Yadda magidanci da iyalansa suka koma gidansu da yaƙi ya dagargaza a Gaza

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yadda magidanci da iyalansa suka koma gidansu da yaƙi ya dagargaza a Gaza

Yayin da ake fargaba game da ko za a tsawaita wa'adin tsagaita wuta a Gaza, wani magidanci mai ƴaƴa biyar ya koma gidansa, wanda hare-haren Isra'ila suka yi raga-raga da shi a Gaza.

Wael Qudeih ya ce ya koma ne domin ganin abin da ya rage a gidan nasa.

Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Gaza ne bayan wani hari da mayaƙan Hamas suka kai a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,200 tare da garkuwa da wasu 200.