfani da addini wajen alaƙanta wasu masu laifin, ta hanyar cewa ‘masu addini kaza’ ne suke aikata laifi iri kaza, abin da wasu suke ganin ba a musu adalci wajen alaƙanta su da laifin da su aikata ba.
Ba a Najeriya kawai ake samun irin haka ba. Misali, kasashe da kafafen yada labarai na duniya kan alaƙanta mabiya addinin Musulnci da masu tsattsauran ra’ayi, lamarin da ke haifar da wariya ko tsangwama ga mabiya addinin, ko da kuwa ba sa cikin masu aikata irin wadannan laifuka.
Hatsari ga ƙasa
A game da me hakan ke nufi ga tsaro, Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan harkokin tsaro a Najeriya ya ce ɗaukar irin wannan matakin na yin kuɗin goro da wasu ƙabilu wajen alaƙanta su da wata barazanar tsaron ko hare-hare na baragana ga tsaron ƙasa.
Ya ce, "alaƙanta laifuka da wata ƙabila ko addini da ma duk wani abu da ke nuna ɓangaranci abu ne mai matuƙar hatsari saboda yana rura wutar gaba da ƙiyayya da tsana ga baki ɗayan jinsin da ake wa wannan kallon na alaƙa da matsalar da ake magana," in ji Kabiru Adamu.
Masanin tsaron ya ce a lokuta da dama, ƙabilun da ake kallo ko alaƙantawa da wani laifi, "sai ka ga wasu ƴan ƙalilan daga cikin su ne suke aikata laifin," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "wataƙila ma ba za su wuce kashi 10 cikin 100 ba ko kuma ma ba su kai haka ba."
Kabiru Sufi ya ce haɗa ƙabila baki ɗaya a mata kuɗin goro kuskure saboda a cewarsa, "idan aka yi musu kuɗin goro, sai ka ga an ɓata sunan sauran waɗanda ba sa aikata laifin, kuma an ja musu tsana, sannan kuma ba za su shiga duk wani tsari da ake yi ba na ƙoƙarin magance matsalar."
‘Yanbindiga
Ana amfani da wasu kalmomin da ake alaƙantawa da wasu ƙabilu da addini wajen jifar wasu mutane da kalmar ta'addanci ko kuma zargin su da hannu a matsalolin tsaro.
Daga cikin kalmomin da suka fi shuhura, Dr Kabiru ya ce alaƙanta kalmar Fulani da matsalar ƴanbindiga wato 'Fulani bandit' ya fi tayar musu da hankali.
Ya ce, "amfani da kalmar Fulani da alaƙanta su da matsalar tsaro ya fi tayar mana da hankali a matsayinmu na masu nazarin harkokin tsaro saboda a lokuta da dama, ana amfani da hakan wajen ɗaukar doka a hannu, inda ake tsare wasu mutane kamar yadda aka yi a jihar Filato, ake ɗaukar mataki a kan su saboda tunanin ƙabilar su ko addinin su."
Ya ce matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa ba, "akwai yiwuwar za a iya kai wa ga matakin yin kisan kiyashi ga Fulani irin wanda da aka taɓa yi Rwanda saboda tsanar da ake musu."
Sai dai ya ce ba yana nufin babu masu aikata laifi ba ne a cikin su, "amma a yi kuɗin goro a ce ƙabila ko jinsin ne baki ɗaya ke aikata laifin ne matsalar. Akwai kuma alaƙanta lamarin rashin tsaro da addini wanda shi ma yake tayar da hankali. Shi kuma an fi amfani da shi a lokacin siyasa, inda ƴan siyasa suke amfani da shi wajen cimma burin su na siyasa."
Ya ƙara da cewa a Najeriya an daɗe ana amfani da bambancin addini da ƙabila wajen raba kan al'umma, "wanda yake shafar makomar ƙasa da zaman lafiyarta. Ko yaƙin basasar ƙasar da aka yi a shekarun baya a Najeriya, waɗannan abubuwan biyu sun taka rawa."
Rura matsalar
A daidai lokacin da wasu ke cewa gano ƙabilun da suke aikata laifi na da kyau tare da taimakawa wajen gane su domin a iya gujewa, masanin ya ce kuɗin goron ne matsalar saboda a cewarsa hakan na haifar gaba da ƙiyayya.
Ya ce, "ware al'umma a musu kudin goro da alaƙanta su da matsalar tsaro na ƙara rura wutar matsalar tsaro a Najeriya saboda yana jawo tsana kuma yana jefa mutane da dama waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba a cikin matsala."
Ya kawo misalan yadda ya ce aka taɓa tare mutane a Filato da Benuwei, waɗanda ya ce a duk lokuta ake tare su, a kashe su, "kuma duk hakan na da alaƙa da ƙabilar su da addini."
Ya lissafa wasu matsaloli da yake ganin haɗa ƙabila a mata kuɗin goro na haifarwa kamar haka:
- Rura wutar rikici
- Rarraba kai tsakanin mutanen da ake zargi da waɗanda suka zama tare
- Buɗe ƙofar ɓarna: Wasu na amfani da damar wajen aikata laifi, sai su saje, wasu ma suna shiga irin ta ƙabilun su aikata laifi.