'Aiki cikin tsananin zafi na wahalar da jaririn da ke ciki'

Wani sabon bincike ya ce aiki cikin tsananin zafi ka iya shafar jariran da ke cikin mace.

Illar hakan sun haɗa da ta'azzara bugun zuciyar jaririn da rage gudun jininsa ta hanyar cibiyarsa.

Masu bincike sun ce ana buƙatar samar da wasu ingantattun hanyoyi don kare mata masu ciki a yayin da sauyin yanayi ke jawo ƙaruwar zafi a fadin duniya.

Binciken, wanda Kwalejin Kula da Tsafta da Samar da Magungunan Cututtukan da ake samu a yankuna masu zafi ta London, wato London School of Hygiene and Tropical Medicine (LSHTM), ya yi, ya bibiyi manoma 92 a ƙasar Gambiya.

Binciken, wanda aka wallafa a mujallar The Lancet Planetary Health, ya bayar ce, duk matakin zafi ɗaya na digirin salshiyas na wahalar da jaririn da ke ciki da kashi 17 cikin 100.

Duk da cewa akwai binciken da aka yi a ɗakunan gwaji da suka yi duba kan illar da zafi ke yi wa mata masu ciki a ƙasashe masu ƙrfin tattalin arziki, ana ganin wannan binciken na yanzu shi ne na farko da ya yi duba a kan tasirin hakan a ƙasashe masu tasowa.

Mata masu ciki suna aiki a gonakin shinkafa a yankin West Kiang da ke ƙsar Gambiya. Suna aiki a cikin garjin rana na tsawon awa biyu zuwa takwas.

A tsawon lokacin da aka yi binciken, an ga cewa rana kan take har zuwa ma'aunin salshiyas 45, amma a lokacin damina zafin yakan fi haka saboda yanayin huci.

An yi wa matan hoton ciki ta hanyar amfani da wasu na'urori don gano yanayin bugun zuciyar jariran nasu.

Ana ɗaukar yanayin ne a daidai lokacin da suka fara aiki da lokacin da suka ci rabin aikin da kuma lokacin da suka kammala za su tashi.

Kazalika an sa ido kan masu cikin don ganin irin tasirin da zafi ke yi wa jikinsu kamar jawo musu ciwon kai da kasala da tashin zuciya.

Dr Ana Bonell, jagorarr binciken ta LSHTM, ta ce an gano wahalar da jarirai ke sha a ciki saboda tsananin zafin ne duba da bin diddigin ayyukan mata a gonakin da kashi 33 cikin 100.

"Mun yi matuƙar kaɗuwa da gano cewa zafi na illatar jariran da ke ciki," in ji ta.

"Mun ga yadda bugun zuciyar jaririn ke aruwa sosai a tattare da binciken, ta yadda hakan ke saka shi cikin hatsari. Mun kuma ga tasirin da hakan ke yi wa gudun jinin jaririn saboda zafin na illata mabiya."

Ta ce tasirin hakan na shafar kowane yanki saboda sauyin yanayi.

"Hakan na da muhimmanci sosai wajen tabbatar da cewa mata a fadin duniya ba su fuskanci wata matsala ba a yayin rainon ciki. Za a ci gaba da samun aruwa zafi kuma idan mata suna shiga cikin zafi sosai, hakan na iya yin illa sosai a kansu ta wajen jawo musu haihuwar bakwaini ko a haifi jariri babu rai.

"Muna fatan cewa wannan binciken zai yi sanadin da za a fahimci wasu abubuwan da ke dabaibaye da wannan sakamako da aka gano, da kuma taimakawa wajen samar da matakan da za su rage tasirin wannan tsananin zafin."

Dr Bonell ta ce ana buƙatar ƙarin bincike a fayyace kan yadda tsananin zafi ka iya shafar zagayawar jini a jikin jaririn da ke ciki.