Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kun san sunayen tawagogin ƙasashen da za su je gasar kofin nahiyar Afirka?
A nahiyar Afirka sunayen tawagogin ƙwallon ƙafa na ƙasashe ba su tsaya ga harkar wasan ba kawai.
Wasu sunayen suna nuni da irin al'ada da jarunta da kuma tarihi na al'ummar ƙasa.
Tarihin gasar kofin ƙwallon ƙafar ta Afirka na da alaƙa sosai ga sunayen tawagogin nahiyar.
Ba wai kawai ƙasashe suna sanya sunayen ba ne haka, a'a, yawanci suna danganatawa da wasu dabbobin dawa da tarihin ƙasar ya shafa, wanda ke nuna wata jarumta da alfahari, wanda kan al'ummar ƙasar ya haɗu a kai.
BBC ta yi nazari game da sunayen tawagogin ƙasashe 24 da suka samu gurbin gasar ta Kofin Afirka ta 2025, daga 21 ga watan Disamba, 2025 zuwa 18 ga watan Janairun 2026.
Rukunin A: Zaki, Mikiya, da Kifi
Zaki (Moroko)
Sunan, ya samo asali ne daga nau'in zakin da ake da shi a dazukan yankin Afirka ta arewa, wanda yanzu kusan ya gushe, wanda kuma a zamanin da wata alama ce ta ƙarfi da sarauta a Afirka ta Arewa.
Alama ce ta kishi da zaƙaƙurancin tawaga da ke cike da burin cin kofin nahiyar. A matsayin ƙasar na mai masaukin baƙi, Moroko na fatan mamaya a gasar.
Mikiya (The Eagles - Mali)
Wannan suna wanda ya bayyana a shekarun 1970, yana da asali na daban: a lokacin Bajamushe, Karl-Heinz Weigang, ne ke horad da tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta Mali, inda a lokaci ya sa aka sa hoton mikiya (wadda alama ce ta Jamus) a jikin rigar 'yan wasan Malin
Tun daga sannan, Mali ta ci gaba da amfani da wannan alama ta mikiya - wadda alama ce ta mulki da 'yanci.
Jan ƙarfe ( Chipolopolos - Zambia)
Wannan suna na Chipolopolos, wanda ke nufin jan ƙarfe, wanda shi ne babban arziƙin cikin ƙasa, a Zambia ɗin, wanda kuma yana gaba wajen tallafa wa tattalin arziƙin ƙasar.
Tawagar ta Chipolopolos (Jan ƙarfe), wadda alama ce ta juriya, da dagiya, ta yi bajinta inda ta ci gasar ta Afirka ta 2012, wadda nasara ce ta tarihi da aka sadaukar da ita ga 'yan wasan ƙasar da suka rasu a haɗain jirgin sama na 1993.
Kifi (Coelacanths - Comoros)
Alamar tawagar ƙwallon ƙafa ta Komoros (Comoros), ita ce ta kifin da ake kira, coelacanth, wanda wani irin kifi ne na daban na zamanin da, da aka gano a ruwan tsaunukan da wannan ƙasa da teku ya kewaye take.
Tawagar ta Komoros, wadda wannan shi ne karo na biyu da za ta je gasar ta cin kofin ƙasashen Afirka, bayan ta 2021, na cike da alfahari da buri.
Wannan suna na nau'in kifin alama ce ta kasancewarsa na daban da kuma juriya, ta wannan ɗan ƙaramin tsibiri da ke zaman ƙasa a gaɓar tekun gabashin Afirka.
Rukunin B: Pharaohs, Antelopes, Warriors da Bafana Bafana
Fir'aunoni - Masar (The Pharaohs )
Ana yi wa tawagar ta 'yan wasan ƙasar Masar wadda ta ci kofin na Afirka sau bakwai, bajintar da ba wata ƙasa da ta taɓa yi laƙabin Pharaohs (fir'aunoni), tun da aka ƙirƙiro ta.
