Mun shawarci Ganduje kada ya amsa gayyata kan ‘bidiyon dala’ - APC

Ganduje

Asalin hoton, Salihu Tanko

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta aika takardar gayyata ga tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a kan 'bidiyon dala'.

Wata sanarwa da hukumar mai taken (KPCACC) ta fitar, na cewa ta gayyaci Ganduje ne domin ya je ya wanke sunansa game da binciken da ake yi.

A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet, ta fitar da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum wanda ta yi zargin cewa Ganduje ne yake karɓar damin daloli daga hannun wasu 'yan kwangila yana zubawa a aljihu.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar ƙorafe-ƙorafe, Muhyi Magaji Rimin Gado yana cewa: "Na sa hannu a kan wata wasiƙa don gayyatar shi, ya zo a yi masa tambayoyi a hukumar cikin makon gobe. Saboda abin da doka ta ce kenan kuma za mu bayar da ɗumbin damammaki don ya kare kansa".

Sai dai, Mallam Muhammad Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano kuma makusancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce har yanzu ba su samu takardar gayyatar da ake cewa hukumar ta aika wa tsohon gwamnan ba.

Kuma dangane da sahihancin bidiyon da hukumar Muhyi take iƙirari, Muhd Garba ya ce ba za su ce uffan a kan wannan batu ba, don kuwa magana ce da take gaban kotu.

Umar Abdullahi Ganduje dai ya sha musanta zargin, inda ya riƙa iƙirarin cewa abokan adawa ne suka shirya maƙarƙashiya da nufin hana masa damar shiga zaɓen 2019.

Lamarin dai ya janyo matuƙar ce-ce-ku-ce, ba kawai a Kano ba har ma da Najeriya gaba ɗaya, abin da ya kai har majalisar dokokin jihar kafa kwamiti domin binciko gaskiyar lamarin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sanarwar dai ta ce hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano ƙarƙashin jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ta nuna aniyar yin bincike tun sa'ar da bidiyon ya bayyana, sai dai a lokacin Ganduje yana da rigar kariya a matsayinsa na gwamna.

Gwamnatin Ganduje a watan Yulin 2021, ta dakatar da Muhyi Magaji daga shugabancin hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, lamarin da ya janyo taƙaddama, har Muhyi ya garzaya kotu.

Gwamnatin a wancan lokaci ta zargi Muhyi Rimin Gado da ƙin aiki tare da wani jami'i da ma'aikatar kuɗi ta aika hukumar, abin da ya janyo Ganduje ya sallame shi daga aiki a 2022.

Sai dai, shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen ya ci gaba da ƙalubalantar matakin da gwamnatin Ganduje ta ɗauka, kuma ya nemi kotu ta tabbatar masa da 'yancinsa na ɗan'adam.

Daga bisani, kotu ta yanke hukuncin da ya bai wa Muhyi gaskiya, kuma ta ba da umarnin a mayar da shi kan muƙaminsa.

A watan Yunin 2023 ne kuma, sabuwar gwamnatin Kano da Abba Kabir Yusuf ke jagoranta, ta mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado kan muƙamin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis, Muhyi Rimin Gado ya ce bayan ya koma shugabancin a 'yan makwannin da suka wuce ne, suka yanke shawarar sake buɗe binciken.

Ya ce zuwan Abdullahi Ganduje gaban hukumar don wanke kansa ko akasin haka, abu ne mai fa'ida saboda "bidiyon na ci gaba da janyo wa jihar da ma al'ummar jihar muzantawa a faɗin duniya".

'Yunƙurin 'yan adawa ne don ganin bayan Ganduje'

Mallam Muhammad Garba dai ya yi zargin cewa gayyatar da hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta yi wa Ganduje, ba komai ba ne face siyasa. Ya yi iƙirarin cewa abokan adawar Ganduje ne kawai ke yunƙurin ganin sun wargaza aniyar ba shi wani muƙami kamar na minista a gwamnatin tarayya.

"Abin mamaki ne, bai kamata idan muna aiki, mu yarda a dinga amfani da mu domin a cimma wasu abubuwa da 'yan siyasa ke son cimmawa ba".

Ya ƙara da cewa ba daidai ba ne a dinga amfani da mutane don ganin an kassara wani mutum, an kai shi ƙasa, tare da cin mutuncinsa.

Ya yi iƙirarin cewa maganar ta zama ta siyasa.

Gayyatar dai na zuwa ne kwana 38, bayan Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa mulkin Kano ga gwamnatin Kwankwasiyya , a ƙarshen wa'adinsa na biyu, wanda ya fara daga 2015 zuwa 2023.

Tsohon kwamishinan Ganduje dai ya ce matakin, wani yunƙuri ne kawai na daƙile duk wani namijin ƙoƙari da tsohon gwamnan ya yi a Kano. "A ci mutuncinsa, kuma ina ganin wannan ba daidai ba ne."

Ya ce ya tuntuɓi Ganduje bayan samun wannan labari, inda ya tabbatar masa cewa har zuwa lokacin da yake magana da BBC (Alhamis da rana) ba a ba shi wata takardar gayyata ba.

'APC ta ce kada ya je Kano'

Makusancin Dr. Ganduje ya kuma ce yana da masaniyar cewa jam'iyyar APC reshen Kano ta shawarci tsohon gwamnan kada ya amsa gayyatar hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano.

