An kusa ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza - Biden

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
Shugaba Biden ya ce akwai fatan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza nan da Litinin mai zuwa.
Kalaman shugaban Amurkan na zuwa ne yayin da rahotanni ke nuna alamun samun nasara a tattaunawar da ake yi tsakanin Isr’ila da Hamas ƙarƙashin jagorancin Qatar.
Da yake jawabi ga manema labarai a birnin New York, Mr Biden ya ce mai bashi shawara a kan tsaron ƙasa ya shaida masa cewa an kusa ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta, da kuma sakin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
Shugaba Biden ya ce bisa yadda abubuwa ke tafiya, nan da ranar Litinin za a sanar da batun tsagaita wutar.
Ya ce: "Ina fatan zuwa ƙarshen mako...Zuwa ƙarshen mako. Mai bani shawara kan harkokin tsaron ƙasa ya faɗa mani cewa mun kusa cimma nasarar aikin, amma da saura. Ina dai fatan zuwa zuwa Litinin mai zuwa za a tsagaita wuta."
Isra’ila da Hamas na ci gaba da tattauna yadda shirin tsagaita wutar zai kasance, a wani zama da wakilan ɓangarorin ke yi a Qatar.
Akwai rahotannin cewa za a sako fursunonin Falasɗinawa har 400 da ke tsare a Isra’ila, domin neman Hamas ta sako wa Isra’ilan mata 40, mafi yawan su dattijai ne.
Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu dai ya sha alwashin ci gaba da shirinsa na luguden wuta a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, ko da kuwa an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar.
Can kuwa a gaɓar yamma da kogin Jordan, rahotanni sun ce an kashe Falasɗinawa uku a wata aran-gama da dakarun Isra’ila.
Hukumar lafiyar Falasɗinawan ta ce mutum aƙalla dubu huɗu aka kashe a gaɓar yamma da kogin Jordan tun da aka fara yaƙin a Gaza.