Wannan suna na sa su ji irin girma da isa na shugabanni na zamanin da.
Fir'auna - a zamanin da shi ne, shugaban ƙasa, shugaban soji, da kotuna, kuma ikonsa ya zarta na kowa da komai a lokacin.
Tawagar ta Masar, (Pharaohs), wadda ta mamaye tarihin ƙwallon ƙafa na Afirka, ta ci kofin a jere sau uku a tsakanin 2006 da 2010.
Bafana Bafana (Afirka ta Kudu)
Ɗanjaridar Soweto, Sbu Mseleku shi ne ya sa wannan suna da aka samo daga harshen Xhosa na Afirka ta Kudu, ya yi fice a shekarun 1990.
Suna ne da ke nuni da yarinta ko tashe, da sabunta, da kuma buri na ƙasar ta Afirka ta Kudu, wadda har yanzu take son ganin ta ci gaba a wannan gasa ta Afirka.
Bafana Bafana ta kafa tarihi ne a wasan ƙawallon ƙafar Afirka a 1996, bayan da ta ci kofin nahiyar a karon farko lokacin da aka yi gasar a ƙasarta.
Os Palancas Negras - (The Black Antelopes - Baƙaƙen Mariri) -Angola
Wannan alama ta ƙaton baƙin mariri, wadda ke nuni da karsashi da kuzari, alama ce ta dabbar da ƙasar ke alfahari da ita inda hatta a tambarin ƙasar.
Tawagar ta Angola ( The Palancas Negras) na da ƙudirin damfaruwa da wannan ƙarfi da kuzari na kakanninsu, su nuna bajinta a gasar - wadda suka kai wasan dab da na kusa da zuwa na ƙarshe ( quarterfinals) a 2008.
The Warriors (Zimbabwe)
Saɓanin masu amfani da suna da kuma alama ta gwarazan dabbobi, ita ƙasar Zimbabwe, ta zaɓi inkiya ce da ke zaburarwa, a yi ƙwazo da jarinta, wato ''Mayaƙa''.
"Warriors (Mayaƙa)" na nuni da alamu na juriya a ƙasar da wasan ƙwallon ƙafa ke zaman wata alama ta haɗin kai.
Ƙasar ta zaɓi amfani da wannan kalma ta ''Mayaƙa'' ne saboda tarihinta na mayaƙa,
musamman sarakuna irin su Mzilikazi da Lobengula, na masarautar Ndebele.
Rukunin C: Eagles, Cranes and Stars
Super Eagles - Najeriya (Babbar Mikiya)
Wannan tsuntsuwa mai kaifi da tsinin baki, alama ce ta ƙarfi - wadda kuma alama ce da ke kan tambarin ƙasar, hatta na sojojinta.
Sunan na nuni da buri da ƙarfin tawagar ta Najeriya, wadda take da tarihi da kuma buri na wakiltar Afirka ta Yamma a gasar ƙwallon ƙafa.
The Eagles of Carthage (Mikiya ) - Tunisia
Mikiya, wadda alama ce ta, tsohon birni na Carthage, na sa tunawa da bunƙasar da wannan Daular ta Afirka wadda ta zama kishiya ga Daular Rum.
Sunan na sanya wa, 'yan ƙwallon ƙasar ta Tunisia - mutanen da suke magadan Hannibal, tunawa da jarunta da alfaharin kakan nasu wanda ya yi fice wajen dabaru da ƙarfafa gwiwa.
Cranes - (Zalɓe) - Uganda
Tawagar Uganda ta ɗauki sunanta - The "Cranes" (Zalɓe), ne daga tutar ƙasar, wadda aka ƙawata ta da hoton zalɓe, da ke zaman alama ta zaman lafiya da lura (sanya ido sosai).
Ƙasar wadda za ta karɓi baƙuncin gasar ta cin Kofin Afirka ta 2027, na fatan taka rawar-gani a nahiyar.
