Wanne zaɓi ya rage wa Abba Kabir Yusuf a Kano?

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, FACEBOOK/Abba Kabir Yusuf

Bayanan hoto, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Tun bayan soke nasarar zaɓen Abba Kabir Yusuf da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi, a matsayin halastaccen gwamnan Kano, mutane ga alama ke tambayar ko wanne zaɓi ya rage masa?

Kotun, wadda ta gabatar da hukuncinta ta manhajar Zoom a ranar Laraba, ta ce tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasir Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC ne ya ci zaɓen 18 ga watan Maris, 2023.

Ta ce ta soke ƙuri'a 165,633 da in ji ta aka yi wa ɗan takarar jam'iyyar NNPP aringizo, inda tun farko hukumar zaɓe ta ce ya samu ƙuri'a 1,019, 602.

Tuni dai lauyoyin Abba Kabir Yusuf da jam'iyyarsa ta NNPP suka yi fatali da hukuncin.

Mataki na gaba kawai da Gwamna Abba Kabir da jam'iyyar NNPP suke da shi, shi ne amfani da damar ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.

Bayan nan, duk wanda hukuncin kotun ɗaukaka ƙara bai yi masa daɗi ba tsakanin Abba Kabir Yusuf da Nasir Yusuf Gawuna, yana iya sake tafiya gaba zuwa Kotun Ƙoli.

Mene ne matsayin Abba Kabir a yanzu?

Abba Kabir Yusuf zai ci gaba da kasancewa a kan kujerar gwamnan jihar Kano, har sai an kai ƙarshen wannan ƙara, idan shi, ko jam'iyyar NNPP ta yanke shawarar ɗaukaka hukuncin da aka yanke.

Yanzu dai Abba Kabir Yusuf yana da mako uku, wanda a ciki dole ne ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun gaba, matuƙar bai amince da hukuncin ba.

Masana shari'a kuma sun ce, kotun ɗaukaka ƙara tana da tsawon wata biyu ne ta saurari duk wani ƙorafi da aka ɗaukaka game da zaɓe, sannan ta yanke hukunci.

Wani ƙwararren lauya a Najeriya Dr. Sulaiman Santuraki ya ce "Abba zai ci gaba da zama gwamna har sai an ɗaukaka ƙara, kuma ba zai ajiye muƙaminsa ba har zuwa lokacin da za a kai ƙarshen shari'ar a kotun ƙoli."

Mene ne matsayin Nasir Gawuna?

Nasir Yusuf Gawuna

Asalin hoton, DK

Bayanan hoto, Nasir Yusuf Gawuna

Dr Santuraki ya ce "yanzu Nasir Gawuna na a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano wanda kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta tabbatar."

"Sai dai ba za a rantsar da shi ba har sai idan an kammala sauraron ƙara a kotuna na gaba."

Sai dai kuma ya ce za a iya rantsar da Nasir Gawuna nan da kwana 21 idan har gwamna Abba Kabir Yusuf ko jam'iyyarsa ta NNPP ba su ɗaukaka ƙara ba.

Shari'ar ta zaɓen gwamnan jihar Kano ta ja hankalin al'umma sanadiyyar hamayya mai ƙarfi da ke tsakanin jam'iyyun biyu (APC da NNPP) da kuma rawar da iyayen gidansu ke takawa a siyasar Najeriya.

Kano ce jiha ta biyu mafi yawan masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya.

Abba Kabir Yusuf dai ya kayar da Nasir Yusuf Gawuna ne a zaɓen da aka gudanar a watan Maris na shekara ta 2023.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa ta ce Abba ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Yusuf Gawuna ya samu ƙuri'a 890,705.