Ya ce jam'iyyarsu ce ta fitar da wannan sanarwa.

Sai dai ya ce duk da haka, Ganduje zai tuntuɓi lauyoyinsa domin jin irin shawarwarin da su ma za su ba shi game da wannan gayyata.

"Saboda na san wannan magana ta bidiyo da ake zance a kai, magana ce da take gaban babbar kotun Najeriya da ke Abuja. Kuma ni a ƙaramin sanina, in dai magana tana gaban kotu, bai kamata a ce an sake tado ta ba," in ji Muhammed Garba.

Ya ce idan lauyoyinsa sun ba shi shawara, sun ga dacewar ya je, to me zai hana shi zuwa?

Idan kuma suka ce kada ya je saboda dalilan da suka ba shi, in ji Mallam Garba, sannan ga umarnin da jam'iyyar APC ta ba shi, saboda haka wannan abin da Ganduje ya kamata a ce ya tsaya ya yi duba ne a kansu.

Tsohon kwamishinan ya ce saboda ba abu ne, nasa shi kaɗai ba. "Abin da ya shafe shi, ya shafi dukkan jam'iyyar APC, saboda an mayar da batun siyasa".

Ita dai jam'iyyar APC a cikin sanarwar da shugabanta na Kano Abdullahi Abbas da sakataren jam'iyyar, Zakari Sarina suka sanya wa hannu, ta ce jam'iyyar NNPP ta sake dawo da "batun da aka tsiro da shi saboda dalilai na siyasa game da bidiyon dala, wanda ke gaban kotu ne da wata muguwar maƙarƙashiya don zubar da mutuncin tsohon gwamnan".

Ta ce 'yan hana ruwa gudu ne suka shiga wannan yunƙuri na ɓata suna da nufin shiga tsakanin Bola Ahmed Tinubu da Ganduje, wanda sanarwar ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin babban aminin shugaban ƙasar a arewacin Najeriya.

APC ta ce an yi amfani da irin wannan salo don lalata damar Ganduje ta neman tikitin jam'iyyar don sake tsayawa takarar gwamna a 2019.

'Binciken kimiyya ya tabbatar da bidiyo'

A ranar Laraba ne, hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta jihar Kano ta yi iƙirarin cewa ƙwararru sun tabbatar da sahihancin bidiyon dala, ta hanyar binciken ƙalailaita na kimiyya.

Shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji ne ya sanar da haka, lokacin da ya zanta da wasu ƙungiyoyin fararen hula, inda aka nuna bidiyon ga mahalarta.

Binciken ƙalailaitar kimiyya (forensic analysis), wata hanyar kimiyya ce da ƙwararru ke amfani da ita wajen bin diddigi da ƙwanƙwance shaida don warware sarƙaƙiyar wani aikin laifi.

Sai dai, hukumar ba ta yi cikakken bayani ga jama'a game da abubuwan da ƙwararrun suka yi la'akari da su, ko kuma suka gano da ke tabbatar da sahihancin bidiyon ba.

Haka zalika, Muhammed Garba ya buƙaci sanin mutanen da hukumar ta bayyana da ƙwararru. "Sai a ce su wane da wane, ko kuma ƙungiya kaza da kaza, ko da hukuma kaza ne suka tsaya, suka yi bincike, da kuma irin abubuwan da suka binciko.

Ya yi zargin cewa yawancin waɗanda shugaban hukumar ya gayyata don ganin bidiyon a ranar Laraba, abokansa ne.

Tsoffin aminan juna

Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kasance mataimakin gwamna ga tsohon maigidansa, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso har karo biyu, daga 1999 zuwa 2003 da kuma a shekara ta 2011 zuwa 2015.

Sai dai sun samu saɓani, bayan Ganduje ya gaji maigidansa a mulkin Kano daga shekara ta 2015, inda suka raba gari a siyasance. Tsananin rikicin siyasar tsakanin tsoffin manyan aminan guda biyu, ya sanya Kwankwaso ficewa daga jam'iyyar APC wadda ta koma hannun Ganduje a Kano.

Daga nan ne, Kwankwaso da ƙungiyar siyasarsa ta Kwankwasiyya suka koma tsohuwar jam'iyyarsu ta PDP, inda ya tsayar da Abba Kabir Yusuf - tsohon kwamishinansa na ayyuka - takara don ya ƙalubalanci Ganduje, da ke neman wa'adi na biyu a zaɓen 2019.

Sai da aka je zagaye na biyu, bayan hukumar zaɓe ta ce sakamakon zaɓen gwaman Kano, da ya bai wa Abba nasara da farko, bai kammala ba.

Daga bisani, Ganduje ya kayar da Abba Kabir a zaɓen da aka kammala, wanda aka fi sani da suna 'Zaɓen Gama' da ratar ƙuri'a 8,982.

Bayan sake canza sheƙa, Kwankaso ya sake tsayar da Abba Kabir Yusuf takara a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, inda ya yi nasarar kayar da ɗan takarar Ganduje a zaɓen watan Maris ɗin 2023.

Za dai a zuba ido zuwa makon gobe, don ganin ko Ganduje zai amsa gayyatar hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta jihar Kano, kuma a'a. Da kuma ganin abin da zai faru bayan ya amsa ko ya ƙi amsa goron gayyatar.