Da gaske ƴanbindiga na kwarara daga arewacin Najeriya zuwa Kudanci?

Asalin hoton, Getty Images
Jihohin yankin kudu maso Yammacin Najeriya sun ce sun tsaurara tsaro a kan iyakokinsu sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴanbidiga a yankunan daga jihar Kwara mai makwabtaka.
Wani rahoto da jaridar Punch ta ruwaito ta ambato shugabannin tsaron jihohin Oyo da Ekiti da Osun da kuma jihar Ondo na cewa sun yi wani gagarumin shirin haɗin gwiwa domin hana ƴanbindiga daga jihar Kwara kwarara zuwa jihohin yankin.
Rahoton na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ta ɓankado yadda ƴanbindiga ke kwarara jihohin kudu maso Yamma daga jihar Kwara.
A baya-bayan nan jihar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin yankunan da ke neman zama matattarar ƴanbindiga a Najeriya.
A watannin baya ne dai aka kama wasu jagororin ƙungiyar Ansaru a jihar, waɗanɗa suka ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a ƙasar.
Da gaske akwai barazanar tsaro a kudu maso yammacin Najeriya?
Dakta Kabiru Adamu Shugaban Kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a ƙasashen Afirka, ya ce binciken kamfaninsu ya tabbatar da wannan iƙirari.
A hirarsa da BBC, masanin tsaron ya ce wannan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da yadda taswirar jihar Kwara take.
''Idan ka duba yadda jihar Kwara ta yi iyaka da jihohin yankin aƙalla uku, za ka ga cewa duk abin da ya shafi jihar Kwara ya shafi jihohin Ekiti da Oyo da jihar Ogun'', in ji shi.
A shekarun baya ma dai akwai wasu mahara da suka kai hari kan wani coci a jihar Ondo, inda bayanai suka nuna cewa maharan sun fito daga jihar Kogi mai makwabtakata da Kwara, kamar yadda Kabiru Adamu ya bayyana.
Ya ce yana da kyau jihohin yankin su ɗauki matakai domin kare yankinsu, daga maharan.
Ta yaya ƴanbindigar ke shiga yankin?

Asalin hoton, Samuel Aruwan
Dakta Kabiru Adamu ya ce a jihar Kwara akwai wani daji da ya ratso jihar daga ƙasar Jamhuriyar Benin.
Ya kuma ce ta cikin dajin ne ake samun ƙwararowar masu iƙirarin jihadi irin su al'qeada da IS, daga Yammacin Afirka zuwa Najeriya.
Masanin tsaron ya ce ta hanyar wannan daji ne suke bazuwa suwa jihohin kudu maso yammacin.
''Wasu ma sanadiyyar kasuwanci da sauran sana'o'i ne suka shiga jihohin'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa a wasu lokuta ma sukan saje cikin jama'a su riƙa yin zirga-zirga su je su yi ɓarnarsu.
Masanin tsaron ya ce a wasu lokutan kuma ta hanyar harkokin haƙar ma'adinai suke shiga yankin.
Masu iƙirarin jihadi ko ƴanfashin daji?
Dangane da nau'in ƴanbindigar da ke shiga yankin kuwa, Dakta Kabiru Adamu ya ce babu nau'in ƴanbindigar da ba sa shiga yankin.
''Duka da masu iƙirarin jihadin da ƴanfashin dajin kowannensu na shiga yankunan domin aikata laifuka'', in ji shi.
Masanin tsaron ya ce wani abun tayar da hankali ma game da ƴanbidigar yankin shi ne yadda duka nau'ikan ƴanbindigar da suka haɗa da masu iƙirarin jihadin da ƴanfashin daji ke zaune a wuri guda kuma suna aiki tare.
''Wannan ba abu ne da aka saba gani ba, to amma a Najeriya yanzu galibi sai ka samu ƴanbindiga da masu iƙirarin jihadi da masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba duk suna aiki tare a yanki guda'', in ji shi.
Matakan da ya kamata yankin ya ɗauka

Asalin hoton, Amotekun
Tuni dai shugabannin tsaron yankin suka sanar da matakan tsaurara tsaro a yankunansu domin kare jihohinsu daga ƴanbindigar.
Matakin da Dakta Kabiru Adamu ya ce shi ne ya fi dacewa.
Shugaban kamfanin tsaron ya kuma wani abu da ya kamata jihohin yankin su yi, shi ne ƙarfafa dangantakar tsaro da hukumomin jihar Kwara.
''Yana da kyau jihohin yankin su haɗa kai da jihar Kwara da ma wasu jihohin arewaci da ke makwabtaka da yankin''.
''Gwamnonin yankin su haɗa kai su kuma fito da wani tsari na aiki tare domin ƙarfafa tsaron yankin'', in ji shi.
Haka kuma dakta Kabiru Adamu ya ce yana da kyau jihohin yankin su ƙarfafa ƙungiyar samar da tsaro ta yankin wato, Amotekum.
''Dama ita wannan ƙungiya na da kayan aiki masu inganci kuma na zamani, don haka yana da kyau a ƙara ƙaimi wajen bai wa mambobinta horon ƙwarewar aiki, domin magance wannan matsala'', in ji shi.











