Yadda ango da ƴan uwansa biyar suka mutu 'bayan cin abincin biki'

OBINNA DIEKE

Asalin hoton, OBINNA DIEKE

Mutanen garguruwan Obollo-Eke da Udenu da kuma Aka-Utara a ƙaramar hukumar Adani, Uzo-Uwani a jihar Enugu sun girgiza bayan faruwar wani mummunan al'amari na mutuwar mutum shida ciki har da ango bayan kammala bikinsa.

Angon mai suna Obinna Dieke na cikin wadanda ƙaddarar ta afka musu, yayin da ita ma amaryar a yanzu haka take kwance a asibiti ita da wasu mutum biyun.

Obinna Dieke ɗan asalin garin Markurdi na jihar Benue ne da yake harkokin kasuwanci kafin mutuwarsa.

Ƙanin anogon Chinedu Dieke, ya shaida wa sahsen BBC Pidgin cewa, surukinsa Joseph Ogbonna, da ƴaƴansa biyu Chijindu da Obinna na cikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Chinedu ya ce yayan nasa shi ne gatan zuri'arsu.

Sannan ya ce wata yayarsa mai suna Goodness da mahaifiyar Chijindu da Obinna suna asibiti a kwance su ma.

Ya ƙara da cewa ita ma mahaifiyar angon an kwantar da ita a asibiti amma ta fara farfaɗowa.

Di house wey di groom build for Aka-Utara, Uzo-Uwani Local Goment Area of Enugu State- na here di new couple suppose dey stay after dia wedding

Asalin hoton, OBINNA DIEKE

Bayanan hoto, Di house wey di groom build for Aka-Utara, Uzo-Uwani Local Goment Area of Enugu State- na here di new couple suppose dey stay after dia wedding

Wani mutum daga garin Adani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce suna zargin abinci mai guba suka ci har ya yi sanadin mutuwarsu - amma dai ba a tabbatar da hakan ba.

Majiyar ta kuma wasu kuma na zargin cewa wata gurɓatacciyar iska da mutanen suka shaƙa ne daga wani janareto da aka ajiye a barandar gidan, inda suka zazzauna a cikinta saboda gudun dukan ruwan sama ne, ta yi sanadin mituwar tasu.

Sai dai mutumin ya ce binciken da za a yi kan gawarwakinsu ne kawai zai tabbatar da ainihin sanadin mutuwar.

Ƴan sanda na bincike

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A hannu guda kuma, kwamishinan ƴan sanda na jihar Eungu Ahmed Ammani, ya bai wa sasahen bincikin aikata miyagun laifuka umarnin yin cikakken bincike don gano musabbabin mutuwar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar Daniel Ndukwe ya fitar, ya ce kwamishinan ƴan sandan Ahmed Ammani ya nemi al'ummar yankin da abin ya faru su kwantar da hankulansu da bai wa jami'ai cikakken goyon baya don binciken lamarin.

"Sakamakon samun rahoto kan mutuwar wasu mutum shida da kwantar da wasu takwas din a asibiti a ƙauyen Akutara ranar 27 ga watan Agustan 2022 da misalin ƙarfe 0.30, kwamishinan ƴan sandan jihar Enugu ya ba da umarnin ƙaddamar da cikakken bincike kan abin da ya jawo mutuwar da rashin lafiyar sauran," a cewar sanarwar.

"Binciken farko-farko ya nuna cewa ɗaya daga cikin mamatan Obinna Dike mai shekara 31 ya je bikin aurensa ne shi da ƴan uwansa, bayan an kammala sai suka koma gida don ci gaba da shagali."

Sai dai washe gari babu wanda ya ita fita daga gidan lafiya, sai da mutane suka taru suka ɓalle ƙofar gidan, inda aka gan su a kwance magashiyyan cikin dafara.

Daga nan ne sai aka kwashe su zuwa asibiti ranga-ranga, inda aka tabbatar da mutuwar shida daga cikinsu, kuma aka fara bincike a kan gawarwakinsu, su kuma sauran da ba su mutu ba an kwantar da su ana duba su.