The Taifa Stars (Taurari) - Tanzania
"Taifa" na nufin ƙasa a harshen Swahili. To a taƙaice, ''Taifa Stars'', wato suna tawagar ƙwallon ƙafa ta Tanzania na nufin, ''Taurarin Ƙasa''.
Wannan inkiya ko suna na tawagar da ke da kinaya ta azanci, na sanya alfahari da haɗin kai a ƙasar da ke da ƙabilu da al'adu daban-daban, wadda wasan ƙwallon ƙafa ke haɗa kan al'ummarta.
Rukunin D: Zakuna, Jakan dawa, Damusa( mai roɗi-rodi), da Damusa
Jakin dawa dabba ce ta ƙasa a Botswana, kuma tana alamta daidaito da zaman tare cikin lumana a tsakanin jinsin mutane daban-daban.
The Lions of Teranga - Zakunan Teranga - Senegal
Zaki na ɗaya daga cikin alamun tambarin ƙasar Senegal, kuma daman dabbar dawa ce da ake alfahari da ita a nahiyar Afirka, kasancewar tana nuna alama ta ƙarfi da mulki.
Sunan, "Lions of Teranga" (kara a harshen Wolof), inkiya ce da ake yi wa tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, domin bambanta ta da tawagar Kamaru -The Indomitable Lions, ko ta Moroko - the Atlas Lions.
The Leopards (Damisa mai roɗi-roɗi) - JD Congo
Hoton damisa (mai roɗi-roɗi) shi ne a kan tambarin hukumar ƙwallon ƙafa ta Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo (FECOFA), wadda aka daɗe da sani a matsayin "Simba" ( Zaki a harshen Swahili).
Amma kuma damisa wadda, ta fi natsuwa da iya sanɗa, ta kasance a matsayin wata alama ta bunƙasar tawagar ƙwallon ƙafar ta Kongo - wadda ta shahara a shekarun 1970.
The Cheetahs (Damisa) - Benin
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Jamhuriyar Benin wadda a da ake kira "Squirrels (Kurege)" ta sauya sunanta saboda wancan na da ba shi da wani karsashi, sai ta koma ''The Cheetahs'' a 2022, wato damisa wadda dabba ce da ake jin tsoro kuma mai gudun tsiya. Wannan sanuyi na nuni da buri na neman sabuntawa da kuma ƙarfi.
The Zebras - (Jakin dawa) - Botswana
Ana iya ganin launin zanen baƙi da fari na jikin jakin dawa, sosai a tambari da tutatr ƙasar Botswana.
Sunan na nuna alama ta bambance-bambance da haɗin kai a ƙasar da wasanni ke zaman wata hanya ta haɗa kan al'ummarta.
Group E: Fennecs, Stallions, Crocodiles and Lightning Bolts
The Fennecs (dila) -Algeria)
Dila ta kasance alamar da ke kan tambarin ƙasar ta Algeria.
Wannan dabba ce da aka santa da wayo da juriya wadda ta dace da burin tawagar ta Aljeriya mai suna ''Desert Warriors'' wadda kuma ake yi wa laƙabi da Greens, saboda juriyar da tawagar ke nuna wa a wasan ƙwallon ƙafar Afirka.
The Stallions (Alfadarai) - Burkina Faso
Hoton dokin da ke kan tambarin ƙasar ta Burkin Faso alama ce da ke nuni da tarihin labarin zamanin da na Gimbiya Yennenga, gwarzuwar Mossi, wadda ta kafa daular.
Dawakan wata alama ce ta sarauta da juriyar kasar da a kodayaushe take da burin bunƙasar zama babba.
Nile Crocodiles (Kaduna) - Sudan
A nan an sake nuni da muhimmanci da amfanin wannan dabba mai muhimmanci a zamanin da na Masar: kada na alamta ƙarfi da juriya na ƙasar da take da tarihi a ƙwallon ƙafa a da - inda ta kasance wadda ta yi nasara a gasar farko ta cin kofin ƙwallon ƙafar Afirka (AFCON) a 1957.
