Me kuke son sani kan wasan Dortmund da Real a Champions League?

Borussia Dortmund za ta fafata da Real Madrid a wasan karshe a Champions League ranar Asabar a Wembley, karo na 15 da za su fuskanci juna a tsakaninsu.

Dortmund ta bayar da mamaki da ta kawo wannan matakin karshen a kakar bana, bayan da ta ja ragamar rukuni na shida a Champions League.

Ita ce ta yi ta daya a rukunin da maki 11, sai Paris St Germain ta biyu da maki takwas da AC Milan ta uku da kuma Newcastle United a gurbin da ya fi kowanne zafi.

Haka kuma kungiyar ta Jamus ta fitar da PSV a zagaye na biyu da yin waje da Atletico Madrid a quarter finals da doke PSG gida da waje a daf da karshe.

Real Madrid ce ta ja ragamar rukuni na uku da maki 18 - ta fuskanci kalubale da yawa, musamman a karawa da RB Leipzig da Manchester City da kuma Bayern Munich da ta kai karawar karshe.

Real Madrid, wadda Carlo Ancelotti ke jan ragama ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla, kenan za ta so daukar Champions League na 15 a tarihi.

Kungiyar Santiago Bernabeu ta yi wasa 12 ba tare da an doke ta ba a gasar zakarun Turai ta kakar nan da yin nasara takwas da canjaras hudu.

Ita kuwa Dortmund ta yi rashin nasara daya daga 11 da ta fafata a gasar zakarun Turai da nasara bakwai da canjaras uku da yin wasa shida ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, kuma ita ce ke fara zura kwallo a raga karo tara daga fafatawa 10.

Wasan karshe a Champions League da Dortmund ta buga shi ne a Wembley, inda ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Bayern Munich a 2013, Mats Hummels da Marco Reus sun taka rawar gani, wadanda har yanzu na taka leda shekara 11 da ta wuce.

Ita kuwa Real Madrid ta sha fafatawa da kungiyoyin Jamus a wasan karshe, wadda sau daya ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Bundesliga daga 20 da cin 13 da canajaras shida a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai.

Karo na uku Dortmund ta kai wasan karshe, Real kuwa shi ne na 18 a Champions League

Wannan shi ne karo na uku da Dortmund ta kai wasan karshe a Champions League, yayin da Real Madrid za ta yi karawa ta 18 a gasar da lashe 14 daga ciki.

Dortmund ta yi nasarar doke Juventus a wasan karshe a 1997 da rashin nasara a hannun Bayern Munich a fafatawar karshen a 2013.

Ita kuwa Real Madrid ta yi rashin nasara uku a wasan karshe, kuma na baya-bayan nan shi ne a 1981.

Wannan shi ne karo na 15 da za su fafata a tsakaninsu kuma duka a Champions League, inda Dortmund ta yi nasara uku da canjaras biyar, Real ta ci wasa shida.

Real Madrid ce kan gaba a yawan lashe Champions League a tarihi, mai 14 jimilla, yayin da Dortmund take da daya a tarihi.

Rabonda Real ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Jamus tun 2013 a hannun Borussia Dortmund.

Wannan shi ne wasan karshe karo na biyar tsakanin kungiyar Jamus da ta Sifaniya a ko dai European Champions Cup ko kuma UEFA Champions League.

Kowacce ta yi nasara bibiyu, inda Bayern Munich ta doke Atletico Madrid a 1974 da kuma cin Valencia a 2000.

Ita kuwa Madrid ta yi nasara a kan Eintracht Frankfurt a 1960 da doke Bayern Leverkusen a 2002.

Wasu batuwan da suka shafi Dortmund, wadda za ta buga wasa na 300 a zakarun Turai

Idan Dortmund ta lashe wasan karshe a Wembley ranar Asabar za ta zama ta hudu da ta dauki kofin da tazara mai yawa tsakani da kofin farko, wato daga 1997 zuwa 2024, kenan shekara 27 tsakani.

Wadda take da tazarar daukar kofi da yawa ita ce Inter Milan, shekara 45 da ta lashe kofin farko 1965 na Champions League, sai ta dauki na gaba a 2010.

Dortmund ta ci kungiyar Sifaniya, Atletico Madrid a zagayen daf da na kusa da na karshe a bana, kenan ta Jamus din ta doke ta Siafaniya 7-3 a irin wannan gurbin.

Idan ta kai ga fenariti kuwa, Dortmund ta yi nasara a kan AJ Auxerre a 1993 da kuma Rangers a 1999, amma ta yi rashin nasara a hannun Club Bruges a 2003 da kuma Udinese a 2008 a Champions League.