The Nzalang Nacional (Walƙiya ta Ƙasa - "National Lightning") - Equatorial Guinea
Walƙiya wanan suna ne da ke nuna azama da kai hari cikin sauri da bazata. Kalmar "Nzalang" ta harshen Fang, ɗaya daga cikin harsunan ƙasar ce. Tawagar ƙwallon ƙafar ta wannan ƙasa ta yi fice a matsayin wata sabuwar gwarzuwa a wasannin gasar na baya-bayan nan.
Rukunin F: Giwaye, Zakuna, Baƙar damisa da Macizai
The Elephants (Giwaye) - Ivory Coast
Giwa wadda ita ce ke tambarin ƙasar Ivory Cosat na fuskantar barazanar gushewa a duniya saboda sare dazuka musamman domin noman koko da kwakwa, da farauta da kuma fadada garuruwa.
Giwa wata babbar alama ce ta ƙarfi da alfahari da ƙasaita - ita ce alama ta tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar da kuma tambarin ƙasar, kamar yadda sunan ƙasar, da ya haɗa da hauren giwa (Ivory), ya nuna.
Giwa alama ce ta zummar tawagar ƙasar ta sake cin kofin na Afirka.
In Côte d'Ivoire, the elephant is a powerful national symbol, representing quiet strength, pride, and majesty. It is the emblem of the national football team and features on the country's coat of arms, as the country takes its name from ivory, which comes from this animal. The elephant illustrates the power of the reigning African champions, determined to reclaim their throne.
The Indomitable Lions (Zakunan da suka gagara) - Kamaru
Kusan za a iya cewa wannan suna na tawagar ƙwallon ƙafa ta Kamaru shi ne mafi shahara a nahiyar.
Tsohon gwarzon ɗan wasan ƙasar Roger Milla, shi ne ya ƙasa sunan ya yi fice a 1990 sai kuma daga baya sauran 'yan wasa irin su Rigobert Song da Samuel Eto'o, suka suka sa duniya ta ƙara sanin tawagar.
Zaki na zaman wata alama ta alfahari da ƙarfi da jarunta a tsakanin ƙabilun Fang, da Bamileke, da Bassa, da Bamoun, da sauran ƙabilu na ƙasar.
The Panthers (damisa) - Gabon
Kafin shekara ta 2000, ana kiran tawagar ƙwallon ƙafar Gabon da "Azingo," kamar da ke nufin ''rashin nasara" a harshen ƙasar.
Domin kare kanta daga rashin nasara, da kuma nuni da ƙarfinsu a fagen ƙwallon ƙafa , sai hukumar ƙwallon ƙafa ta Gabon ɗin ta zai ta sauya sunan tawagar ta kona Panther - wadda wani nau'i ne na damisa, wanda hakan ke alamta ƙarfi da kuzari.
The Mambas ("The Snakes - Kumurci ") - Mozambique
Mamba sunan wani nau'in miciji ne mai dafi da ke da zafin nama da kuma faɗa - wanda ake tsoro sosai.
An aro sunan ne daga tauraron ƙwallon kwando na Amurka Kobe "Black Mamba" Bryant, wanda ke nuni da sauri da zafin nama da kuma haɗarin tawagar da ake rainawa.
Waɗannan sunaye na tawagogin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka, wasau ana sa su ne a sanadiyyar wasu 'yan jarida masu sha'awa da ƙwazo a fagen wasan.
Wani lokacin kuma hukumomin wasa na ƙasar ne ke zaɓo sunan bayan tattaunawa da jama'a.
Kuma duka wannan na nuni da yadda wasan na ƙwallon ƙafa ke da muhimmanci da alaƙa da al'adu a Afirka.
Saboda haka kowace tawaga ke ƙoƙarin nuna irin tunani da gudummawarrta wajen bunƙasa wannan wasa mai farin jini.
A don haka gasar ta bana ta 2025 ba za ta kauce daga wannan ala'ada da tawagogin na Afirka suka yi fice a kai ba.