Wasan da Dortmund za ta kara a Wembley ranar Asabar shi ne na 300 a gasar zakarun Turai, kuma kungiyar sai da ta yi shekara 41, sannan ta yi fafatawa ta 100 daga 1956 zuwa 1997.

Haka kuma Dortmund ta yi shekara 17, sannan ta kara yin wasa na 100 kuma na 200 jimilla tsakanin 1997 zuwa 2014).

Sai kuma ta yi shekara 10 da ta kara wasa na 100 kuma na 300 a gasar zakarun Turai tsakanin 2014 zuwa 2024.

Haka kuma a wasanta na 100 a gasar zakarun Turai, Borussia ta doke Juventus 3-1 ta kuma lashe kofin.

Wasu batutuwan da suka shafi Real Madrid

Borussia Dortmund ita ce kungiya ta hudu da Real Madrid za ta fafata da wadda ke buga Bundesliga a Champions League a bana.

Real din ta doke Union Berlin 1-0 a gida da kuma 3-2 a waje a cikin rukuni na uku.

Haka kuma Real ta doke Leipzig 1-0 a Jamus, sannan suka tashi 1-1 a Sifaniya.

Sai kuma Real Madrid ta fuskanci Bayern Munich, wadanda suka tashi 2-2 a Jamus, sannan ta yi nasara 2-1 a Santiago Bernabeu a zagayen daf da karshe.

A shekara ta 2017, Real Madrid ta zama ta farko da ta kare kofinta na Champions League, sannan ta zama ta farko da ta lashe uku a jere a 2016 da 2017 da kuma 2018.

Wannan shi ne wasan karshe na 22 da Real Madrid za ta fafata a dukkan gasar zakarun Turai.

Kuma a kofi 17 da take da shi a European Cup/Champions League ta dauki UEFA Cup a 1985 da kuma 1986, sai ta yi rashin nasara a wasan karshe a European Cup Winners’ Cup a 1971 da kuma 1983.

A wasan da Real Madrid ta buga da kungiyoyin Jamus tun daga zagaye na biyu ta yi nasara 20 da kai wa zagayen gaba karo takwas.

Wasa tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund

Real Madrid da Borussia Dortmund sun kara a gasar zakarun Turai sau 14 a tsakaninsu, inda Real ta ci wasa shida da canjaras biyar, Dortmund ta ci karawa uku.

Kuma sun hadune a Champions League, inda suka fara fuskantar juna ranar 1 ga watan Afirilun 1998, inda Real Madrid ta yi nasarar cin 20.

Wasa na biyu kuwa da aka yi a Jamus ranar 15 ga watan Afirilu, sun tashi ba ci a fafatawar.

To sai dai wannan shi ne karon farko da za su fafata a wasan karshe a babbar gasar ta zakarun Turai.

Jerin wasannin da aka yi tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund:

2017/2018

Champions League Laraba 06 ga watan Disambar 2017

  • Real Madrid 3 - 2 B Dortmund

Champions League Talata 26 ga watan Satumbar 2017

  • B Dortmund 1 - 3 Real Madrid

2016/2017

Champions League Laraba 07 ga watan Disambar 2016

  • Real Madrid 2 - 2 B Dortmund

Champions League Talata 27 ga watan Satumbar 2016

  • B Dortmund 2 - 2 Real Madrid

2013/2014

Champions League Talata 08 ga watan Afirilun 2014

  • B Dortmund 2 - 0 Real Madrid

Champions League Laraba 02 ga watan Afirilun 2014

  • Real Madrid 3 - 0 B Dortmund

2012/2013

Champions League Talata 30 Afirilun 2013

  • Real Madrid 2 - 0 B Dortmund

Champions League Laraba 24 ga watan Afirilun 2013

  • B Dortmund 4 - 1 Real Madrid

Champions League Talata 06 ga watan Nuwambar 2012

  • Real Madrid 2 - 2 B Dortmund

Champions League Laraba 24 ga watan Oktoban 2012

  • B Dortmund 2 - 1 Real Madrid

2002/2003

Champions League Talata 25 ga watan Fabrairun 2003

  • B Dortmund 1 - 1 Real Madrid

Champions League Laraba 19 ga watan Fabrairun 2003

  • Real Madrid 2 - 1 B Dortmund

1997/1998

Champions League Laraba 15 ga watan Afirilun 1998

  • B Dortmund 0 - 0 Real Madrid

Champions League Laraba 01 ga watan Afirilun 1998

Real Madrid 2 - 0 B Dortmund

'Yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Dortmund:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa y Fran.

Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger y Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos y Arda Güler.

Masu cin kwallo: Vini Jr., Rodrygo, Joselu y Brahim.